Tsadar Rayuwa: Litar Fetur Ta Haura N1000 A Jihohin Arewa

IMG 20240225 WA0030

An fara shiga matsalar tsadar man fetur ne tun daga ranar 29 ga Mayu, 2023, ranar da aka rantsar da Shugaba Bola Tinubu, inda tun a kan mimbarin rantsuwa ya bayyana cire tallafin fetur, wanda nan take sai da ya dangana lita ɗaya ta kai 650 a cikin sati ɗaya.

Tun daga nan kuma tsadar rayuwa ta riƙa kwankwatsar marasa galihu, talakawa da masu ƙaramin ƙarfi.

A Kano, yawancin masu motoci duk sun ajiye, wasu motocin kuma duk su na kan layin mai, ana jiran tsammani, amma kuma farashin a ranar Litinin ɗin nan ya ma haura Naira 1,000.

Wakilin mu ya shiga harabar katafaren Masallacin Bilal da ke unguwar Karkasara, inda ya ga motoci jingim a cikin harabar da rana.

Yawancin motocin na maƙwautan Masallacin ne, waɗanda ke ajiye su a cikin harabar da dare, su na kwana a harabar, wataƙila saboda ƙarancin wurin ajiye motoci a gidajen su.

To sai dai kuma wakilin mu ya lura kusan kashi 85% bisa 100% na motocin ba a fita da su ba, saboda ƙarancin fetur da kuma tsadar sa.

Dukkan gidajen mai da ake sayar da fetur a Kano, akwai dogayen layukan motoci da babura. Sannan kuma ga tsananin zafin rana, wadda ke fara kuɗa tun daga ƙarfe 10:30 na safiya.

Yadda ake fama da ƙarancin fetur a Kano, haka lamarin ya ke a Jigawa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply