Muna Da Rahotannin Sirri Na Masu Ɗaukar Nauyin ‘Yan Bindiga – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewar akwai rahotanni da bayanan sirri da take dasu dangane da masu ɗaukar nauyin ‘yan Bindiga a Najeriya musamman yankin Arewacin kasar, kuma nan gaba ba da dadewa ba za ta fallasa su. Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya tabbatar da hakan, inda ya ce wasu mutane suna amfani da damar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar don amfanar kansu da kansu domin cimma manufofin su na son zuciya. Da yake magana a ranar Talata bayan taron majalisar tsaron kasa…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Da Amurka Za Su Haɗa Ƙarfi Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda

Ƙasar Amurka ta bayyana goyon bayan ta akan yaƙi da ta’addanci da ‘yan ta’adda da Najeriya ke yi, sannan ta yi alkawarin haɗa karfi da Najeriya wajen kawo karshen ‘yan ta’adda dake addabar kasar musamman yankin Arewacin kasar. Amurka ta bayyana hakan ne a yayin ganawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da kwamandan Sojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka Janar Stephen Townsend ya yi a birnin tarayya Abuja. Kwamandan Sojin Amurka a yankin Afirka, Janar Stephen Townsend ya ce za a kawo jiragen nan guda goma sha biyu na…

Cigaba Da Karantawa

Har Yanzu Ɗaliban Jangeɓe Na Hannun ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Zamfara

Rahotonni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Daliban da aka sace daga makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati dake Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su, in ji gwamnatin jihar. Yusuf Idris, mai taimaka wa Gwamna Bello Matawalle a harkar yada labarai, ya shaida wa manema labarai haka da yammacin ranar Lahadi cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an sake su. Gwamnatin ta Zamfara ta yi wannan bayani ne biyo bayan rahotannin da…

Cigaba Da Karantawa

Kungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Koka Akan Matsalar Tsaro Dake Addabar Najeriya

Kungiyar gidajen yaɗa labarai Talabijin da Rediyo masu zaman kansu na ƙasa, ta koka dangane da halin da matsalar tsaro ke cigaba da addabar ƙasa musamman yankin Arewacin Najeriya. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar ranar Asabar wacce take ɗauke da sanya hannun Shugaban kungiyar na ƙasa Guy Murray Bruce da mataimakin shi Alhaji Tijjani Ramalan kuma aka rarraba ta ga manema labarai. Kungiyar ta bayyana cewar halin da tsaro ke ciki yanzu a Najeriya tabbas abin tsoro da fargaba ne akan makomar…

Cigaba Da Karantawa

Akwai Dalilin Da Yasa Ba Za Mu Murkushe ‘Yan Bindiga Ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin tsananin fushi ya gargadi ‘yan bindiga da ke adabar al’umma a sassan kasar musanman Arewacin Najeriya da cewa gwamnatinsa za ta iya yin maganin su, cikin ƙanƙanin lokaci ba domin wani dalili ba. A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan karuwar ayyukan bata gari a ƙasar inda ya ce ba domin ana iya amfani da wadanda aka sace a matsayin garkuwa ba wanda zai haifar da salwatar rayyuka, da tuni…

Cigaba Da Karantawa

Tu’ammali Da Kwayoyi Na Taka Rawa Wajen Tabarbarewar Tsaro – Marwa

Shugaban hukumar yaki da fatauci da ta’amulli da miyagun kwayoyi, NDLEA, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai murabus) a ranar Alhamis, ya koka gami da yin gargadi kan karuwar ta’amulli da miyagun kwayoyi a Nijeriya, da rawar da hakan ke takawa wajen gurbatar tsaro. A cewarsa, masu garkuwa da mutane da sauran bata gari sun fara neman a biya su fansa da miyagun kwayoyi a maimakon kudi kafin su sako wadanda suka sace, wanda hakan babbar barazana ce ga harkar tsaro. Sanarwar da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnonin Arewa Sun Sha Alwashin Shawo Kan Matsalar Tsaro Dake Addabar Yankin

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Kungiyar Gwamnonin Arewa a bisa irin matakan da suke dauka na ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da ya addabi yankin baki daya. Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Shugaban ma’aikatan fadan Gwamnati Ibrahim Gambari, a yayin da ya wakilci shugaban ƙasa wajen buɗe taro kan matsalar tsaro da tattalin arziki Gwamnoni da Sarakunan Arewa suka shirya a Gidan Gwamnati na tunawa da Sir Kashin Ibrahim dake Kaduna. Buhari ya bayyana cewa, duk da kokarin da Gwamnonin Arewan ke yi, ya zama wajibi…

Cigaba Da Karantawa

Akwai Yiwuwar Gwamnoni Su Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Manyan alamu sun bayyana cewa Kungiyar gwamnonin Najeriya na wani shiri domin yin zaman sulhu da miyagun ‘yan bindiga dake addabar kasar musamman yankin Arewacin Kasar da nufin kawo zaman lafiya dawamamme a faɗin Najeriya. Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Dr. Kayode Fayemi ya nuna yiwuwar yin hakan a ranar Talata, bayan ya kai wa gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ziyarar jaje na garkuwa da ɗaliban Makarantar Kagara da ‘yan Bindiga suka yi. Gwamna Kayode Fayemi ya ziyarci abokin aikin na sa ne tare da wasu takwarorinsa a garin Minna.…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ce Sahun Gaba Wajen Yawan Matalauta A Duniya – El Rufa’i

An bayyana cewar Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace kasa fama da talauci da kuma yawan matalauta a faɗin duniya gaba daya, kuma lamarin ya ƙara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun nan. Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin kaddamar da Hukumar Kula da Kare Lafiyar Jama’a a jihar ranar Talata. El Rufa’i ya ce gwamnatinsa ta kafa hukumar ne don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen kula da kare rayuwa da zamantakewa an isar da su cikin hadaka, mai kunshe da ci gaba. Gwamnan ya…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Na Sahun Gaba Wajen Yawan Matalauta A Duniya – El Rufa’i

Gwamna Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewar Najeriya na sahun gaba wajen fama da yawan matalauta a faɗin duniya, sannan tabbas ita ce ƙasar da ta fi kowacce kasa talauci a jerin kasashen duniya. Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin kaddamar da Hukumar Kula da Kare Lafiyar Jama’a a jihar ranar Talata. El Rufa’i ya ce gwamnatinsa ta kafa hukumar ne don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen kula da kare rayuwa da zamantakewa an isar da su cikin hadaka, mai kunshe da…

Cigaba Da Karantawa

Hauhawar Farashin Mai: Buhari Zai Gana Da Gwamnoni

Babban Ministan Kwadago a tarayyar Najeriya Mista Chris Ngige ya ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da gwamnonin jihohi inda za su tattauna a kan hauhawar farashin fetur dake tunkarar ƙasar. Sanata Chris Ngige ya na cewa za ayi wannan zama ne a ranarAlhamis, 25 ga watan Fubrairu, 2021. Chris Ngige ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, bayan ya jagoranci gwamnatin tarayya yi zaman karshe da kungiyoyin kwadago a fadar Shugaban ƙasa ta Aso Rock. Ministan ya ce sun duba aikin da kwamitin da aka kafa domin…

Cigaba Da Karantawa

Ya Kamata Najeriya Ta Koma Salon Mulkin Shugaban Kasa Na Jeka Nayi Ka – Na’ Abba

An bayyana cewar salon tsarin mulki da Najeriya ke kai a halin yanzu na Shugaban ƙasa mai cikakken iko ko kaɗan bai dace da tsari na ƙasar Najeriya ba, domin ya bada wata dama ce ga shugaban kasa na yin mulkin danniya, wanda hakan ya taimaka gaya wajen jefa kasar halin da take ciki na koma baya a yanzu. Tsohon Shugaban majalisar wakilai na Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’ Abba ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da shi a cikin shiri na musamman mai suna “State Of Union” na Gidan…

Cigaba Da Karantawa

Ya Kamata Najeriya Ta Koma Salon Mulkin Shugaban Kasa Na Jeka Nayi Ka – Na’ Abba

An bayyana cewar salon tsarin mulki da Najeriya ke kai a halin yanzu na Shugaban ƙasa mai cikakken iko ko kaɗan bai dace da tsari na ƙasar Najeriya ba, domin ya bada wata dama ce ga shugaban kasa na yin mulkin danniya, wanda hakan ya taimaka gaya wajen jefa kasar halin da take ciki na koma baya a yanzu. Tsohon Shugaban majalisar wakilai na Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’ Abba ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da shi a cikin shiri na musamman mai suna “State Of Union” na Gidan…

Cigaba Da Karantawa

Laifin Gwamnonin Yarbawa Ne Kisan Da Ake Yi Wa ‘Yan Arewa A Kudu – Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ranar Asabar ya soki lamirin gwamnonin Yarbawa dake sashin kudu maso yamma, inda ya ɗaura musu alhakin kashe-kashen da akayi wa al’ummar Arewa da ya faru a kasuwar Shasha a Ibadan, jihar Oyo. A cewar Lawan, gwamnonin ne suka tunzura matasan yankin wajen kaiwa yan Arewa hari. A hirar da yayi da sashin Hausa na BBC Hausa, Lawan ya ce kiran da wasu gwamnonin kudu maso yamma keyi na korar Fulani daga yankin ya haifar da hakan. Shugaban Majalisar ya ƙara da cewar ko…

Cigaba Da Karantawa

Izala Ta Fi Ta’addanci Da Garkuwa Da Mutane Muni – Ɗahiru Bauchi

Mashahurin Malamin Ɗarikar Tijjaniya a Najeriya Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya yi kira da babbar murya ga Fulani Makiyaya masu aikata ta’addanci da yin garkuwa da mutane cewa, su kula matuƙa akan halin da suke ciki, ka da akai ga matsayin da za su faɗa cikin Ƙungiyar Izala bayan ayyukan ta’addanci da suke yi, saboda munin Izala ya fi ta’addancin da suke ciki. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai dangane da halin da matsalar tsaro da ya addabi yankin Arewacin Najeriya…

Cigaba Da Karantawa

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Sake Farfadowa

Rahotonni daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa na bayyana cewar tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 0.11 bisa dari a zango na hudu na shekarar 2020, wanda ke wakiltar ci gaban farko a cikin zango uku da suka gabata. Rahoton ya cigaba da cewar “Koda yake yana da rauni, ci gaban da aka samu yana nuna yadda ayyukan tattalin arziki ke dawowa sannu a hankali biyo bayan cire dokar takaita zirga-zirga da kuma takaita ayyukan kasuwanci na cikin gida da waje a zangon da suka gabata. “A sakamakon haka, yayin…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Sayar Da Manyan Kadarorin Gwamnati 36

Gwamnatin Nijeriya na shirin sayar da kimanin manyan kadarorin gwamnati kusan 36 don samun kudin da za ta tunkari kasafin shekarar nan ta2021. Jaridar Premium Times wace ta sanar da mallakar takardun da gwamnati ta rubuta wannan kuduri nata ta ce ana shirin sayar da kadadorin ko kuma bayar da su aro domin cike gibin da za a iya samu a wurin aiwatar da kasafin kudin wannan shekara. Kadarorin gwamnati da ake shirin cefanarwa ko kuma bayar d aro sun hada da bangaren lantarki kamar hukumar TCN da banagren sadarwa…

Cigaba Da Karantawa

Kisan ‘Yan Arewa: Babu Batun Yin Ramuwa – Gwamnonin Arewa

Kungiyar gwamnonin Arewa sun bukaci mutanen arewacin Najeriya da kar su dauki fansa kan ‘yan kudu da ke zaune a kowane yanki na arewa saboda rikicin kabilanci da ake fuskanta a wasu sassan jihar Oyo. Kungiyar ta lura cewa irin wannan matakin ba zai magance matsalar da kasar ke fuskanta ba a yanzu, amma zai kara fadada ta. Sai dai kuma, kungiyar ta gwamnonin Arewa ta ba mutanen Arewa tabbacin cewa tana yin duk abunda ya dace don magance matsalar da ta shafi wasu ‘yan arewa a jihar Oyo. Gwamna…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindigar Arewa Sun Samu Horo Ne Wajen Tsagerun Neja Delta – Gumi

Mashahurin Malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya yi ƙarin haske akan yadda ayyukan ‘yan Bindiga ke gudana, inda ya tabbatar da cewa da akwai dangantaka ta ƙut da ƙut tsakanin ‘yan bindigar da tsagerun Neja Delta, wanda ya kamata gwamnati ta fahimta kuma ta ɗauki matakin sulhu da yafiya domin samun nasara. Dr. Gumi ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata 16 ga watan Fabarairu, inda ya bayyana cewa a wurin tsagerun…

Cigaba Da Karantawa

Osinbanjo Ya Yi Tir Da Kisan ‘Yan Arewa A Kudanci

Mataimakin Shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi tir gami da Allah wadai da kisa tare da harin da ake kaiwa yan Arewa a Kasuwar Shasha Ibadan. Mataimakin Shugaban kasar ya siffanta hakan a matsayin dabbacin kuma abin kunya tsakanin Hausawa da Yarbawa, waɗanda aka san su a matsayin ‘yan uwa kuma abokanan zama shekaru da dama. A cewarsa, kasuwar Sasha kasuwace da Hausawa ke rayuwa tare da Yarbawa tsawon shekaru, cikin zama na lumana da amana. “Babu shakka wannan abin da ya faru aikin Shaiɗan ne da ya kamata kowa…

Cigaba Da Karantawa