An Nada Shugaban Asusun Ba Wa Dalibai Bashin Kudin Karatu
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da yaƙinin mista Ovia zai yi amfani da ƙwarewarsa...