Rashin Imani Ne Ɓoye Kayayyakin Tallafin CORONA Da Gwamanoni Suka Yi – Galadima

Tsohon na hannun daman Shugaban ƙasa Buhari Malam Buba Galadima, ya ce, abin baƙin ciki ne da takaici kuma rashin imani ne ƙarara ɓoye kayayyakin tallafin CORONA da gwamnoni suka yi, kuma tabbas jami’an gwamnatin wata jiha da bai bayyana sunanta ba, sun taba tunkarar ofishinsa domin sayar da kayayyakin tallafin korona da suka karbo daga gwamnatin tarayya. Dattijon dan siyasar ya caccaki gwamnatocin jihohi a kan boye kayan abincin da ‘yan kasuwa da kungiyoyi (CACOVID) suka bayar a matsayin gudunmawarsu domin tallafawa talakawa lokacin annobar korona. Galadima ya bayyana…

Cigaba Da Karantawa

Ba A Taɓa Yin Adalin Shugaba A Najeriya Kamar Buhari Ba – Jiƙamshi

Shugaban hukumar Kula Da Zuba Hannun Jari ta Jihar Katsina Kuma Shugaban kwamitin wayar da Jama’a Kan Al’umma Jihar Katsina bisa ga shirye-shiryen tallafin da Gwamnatin Tarayya, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana cewa tunda aka dawo mulkin damakaradiyyaamakaradiyya a kasar nan ba’a taba samun gwamnatin da ta bullo da shirye- shiryen tallafi da ta zizarawa yan Nijeriya kudade daban daban kamar ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ba. Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana haka ne a dakin taro na hukumar EEC, da ke kan hanyar Kano a cikin garin Katsina,…

Cigaba Da Karantawa

Albashin ‘Yan Majalisa Bai Taka Kara Ya Karya Ba – Ndume

Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya soki kiran da ake yi na rage albashin ‘yan majalisar dokokin tarayya inda ya ce shi a ganinsa albashin ‘yan majalisar bai da wani tasiri kan tattalin arzikin kasar. Ndume, ya bayyana hakan ne a yayin da aka yi masa wata tambaya a cikin wani shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, 25 ga watan Oktoban 2020. Dan majalisar mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa ‘yan majalisar sun…

Cigaba Da Karantawa

Albashin ‘Yan Majalisa Bai Taka Kara Ya Karya Ba – Ndume

Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a Majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya soki kiran da ake yi na rage albashin ‘yan majalisar dokokin tarayya inda ya ce shi a ganinsa albashin ‘yan majalisar bai da wani tasiri kan tattalin arzikin kasar. Ndume, ya bayyana hakan ne a yayin da aka yi masa wata tambaya a cikin wani shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, 25 ga watan Oktoban 2020. Dan majalisar mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa ‘yan majalisar sun…

Cigaba Da Karantawa

Albashin ‘Yan Majalisa Bai Taka Kara Ya Karya Ba – Ndume

Wani dan majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya soki kiran da ake yi na rage albashin ‘yan majalisar dokokin tarayya inda ya ce shi a ganinsa albashin ‘yan majalisar bai da wani tasiri kan tattalin arzikin kasar. Ndume, ya bayyana hakan ne a yayin da aka yi masa wata tambaya a cikin wani shirin Channels Television na yammacin ranar Juma’ a, 25 ga watan Oktoban 2020. Dan majalisar mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi bayanin cewa ‘yan majalisar sun samu naira biliyan 128 ne kacal…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: Obasanjo Ya Yaba Jawabin Shugaban Ƙasa

Tsohon Shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan jawabin kasa da yayi kan zanga-zangar EndSARS ranar Alhamis da ta gabata. Tsohon Shugaban kasar ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da ke raye wadanda Buhari ya gayyata zuwa wani taro na yanar gizo a ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba. Da yake magana a wajen taron, Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Buhari a kan nunawa da yayi cewa zanga-zangar lumana na daga cikin damokradiyyar Najeriya. Idan ba a manta ba Shugaban kasa Muhammadu…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: PDP Ta Dakatar Da Dukkanin Harkokin Jam’iyyar

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a yanzu, biyo bayan cigaba da ƙazamar Zanga-Zanga ta EndSARS da ke cigaba a wasu sassa na Jihohin ƙasar. Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da sakataren yada labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya saki a ranar Juma’a a Abuja. Ologbondiyan ya ce sun dauki wannan matakin ne don nuna alhininsu a kan kisan matasa da aka yi a Lekki Toll Gate da sauran kashe-kashe da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS. Tun da fari…

Cigaba Da Karantawa

Sokoto: Wamakko Ya Shirya Addu’ar Samun Tsaro A Najeriya

Tsohon gwamnan jahar Sokoto Dr Aliyu Magatakarda Wamakko ya shirya addu’a ta musamman a yau Juma’a a gidan sa dake Gawon-Nama jim kadan bayan dawowarsa daga birnin tarayya Abuja. Sanata Wamakko ya shirya addu’ar ne domin neman dauki daga wajen Allah madaukakin sarki na matsalolin da ke addabar kasar mu Najeriya wadanda suka hada da matsalar tsaro, zanga-zangar EndSars, garkuwa da mutane, kashe-kase da sauran abubuwa. Hakama Sanata Wamakko yayi kira ga matasan Najeriya da su guji shiga duk wata zanga-zangar wadda zata haifar da tashin hankali ko asarar dukiya.…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Raba Tallafin Kayan Abinci

Uwar gidan gwamnan jihar Bauchi Aisha Bala Abdulkadir Mohammed taja hankalin iyaye da suci gaba da tarbiyan yayansu domin samun ci gaba tare da zaman lafiya mai dorewa Tayi wan nan kiran ne a lokacin taron da ta shirya na addu’oin zaman lafiya ma kasa, da kuma raba kayan abinchi ga makarantun Islamiyya a jihar Bauchi. Aisha Bala tace babu al’ummar da zata ci gaba cikin rudani da tashin hankali, saboda haka iyaye suna da jan aiki ta wajen kulawa da yayansu, “Irin wan nan tashin hankali a sanadin zanga-…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: INEC Ta Ɗage Dukkanin Zaɓukan Cike Gurbi

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ɗage dukkan zaɓuɓɓukan cike gurbi da ta shirya yi a jihohi 11 na ƙasar nan. A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin hukumar, Festus Okoye, ya ce an dakatar da gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabe 15 saboda halin rashin tsaro da ake ciki yanzu. A da an shirya yin zaɓuɓɓuka shida na sanatoci da kuma tara na majalisun jihohi a ranar 31 ga Oktoba. Zanga-zangar Allah-wadai da ta’asar ‘yansandan SARS ƙarƙashin yekuwar #EndSARS dai ta rikiɗe ta zama tarzoma wadda har da…

Cigaba Da Karantawa

Ba Zamu Lamunci Duk Wani Yunkuri Na Hargitsa Najeriya Ba – Gwamnonin Arewa

Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta bayyana bacin ranta kan wasu bata gari da miyagun ‘yan siyasa da suka lashi takobin durkusar da kasar nan da kuma kokarin yin juyin mulki. Gwamnonin sun yi mamakin ta wane dalili za’a cigaba da zanga-zanga bayan irin sauraro da biyayyar da gwamnatin tarayya da na jihohi suka yi. A jawabin da aka saki bayan zaman gaggawan da sukayi a jihar Kaduna ranar Alhamis, gwamnonin sun yi kira ga ‘yan Najeriya su yi fito-na-fito da makiyan Najeriya ta hanyar goyawa shugaban kasa baya. A cewar…

Cigaba Da Karantawa

Na Gagara Magana Da Buhari Har Yanzu – Babajide

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ce har yanzu bai samu yin magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, kan hargitsin da aka samu a Lekki Toll Gate, ranar Talata. A wata zantawa da aka yi da shi gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, Gwamnan ya ce sau biyu yana kokarin son yin magana da shugaban kasar amma bai yi nasara ba. Ya ce a karo na farko da ya kira ofishin shugaban kasar, an sanar da shi bai shigo ofishin ba, da ya sake kira na biyu…

Cigaba Da Karantawa

Tasirin EndSARS Ga ‘Yan Najeriya – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce zanga-zangar kyamar rundunar SARS ta sa gwamnati za ta yi gyara ga tsarin ƴan sanda a ƙasar baki daya. Zanga-zangar da ake kira EndSARS ta ci gaba da bazuwa a sassan Najeriya, inda yanzu ta shiga mako na uku ana gudanar da ita a fadin ƙasar. A kwanaki goma sha biyu da suka gabata, kasarmu ta fuskanci zanga-zangar matasa daga birane da dama, waɗanda suka nuna rashin jin daɗinsu kan take haƙƙin ɗan Adam da suka hada da…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Za A Fara Hukunta Masu Batsa Wajen Tallan Magunguna

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin aiki da zai kama duk wani mai sayar da maganin gargajiya da yake amfani da kalaman da ba su dace ba lokacin da yake tallar maganinsa. Kwamitin wanda Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa zai jagoranta, zai ƙunshi rundunar ƴan sandan jihar, KAROTA, HISBAH, da sauran hukumomin tsaro da jami’an kiwon lafiya, waɗanda za su kama tare da gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotu. Babban Sakataren hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar…

Cigaba Da Karantawa

EndSARS Shirine Na Ƙwace Mulki A Arewa – Miyyeti Allah

Wata kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah mai suna Kautal Hore, ta zargi tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Tinubu, da daukar nauyin zanga-zangar #EndSARS. Miyetti Allah, a wani rahoto daga jaridar The Sun ta yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa daga yankin kudancin kasar, ciki harda Tinubu, sune ke daukar nauyin zanga-zangar fadin kasar. Kungiyar ta yi zargin cewa shirin domin dagulawa da tunkude gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kuma son tsoratar da arewa don ta hakura da ‘yancinta na jagoranci har bayan 2023. An ruwaito cewa…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: Rikicin Cikin Gida Na Neman Tarwatsa APC

Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da barkewa wanda har hakan ya kai ga kotun koli dake Abuja, ta shigo ciki domin shawo kan rikicin. Sakamakon taron Jam’iyyar APC da aka yi a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, wanda aka nada shugabannin Jam’iyyar na jihar Zamfara ya jawo rikici, kamar yadda bangaren da Sanata Marafa ke jagoranta ke ganin cewa kotun daukaka kara ta yanke hukuncin da basu gamsu da shi ba, zasu kai kara kotun koli. Bangare daya na jam’iyyar, wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta sun…

Cigaba Da Karantawa

Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Bukaci A Biya Diyya Ga Jama’ar Jihar Kebbi

Sakamakon ambaliyar da ya yi sanadiyyar rushewar gidaje, gadaje, gonaki da kadarori na bilyoyin kudi, Dan majalisar tarayya mai wakiltar Koko/Besse da Maiyama dake jihar Kebbi, wato Honarabul Shehu Muhammad Koko (Wamban Koko) ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta waiwayi lamarin domin baiwa al’ummar da lamarin ya shafa tallafi. Jihar Kebbi dai ta shahara wajen harkar noma amma sai gashi baya ga matsalar corona sai ambaliyar ruwa ta shafi wasu yankunan jihar, wanda hakan ya jawo asarar gadoji, gidaje, gonaki da abubuwan more rayuwa. Sakamakon haka ne Honarabul…

Cigaba Da Karantawa

Babu Ɗan Arewan Da Ya Taimaki Buhari Kamar Tinubu – Lado Suleja

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Suleja, Gurara da Tafa dake jihar Neja, wato Honarabul Lado Suleja ya musanta zargin da wasu ‘yan Arewa ke yi na cewa tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu yana da mugun nufi ga al’ummar Arewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Honarabul Lado ya kara da cewa, Tinubu masoyi ne na hakika ga Shugaba Buhari da yankin Arewa da al’ummarta. “Idan muka duba kaf mutanen yankin Kudu babu wanda ya bada gagarumar gudummawa a nasarar da Buhari ya samu…

Cigaba Da Karantawa

Bani Da Hannu A Zanga-zangar SARS – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nisanta kansa daga zanga-zangar EndSARS da matasa suka shafe mako biyu suna yi a wasu jihohin ƙasar. Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, ya faɗa cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar cewa ba daidai ba ne a ce mai gidan nasa ne ke ɗaukar nauyin zanga-zangar, kamar yadda ake yaɗawa. Ya ce abu ne mai wuya Tinubu ya iya ɗaukar nauyin zanga-zangar a duka jihohin da ake yi. “Ba zai yiwu Asiwaju Tinubu ya ɗauki…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: APC Ta Zargi Tafka Maguɗi A Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Jam’iyyar APC a karamar hukumar Darazo tayi zargin Jamiyyar PDP mai mulkin jihar da tabka magudi a zaben kananan hukumomi a jihar Bauchi Adamu Maichi, shine Shugaban Jamiyyar APC na Darazo yayi zargin ne yayin zantawa da manema labarai a daidai lokacin da suke sa ido yadda zaben yake wakana a yankin. “Zan iya gaya maku babu shakka jamiyyar PDP ta shirya tsaf don yin magudin da suka saba yi, a yanzu haka sun tare kayan zabe masu yawan gaske na gundumomi a karamar hukumar da runfunan kada kuri’u. “Yanzun…

Cigaba Da Karantawa