Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Ware Kwanaki Uku Na Makokin Rasuwar Sarkin Zazzau

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir Erufai ta bayyana kwanaki uku a matsayin ranakun ci gaba da nuna alhinin rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris. A takardar da gwamnatin Kaduna ta sanar da hakan, ta bayyana cewa duk da nuna jimamin za a bude ofisoshin gwamnati a ranakun Litinin da Talata, amma za a yi hutun gama gari a ranar Laraba. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce jama’ar jihar Kaduna sun yi babban rashi. Ya mika godiyarsa ga shugaban kasar a kan tura wakilansa da…

Cigaba Da Karantawa

Rasuwar Sarkin Zazzau: Najeriya Ta Yi Babban Rashi – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Lahadi ya jagoranci ministoci da manyan jami’an gwamnati zuwa Birnin Zazzau dake jihar Kaduna domin wakiltar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin jana’izar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Dr Shehu Idris. Daga cikin ministocin da suka rufa mishi baya, akwai ministar kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed, ministan muhalli, Dr. Mahmud Mohammed da ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.Hakazalika, daga cikin wakilan shugaban kasan akwai mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu. Bayan saukar wakilan a makarantar koyon tukin jirgin…

Cigaba Da Karantawa

Rasuwar Sarkin Zazzau: Babban Rashi Ne Ga Ƙasa – Ramalan

An bayyana rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris a matsayin wani gagarumin rashi ba kawai ga jama’ar Masarautar Zazzau ba, sai ga dukkanin jama’ar Najeriya baki ɗaya. Shugaban Kamfanin Atar Communication masu gidan Talabijin da Rediyo na Liberty da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty Alhaji Tijjani Ramalan ya bayyana hakan a sakon ta’aziyya da ya gabatar na rssuwar mai martaba Sarkin na Zazzau. Ya kara da cewar a madadin shi da kafatanin ma’aikatan Liberty sun samu labarin rasuwar ne, cikin kidimewa da shiga damuwa, amma babu…

Cigaba Da Karantawa

Taƙaitaccen Tarihin Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi shine Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi ɗa ne, ɗan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo. Shi kuma Sarki Muhammadu Sambo ɗa ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a Daular Fulani ƙarƙashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Ɗanfodiyo ya yi…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: Ba Mu Yarda Da Magudin Da INEC Ke Yi Ba – Oshiomole

Bayan bayyana nasarar jam’iyyar PDP a kananan hukomin takwas cikin goma sha biyu da INEC ta yi, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole ya ce ba za su amince da magudin da hukumar zabe take shirin shirya musu ba, domin babu adalci a ciki. A wani lamarin daban kuwa kwamishinan zaben ya sanar da harbe wani jami’in INEC a karamar hukumae Etsako, sannan kuma wani jami’in tattara sakamakon zabe shi ma ya yi batan dabo a wata karamar hukuma. Yayin da ya rage zaura sakamakon kananan hukumomi biyu…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: El Rufa’i Ya Shiga Gasar Gudun Fanfalaki

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ya yi rajista domin shiga gasar tseren fanfalaki na kasa da kasa a jihar amma ba zai yi fiye da kilo mita biyar ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a ranar Asabar a Kaduna inda ya ce gasar da za ayi a ranar 21 ga watan Nuwamba zai ci kimanin Naira miliyan 300 kuma ana sa ran manyan ‘yan tseren duniya 10 za su shiga gasar. A cewarsa, an shirya gasar ne domin gano matasa masu…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, biyu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin. A jiya hankali ya fi karkata ga zaben gwamnan jihar Edo da aka yi. A yanzun haka ana can ana ci gaba da hada hancin alkaluman sakamakon zaben. Gwamna Obaseki da ke yin takara a jam’iyyar PDP da na APC Ize Iyamu duk sun kada tasu kuri’ar a mazabunsu. Sai dai an ta korafin ba a kiyaye…

Cigaba Da Karantawa

Sokoto: Sarkin Musulmi Ya Nada Sabbin Hakimai

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, a ranar Asabar ya nada sabbin hakaimai 15 a Jihar Sokoto. Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta ruwaito cewa anyi nadin ne bayan rasuwar hakiman da ke shugabancin garurruwan. Sarkin musulmin ya taya sabbin hakiman murna kuma ya bukaci su tabbatar sun yiwa garurruwansu wakilci mai kyau a majalisar sarkin musulmin.“Nadin da aka yi muku karin nauyi ne da kuma dama domin ku yi wa garurruwan ku hidima, saboda haka ina kira gare ku ku mayar da hankali domin tabbatar da kawo…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: PDP Ta Yi Wa APC Fintinkau

Jam’iyyar PDP ta sha gaban jam’iyyar APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo. Hakan na nufin cewa dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben. Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki; Karamar hukumar Igueben PDP: 7,870 APC: 5,199 Karamar hukumar Esan central PDP: 10,964 APC: 6,719 Karamar hukumar Esan…

Cigaba Da Karantawa

Kimanin Matasa 2000 Ne Za Su Samu Aiki Ƙarƙashin Bizi Mobile

An ƙiyasta cewa kimanin Matasa 2000 ne zasu samu gajiyar aikin Banki da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da ya saba hada hadar kuɗi ta zamani. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kamfanin Alhaji Aminu Bizi, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna. Bizi ya bayyana cewar tuni kamfanin nashi bisa ga haɗin gwiwa da babban Bankin Najeriya,suka cimma wata matsaya na inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, kuma kamfanin nashi ya bada fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma…

Cigaba Da Karantawa

Kimanin Matasa 2000 Za Su Samu Aiki Karkashin Bizi Mobile

An ƙiyasta cewa kimanin Matasa 2000 ne zasu samu gajiyar aikin Banki da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da ya saba hada hadar kuɗi ta zamani. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kamfanin Alhaji Aminu Bizi, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna. Bizi ya bayyana cewar tuni kamfanin nashi bisa ga haɗin gwiwa da babban Bankin Najeriya,suka cimma wata matsaya na inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, kuma kamfanin nashi ya bada fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: APC Ta Yi Babban Kamu

Tsohon Sanata dake wakiltar Bauchi ta tsaskiya Isah Hamma Misau a Jihar Bauchi, yayi ban kwana da Jam’iyyar PDP inda ya hada kai da Dogara a Jam’iyyar APC. Tuni dai ruwa yayi tsami tsakanin Hamma Misau da Jamiyyar sa ta PDP da kuma gwamna Bala Mohammed dake jagoranci Jihar a halin yanzu, indai ba amanta ba Misau ya kasance a cikin yayan jam’iyyar da sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin sun kada Jamiyyar APC a zaben gamagari na 2015. Kuma Jam’iyyar PDP har tabashi mukamin shugabanci kwamitin bankado al’mundahana da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: El Rufa’i Da Ummi Sun Yi Taro Da Masu Yaƙi Da Fyaɗe

Biyo bayan gama gyaran dokar manyan laifuffuka ta 2017 mai lamba ta 5 sashe na 258 da majalissalar dokokin Jihar Kaduna ta yi, gwamna ya sanya hannu, wacce ta tanadar da hukunci mai tsauri na kisa tare da dandaƙa ga masu aikata laifin fyaɗe a Jihar Kaduna; Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i tare da Uwar Gidansa, Hajiya A’isha Ummi Garba Ahmad El-Rufa’i sun yi taro tare da dukkan manyan jagororin yaƙi da matsalar ta fyaɗe domin tattaunawa kan yadda za a cigaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su tainaka wajen…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, daya ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha tara ga watan Satumba na shekarar 2020. Kwamitin da ya saba raba kudi tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi FAAC a duk wata, ya raba naira biliyan dari shida da tamanin da biyu da ‘yan kai na watan Agusta, da ke nuna idan an yi sa’a a soma jin dilin-dilin zuwa karshen mako mai zuwa. Yau za a gudanar da zaben…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, daya ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha tara ga watan Satumba na shekarar 2020. Kwamitin da ya saba raba kudi tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi FAAC a duk wata, ya raba naira biliyan dari shida da tamanin da biyu da ‘yan kai na watan Agusta, da ke nuna idan an yi sa’a a soma jin dilin-dilin zuwa karshen mako mai zuwa. Yau za a gudanar da zaben…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Liverpool Ta Sayi Gogaggen Ɗan Wasan Tsakiya

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila ta sayi Gogaggen dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayern Munich a kan $26m. Thiago, dan asalin kasar ‘Andolus’ wacce aka fi sani da ‘Spain’ a yanzu, ya saka hannu a kan kwantiragi na zama na lokaci mai tsayi a kungiyar Liverpool. Dan wasan mai shekaru 29 a duniya ya shafe tsawon shekaru 7 tare da kungiyar Bayern Munich. Yayin zamansa a Bayern Munich, Thiago ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin gasar Bundesliga, kofin Jamus da kuma kofin gasar zakarun…

Cigaba Da Karantawa

Ebonyi Ce Kan Gaba Wajen Aurar Da Kananan ‘Yan Mata – Ministar Mata

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihar Ebonyi, daya daga cikin jihohin yankin kabilar Igbo na cikin jihohin da aka fi aurar da kananan yara mata a Najeriya. Gwamnati ta yi kira ga gwamnan jihar, David Umahi, ya dakile wannan lamari saboda shugaba Muhammadu Buhari ya damu matuka sosai a kai. Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta bayyana hakan ne yayinda ta kai ziyara jihar Ebonyi ranar Juma’a. Ta ziyarci jihar ne domin kaddamar da shirin rabawa mata rishon girki mai amfani da iskar gas 13,000 ga matan karkara. An…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Tausayi Ne Ƙarin Farashin Mai Da Lantarki A Yanzu – Ladaja

Hamshakin ‘dan kasuwan nan kuma tsohon ‘dan takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 da ya gabata, hon Ibrahim Abubakar Ladaja ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da karin kudin wutar lantarki da man fetur da gwamnatin tarayya tayi. Hon Ibrahim ya bayyana cewa ” a irin halin da talakawan kasar nan ke ciki, bai kamata a kara masu kudin wuta ba. Kowa ya san halin da tattalin arzikin duniya ya shiga sakamakon bullar annobar cutar covid 19 daya tsayar da komai wuri daya. Kasar mu ta shiga halin…

Cigaba Da Karantawa

Rabon Gidaje Ga ‘Yan Bindiga: Gwamnatin Katsina Ta Shiga Ruɗani – Mahadi

An bayyana yunƙurin Gwamnatin Jihar Katsina na raba Gidaje da Shaguna gami da gonaki ga tubabbun ‘yan Bindiga a matsayin rashin sanin ya kamata, wauta da babban ganganci. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin Garin Kaduna Dr Mahadi Shehu, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna. Mahadi Shehu ya ƙara da cewar gwamnatin ta Katsina ta nuna halin ko in kula da rashin tausayi ga talakawan jihar, waɗanda suka fito ƙwai da ƙwarƙwata suka zaɓe su, ta hanyar gaza…

Cigaba Da Karantawa

Duniyar Fina-Finai: Za A Ɗaure Masu Fim Ɗin Maɗigo – Hukumar Tace Fina-Finai

Wasu masu shirya finafinai biyu na fuskantar yiwuwar ɗauri idan suka yi burus da tsattsauran gargaɗin da hukumomi suka yi masu, suka ci gaba da shirye-shiryen fitar da wani fim da ke nuna wasu mata biyu suna soyayya kamar yadda jaridar BBC ta rawaito. Haska fim Don samun damar haska fim ɗin, masu shiryawar na shirin fitar da shi a shafukan intanet don yi wa masu sa idon ba-zata. Sai dai NFVCB na matuƙar sa ido kan duka hanyoyin shafukan intanet don hana fim ɗin fita. A cewar shugaban tace…

Cigaba Da Karantawa