Za A Kashe Naira Biliyan 25 Wajen Inganta Lafiya A Najeriya

images 2024 03 12T063814.559

Ministan lafiya da Walwalar Jama’a, Ali Pate, ne ya bayyana hakan sa’ilin da yake jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Tinubu ta yiwa harkar kiwon lafiyar ‘yan Najeriya garanbawul ta yadda zai dace dana sauran duniya. A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar, Deworitshe Patricia, ta fitar a jiya Lahadi a Abuja, Ministan yace, ba za’a iya samun nasarar yiwa harkar kiwon lafiya garanbawul da sabunta shi harma da samar da karin damammaki ba har sai an samu amincewar tsarin nan na hannu da yawa a bangaren lafiya…

Cigaba Da Karantawa

Fiye Da Yara Miliyan Guda Ke Mutuwa Duk Shekara A Najeriya – Ministan Lafiya

images 2024 03 12T063814.559

Ministan Lafiya a Najeriya, Farfesa Ali Muhammad Pate ya ce kimanin yara ƴan ƙasa da shekara biyar na mutuwa duk shekara sakamakon cututtuka ciki har da waɗanda rigakafi ke samar da kariya daga kamuwa da su. Ministan ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce kashi 70 cikin 100 na mace-macen ana iya kare su. “Bari mu yi bayani, akwai kimanin mace-macen yara miliyan ƴan ƙasa da shekara biyar duk shekara a ƙasar nan, kashi 70 na mace-macen…

Cigaba Da Karantawa

Cutar Sankarau Ta Hallaka Dalibai 20 A Jihar Yobe

IMG 20240229 WA0098

Labarin dake shigo mana daga Jihar Yobe na bayyana cewar, dalibai 20 sun mutu a wasu makarantun sakandaren kwana na ‘yan mata guda 3 da kuma Kwalejojin Gwamnatin Tarayya na ‘yan mata dake kananan hukumomin Potiskum da Fika a jihar Yobe sakamakon barkewar cutar da ake zargin sankarau ce. Kwamishinan iImin Firamare da Sakandare na jihar Yobe Muhammad Sani-Idris ya shaidawa manema labarai cewar “an tabbatar da rasuwar dalibai 20 a makonnin da suka gabata daga barkewar cutar da ake zargin sankarau ce a makarantun sakandaren kwana dake kananan hukumomin…

Cigaba Da Karantawa

Makon Shayarwa: An Shawarci Magidanta Su Rika Tsotson Nonuwan Matansu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kodinetan Cibiyar Kiwon Lafiya a matakin farko da ke Uyo, Peace Essien, ta yi kira da a rika jawo hankalin Iyalai da al’umma da kuma malaman addini sanin mahimmancin shayar da nonon uwa ga jarirai. A cewar jami’a Essien, mahaifin yaro wato baban sa na da muhimmiyar rawa da zai taka kafin mai dakin sa ta haihu wajen ganin kafofin nonuwa sun bude sannan su kasance a shirye don ciyar da jariri. Essien, yayin da yake zantawa da manema…

Cigaba Da Karantawa

Makon Shayarwa: An Shawarci Magidanta Su Rika Tsotson Nonuwan Matansu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kodinetan Cibiyar Kiwon Lafiya a matakin farko da ke Uyo, Peace Essien, ta yi kira da a rika jawo hankalin Iyalai da al’umma da kuma malaman addini sanin mahimmancin shayar da nonon uwa ga jarirai. A cewar jami’a Essien, mahaifin yaro wato baban sa na da muhimmiyar rawa da zai taka kafin mai dakin sa ta haihu wajen ganin kafofin nonuwa sun bude sannan su kasance a shirye don ciyar da jariri. Essien, yayin da yake zantawa da manema…

Cigaba Da Karantawa

Babu Wanda Ya Kamu Da Cutar Anthrax A Najeriya -NCDC

Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax – da wasu dabbobin ƙasar ke fama da ita – ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba. gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla a ƙasar. Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma’aikatar lafiyar ƙasar na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman…

Cigaba Da Karantawa

Kano Ce A Sahun Gaba Wajen Yawan Masu Cutar Mashako A Najeriya – NCDC

Hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce cutar mashako (diphtheria) ta kashe mutum 80 a kasar daga watan Mayu zuwa Yunin bana. A rahoton da hukumar ta fitar ta ce yanzu mutum 836 suka harbu da cutar kuma jihar Kano ce ta fi yawan wadanda suka kamu da ke da mutum 819. Hukumar ta ce alkaluman sun shafi kananan hukumomi 33 na jihohi bakwai da suka hada da Yobe da Katsina da Sokoto Zamfara da Kaduna da kuma Abuja. Ko a makon nan an bayar…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Uba Sani Ya Tura Tawagar Likitoci Domin Dakile Cutar Mashako

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya umarci ma’aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace kan ɓullar cutar mashaƙo a wasu yankunan jihar Ma’aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da bullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema’a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan. Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bayan samun rahotonnin ɓullar…

Cigaba Da Karantawa

Cutar Lassa Ta Lashe Rayuka 170 A Najeriya – NCDC

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu an samu rahoton mutuwar mutane 170 waɗanda suka kamu da zazzabin Lassa daga farkon shekarar nan zuwa yanzu mako na 27. Bayanin ya nuna cewa an samu mutuwar kashi 17.2 cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar, wanda ya yi ƙasa adadin waɗanda suka mutu bayan kamuwa da cutar a cikin irin wannann lokacin 2022 mai kashi 19.6 cikin ɗari. Wannan na kunshe ne a cikin sabon rahoton mako na 25 zuwa na 27 kan bullar…

Cigaba Da Karantawa

Cutar Mashako Na Neman Zama Annoba A Najeriya – NCDC

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da barkewar annobar mashako, tana mai cewa a yanzu an tabbatar da kamuwar mutane 798 a sassan kasar. Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce cikin mutane kusan 800 din da suka kamu, fiye da 654 na cikin wadanda suka ki karbar allurar rigakafin cutar. Sanarwar ta ce jihar Kano ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar da mutanen 782 mafi yawan su kananan yara ‘yan shekaru 2-14, yayin da kaso…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Tsunduma Yajin Aiki Muddin Ba A Cika Mana Alkawari Ba – Kungiyar Likitoci

Likitoci da ke aiki a asibitocin gwamnati sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ta cika musu alkawuran da ta daukar musu a jarjejeniya da suka cimma a baya. Gwamnatin da ta shude ce dai ta alkawarta warware duka matsalolin da kungiyar bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da likitocin suka yi a watan Mayu, to amma kungiyar ta ce babu abin da aka yi game da cika musu alkawari tun bayan da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki. A cikin wata sanarwa da kungiyar…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Da Pakistan Ne Ke Gaba Wajen Mutuwar Yara Sanadiyyar Zazzabin Cizon Sauro

Yara da matasa miliyan uku ne ke mutuwa a kowace shekara sakamakon cututtuka masu yaduwa, kwatankwacin mutuwar mutum daya a cikin duk dakika 10 Ƙasashen Indiya, Najeriya da Pakistan ne ke da mafi yawan mutane masu fama da irin wadannan cututtukan, a cewar wani sabon bincike da aka buga a mujallar Lancet. An gano cewa cututtuka masu yaduwa sun haddasa fiye da rabin irin wadannan mace-mace a kasashe masu karami zuwa matsakacin karfi, idan aka kwatanta da kashi 6 cikin 100 na kasashe masu karfin tattalin arziki, binciken da Cibiyar…

Cigaba Da Karantawa

Ba-Haya A Titi: Najeriya Na Bukatar Ban Daki Miliyan 4 Duk Shekara – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya za ta bukaci ban-ɗaki miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burin kawo karshen ba-haya a fili nan da shekarar 2025. Dakta Jane Bevan, shugabar sashen kula da ruwa da tsaftar mahalli ta UNICEF, ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron kwanaki biyu na masu sana’ar sana’ar ban-daki karo na farko a Abuja. Bevan ta ce yawan ban-dakuna da ake samarwa a kowace shekara a yanzu ya tsaya ne kan guda 180,000 – 200,000,…

Cigaba Da Karantawa

Ba-Haya A Titi: Najeriya Na Bukatar Ban Daki Miliyan 4 Duk Shekara – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya za ta bukaci ban-ɗaki miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burin kawo karshen ba-haya a fili nan da shekarar 2025. Dakta Jane Bevan, shugabar sashen kula da ruwa da tsaftar mahalli ta UNICEF, ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron kwanaki biyu na masu sana’ar sana’ar ban-daki karo na farko a Abuja. Bevan ta ce yawan ban-dakuna da ake samarwa a kowace shekara a yanzu ya tsaya ne kan guda 180,000 – 200,000,…

Cigaba Da Karantawa

Ba-Haya A Titi: Najeriya Na Bukatar Ban Daki Miliyan 4 Duk Shekara – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya za ta bukaci ban-ɗaki miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burin kawo karshen ba-haya a fili nan da shekarar 2025. Dakta Jane Bevan, shugabar sashen kula da ruwa da tsaftar mahalli ta UNICEF, ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron kwanaki biyu na masu sana’ar sana’ar ban-daki karo na farko a Abuja. Bevan ta ce yawan ban-dakuna da ake samarwa a kowace shekara a yanzu ya tsaya ne kan guda 180,000 – 200,000,…

Cigaba Da Karantawa

Noman Taba Na Haifar Da Karancin Abinci A Afirka – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce noman taba na haddasa matsalar karancin abinci da kayan abinci mai gina jiki a akasarin yankunan Afirka. Cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai domin bikin ranar yaki da shan taba sigari ta duniya, daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti ta ce ana amfani da gonakin da ya kamata a noma kayan amfanin gona wajen noma taba lamarin da ke lalata tsarin rayuwa tsakanin halittu. Moeti ta kara da cewa “muna fuskantar ƙalubale babba ta ɓangaren abinci da abinci mai…

Cigaba Da Karantawa

Cutar LASSA Ta Lashe Rayuka 154 A Najeriya – NCDC

Cibiyar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 154 a cikin jihohin ƙasar 26 tun farkon shekarar da muke ciki. A cikin rahoton yanayin cutar da cibiyar ta fitar ranar Litinin, NCDC ta ce a cikin watanni huɗun farko na shekarar 2023, an samu masu ɗauke da cutar 897. Cibiyar ta ce jihohin da aka samu cutar sun haɗar da Ondo da Edo da Bauchi da Taraba da Benue da Plateau da Ebonyi da Nassarawa da Kogi da Taraba da Gombe da…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: ‘Yan Jarida Sun Sha Alwashin Fadarkawa Kan Kiwon Lafiya

Daga Adamu Shehu Bauchi Yan’jarida masu dauko rahottanin kiwon lafiya a jihar Bauchi sunsha alwashin sauke nauyin dake rataye a wuyansu na fadakar da al’umma kan ababen da suka shafi matsalolin samar da ingantachiyar lafiya a matakai daban daban a fadin jihar. Sunsha wan nan alwashin ne yayin wani taron tattaunawa na kwana daya tare da hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Bauchi Da take tsokaci a lokacin taron Shugaban masu dauko rahottanin kiwon lafiya ta jihar Elizabeth Carr, tace sun kirayi shuwagabanin gidajen radiyo na al’umma dasu fahimci muhimmanci taimakekeniyar…

Cigaba Da Karantawa

An Samar Da Maganin Ciwon Zazzabin Lassa A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke inganta tsirrai da dabbobi ta Najeriya ta ce ta yi nasarar samar da maganin zazzabi Lassa, wanda ke halaka al`umma a wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya. Zazzabin Lassa dai ba shi da wani magani sadidan, cuta ce wacce ta daɗe tana kisa a Najeriya wadda aka tabbatar da ɓeraye ne ke haddasa ta. Amma yanzu hukumar ta ce jami`anta sun gano maganin, bayan shafe shekara shida suna gudanar da bincike, kuma a halin da…

Cigaba Da Karantawa

Likitoci Sun Bukaci Sanya Hannu A Dokar Kare Hakkin Mata

Ƙungiyar likitoci masu lura da lafiyar mata ta ƙasa ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar kare lafiyar mata da jarirai. A cewar ƙungiyar hakan zai zamo wani abin tarihi, wanda al’ummar ƙasar ba za su manta da shi ba. Shugaban ƙungiyar, Dr Habib Sadauki ne ya buƙaci hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi. Sadauki ya ce dokar za ta taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna-biyu da jarirai. Ya ƙara da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da…

Cigaba Da Karantawa