Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa an wayi gari an ga an daura hotunan Muhammadu Sanusi II da na Shugaban kasa da Gwamna a gidan Gwamnatin jihar Kano. Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke Sanusi II daga sarautar Kano bayan an yi zaben 2019 Ana rade-radin Basaraken zai sake rike sarautar idan Jam’iyyar NNPP ta kafa gwamnati a Kano. Rahotanni sun bayyana cewa an hangi hotunan Sarkin Kano na 14, Mai martaba Muhammadu Sanusi II a gidan gwamnatin jihar Kano. Wani ‘dan kasuwa mai suna Kabiru…
Read MoreCategory: Al’ajabi
Al’ajabi
TARABA: Hukumar Jin Dadin Alhazzai Ta Sanar Da Kudin Ajiyan Maniyyata
BASHIR ADAMU, JALINGO Rahotannin dake shigomana yanzu daga Jihar Taraba na cewa, Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar ta sanar da Naira Miliyan Biyu da Dubu Dari Shida, a matsayin kudin ajiya da Maniyyata aikin Hajji na bana zasu biya a Jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata takardan sanarwa dake dauke da sa hannun Sakataren Gudanarwar Hukumar, Alhaji Umar Ahmed Ciroma da aka rabawa manema Labarai a Jalingo fadan Jiha. Sanarwan ya kuma umurci dukkanin Maniyyata aikin Hajjin na bana, musamman wadanda basu sami daman tafiya ba a shekaran…
Read MoreZamfara: Matawalle Ya Bada Umarnin Hallaka Kusoshin Jam’iyyar Mu – PDP
Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da kafa wani gungun ?an daba, tare da ha?in gwiwar jami’an tsaro domin kawar da jiga-jigan jam’iyyar adawa a jihar, a daidai lokacin da ‘yan sanda su ka janye tsaron ?an takarar gwamna na PDP a jihar, Dauda Lawal. Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa ‘yan sanda sun fara wani mumunan samame da nufin kamawa tare da tsare wasu manyan shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, tare da yi musu ?age. Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Juma’a,…
Read MoreJigawa: Gujungu Ne Za?in Mu – Jama’ar Ringim Da Taura
An bayyana ?an takarar kujerar ?an Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomi Ringim da Taura dake Jihar Jigawa Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu a matsayin wanda ya zarce tsara kuma shi ne fata ga jama’ar yankin. Al’ummar kananan hukumomin Ringim da Taura ne suka bayyana hakan a wata tattaunawa da suka yi da Wakilinmu da ziyarci yankin a ranar Juma’a. Sun bayyana yankin nasu a matsayin wanda ya dade cikin koma baya sakamakon rashin samun kyakkyawan wakilci, amma cikin ikon Allah samun Gambo Ibrahim Gujungu cikin ‘yan takara ya sanya sun…
Read MoreZamfara: Dambu Mai Guba Ya Yi Silar Mutuwar Mutum 7
Labarin dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewa Hukumar yan sanda reshen jihar ta ce wasu mutum Bakwai ?an gida ?aya sun rasa rayukansu bayan sun ci abincin gargajiya ‘Dambu’ lokacin cin abincin dare. Mai magana yawun hukumar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, shi ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai ta ?asa (NAN). Shehu ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin rasuwar iyalan ?an gida ?aya a ?auyen Dambaza da ke ?aramar hukumar Maradun. “Lamarin ya auku ranar Litinin jim…
Read MoreLikafa Ta Yi Gaba: Dangote Ya Zama Na 65 A Masu Kudin Duniya
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya na Bloomberg, daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya. Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, a cewar Bloomberg, yana da dala biliyan 20.4 kamar yadda a ranar Juma’a 8 ga Yuli, 2022, kuma hakan ne ya kai shi ga matsayi na 65 a mafi arziki a duniya. Rahoton ya kuma nuna cewa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yuli, Dangote ya samu…
Read MoreWasanni: An Kori Shugaban Kano Pillars A Firimiyar Najeriya
Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take. Hukumar ta fitar da wani jawabi a karshen mako da ya shafi dakatar da shugaban da wasu karin hukunce-hukunce. An tuhumi Kano Pillars da karya doka ta gudanar da wasannin Firimiya a lokacin da ta buga karawa da Dakkada ranar 23 ga watan Yunin 2022. A wasan ne shugaban hukumar Pillars, Suraj Yahaya ya ci zarafin mataimakin alkalin wasa Daramola Olalekan. An kuma ci tarar Kano Pillars da laifin…
Read MoreAdamawa: An Shawarci Gwamnati Ta Tallafi Masu Sana’ar P.O.S
An kira yi Gwamnatin tarayya da ta taimakawa masu sana ar P.O.S domin samun cigaban sana’ar tasu yadda ya kamata wanda sana’ar ta taimaka wajen samarwa matasa aikin yi a fadin Najeriya. Shugaban Kungiyar masu sana’ar P.O.S a jihar Adamawa Auwal Usman ne yayi wannan kira a zantawarsa da wakilinmu a Yola. Auwal Usman yace tun da gwamnati tana taimakawa sauran kungiyoyi to ya kamata suma a tuna da su kasancewar yawancinsu Matasa ne wadanda suke dogara da kansu. Auwal ya kara da cewa sana’ar tasu tana fuskantar kalubale da…
Read MoreAn Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon A Kotun Shari’a Ta Kaduna
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta sanin ma’aikacin nan ?an shekara 48, Bala Musa, wanda ya yi ikirarin ta masa al?awarin aure. Jarumar wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ranar Talata, ta fa?a wa Kotun cewa ba ta san mutumin da ake magana a kan shi ba. Da take jawabi ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a harabar Kotun, Gabon ta musanta tuhumar da ake mata baki ?aya inda…
Read MoreDalilin Rufe Kasuwanni A Abuja – Minista
Ministan Abuja mallam Muhammad Musa Bello ya bada umarnin rufe wasu kasuwanni guda uku a unguwar Deidei, biyo bayan wata tarzoma da ta yi sanadiyyar hasarar dukiya da rayuka. Ministan ya ce rikicin dai ya samo asali ne sakamakon wani hadari da ya rutsa da wasu yan Achaba inda wata mata ta fado daga kan Babur abin yazo da karar kwana kuma wata mota ta take kan matar ta rasu. Sai ‘yan uwan matar suka kone babur din yayinda su ma ‘yan Achaban suka shiga kasuwar ‘yan katako inda Galibi…
Read MoreKano: Ruwa Ya Ci Rayukan Wasu Aminai Uku
Ranar Laraba, 18 ga watan Mayun 2022, rana ce da jama’ar garin Bichi a Jihar Kano ba za su ta?a mantawa da ita ba, musamman Idris Umar wanda yana tsaye mutum uku daga cikin abokansa suka rasu bayan sun nutse a cikin ruwa a ?araye a lokacin da suka je wanka a Kogi da safe. Musa Abubakar mai shekara 25 da Isyaku Bashir, mai shekara 23 da kuma Nazifi Ibrahim mai shekara 19, duk sun rasu a lokacin da suka shiga dam don su yi wanka da misalin ?arfe 11:00…
Read MoreAl’ajabi: Wata Mata Ta Haifi Jaki A Zariya
An samu rabuwar kai a unguwar Tudun Wadan Zariya, bayan wata mai juna biyu ta yi ikirarin haifar wani nau’in halitta mai kama da jaki. Al’amarin matar mai suna Murja Abdulsalam, ya sanya mutane tururuwar zuwa gidanta da ke Layin Lemu domin gane wa idonsu. Matar mai shekara 45 ta bayyana wa Aminiya cewa kafin ta haihu abin da ke cikin nata, “Yana min yawo kuma ba na iya tafiya sosai,..Na je asibiti an ce ruwa ne. “Asibitin Dokta Umar nake zuwa; Na yi hoto sau biyu, sai ya nuna…
Read MoreOyo: Mamu Ya Dirka Wa Matar Liman Ciki
Rahotanni dake shigo mana daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na bayyana cewar Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ?irka wa matarsa ciki. Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar ta Oyo. Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ?a?a uku da bai da…
Read MoreNa Jima Ina Zina Da Dan Cikina – Wata Mata
Mummunan al’amari mai ban mamaki, duba da yadda wata mahaifiya ta bayyana yadda ta lalla?i ?anta ?an shekara 16 ya kwanta da ita su yi rayuwar aure saboda ta haihu. Amma haka lamarin ya faru ga Matina Agawua, ‘yar asalin Yelwata, wani yanki mai nisa a tsakanin jihar Nasarawa. Ta kwana da ?an da ta haifa tun a farkon aurenta don faranta wa sabon mijin nata wanda ke barazanar kawo karshen alakarsu matukar ba za ta ?auki ciki ba, kamar yadda The Nation ta rawaito. Abin ya zama abin ?yama…
Read MoreJaruma Aisha Tsamiya Za Ta Amarce
Labari mai dadi da ke bayyana a masana’antar Kannywood shi ne batun auren fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya. Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa za a daura auren a ranar Juma’a. Shafin Labaran Kannywood na Twitter ya fara wallafa labarin amma sai dai sun sanar da cewa jita-jita ce babu tabbaci. “Mun samu jita-jitar cewa a ranar Juma’ar nan mai zuwa jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce… Kuma angon nata babban mutum ne.” A karon farko, mun ci karo da wallafar jarumi Ali Nuhu inda ya saka hoton jarumar…
Read More2023: Kungiyoyin Arewa Sun Amince Da Takarar David Umahi
Daga Adamu Shehu Bauchi Kimanin Kungiyoyi goma sha tara ne wanda suka fito daga yankin arewacin Najeriya suka amince da takarar Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi a matsayin Shugaban kasa a zaben gamagari dake karatowa na shekarar 2023. Kungiyoyi wadan da suka dunkule su goma sha tara suka chure wuri guda da ake masu lakabi da Yan’rajin Shugabanci na Gari a Arewa, (AAGG) sunyi wan nan furucin ne a wajen wani taro da suka gudanar a cikin Jihar Bauchi. Kungiyoyin Matasan dai sunce su a halinda Najeriya take ciki…
Read MoreNa Jima Ina Karin Kumallo Da Naman Mutane – Aminu Baba Fitaccen Dan Kasuwa A Gusau
Alhaji Aminu Baba, fitaccen dan kasuwan nan da ke sana’ar motoci da sauran ababen hawa a kamfanin Aminchi Motors Gusau, Jihar Zamfara, ya bayyana munanan ayyukan sa. Baba, wanda ‘yan sanda suka kama, ya amsa laifin ci da sayar da sassan jikin mutane ga wasu da ba a san ko su waye ba. An kama shi ne a makon da ya gabata bisa laifin kashe wani yaro dan shekara 9 a Gusau. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba N Elkanah, ya ce wanda ake zargin yana da mata uku da…
Read MoreTashin Hankali: Matashi Ya Babbaka Uwarshi Har Lahira A Jihar Neja
Mazauna unguwar Darusalam da ke Minna, Jihar Naija sun tashi cikin ka?uwa da firgici bayan da wani matashi, mai suna Steven Jiya, ya bankawa mahaifiyarsa, Comfort Jiya wuta. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin ?in da ta gabata ne dai Steven, wanda ?an ?waya ne, ya dawo da ga garin Suleja a Jihar Naija ?in dai, inda bayan ya dawo gida ne, sai kawai ta raya masa cewa ya ?ona mahaifiyarsa. Jaridar ta ce a lokacin Comfort, wacce tsohuwar Shugabar makarantar sakandire ce, tana tsaka da girki…
Read MoreKetare: Faransa Ta Rufe Masallacin Da Ake Sukar Luwa?i Da Ma?igo
Ministan cikin gidan Faransa ya kaddamar da wani ku?iri na rufe wani Masallacin har na tsawon watanni shida “saboda irin wa’azi na tsattsauran ra’ayi da limamin masallacin ke yi.” Gerald Darmanin ya shaida wa tashar talabijin ta Cnews cewa ya “gabatar da” tsarin rufe masallacin da ke Beauvais, wani gari mai tazarar kilomita 100 daga arewacin birnin Paris, saboda “wa’azin da ba a yarda da shi ba”. Ya ce limamin Masallacin “ya mayar da hankali kan Kiristoci da ?an luwa?i da ma?igo da Yahudawa” a cikin hu?ubarsa. Hukumomin Oise, yankin…
Read MoreDPO Ya Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Kano
Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Shugaban ofishin ?an sanda na ?aramar hukumar Takai ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur’ani mai tsarki da aka rundunar ?an sandan jihar Kano ta shirya. DPO Mahi Ahmad Ali, ya zo na ?aya ne a gasar ajin izu 60, inda ya samu kyaututuka da dama da suka hada da ku?i da kyayyaki na amfanin yau da kullum. Gasar wacce aka kammala a ranar Alhamis ita ce irin ta farko da rundunar ?an sandan Kano ta gudanar ga jami’nta. ?an sanda…
Read More