‘Yan Shi’a Na Barazanar Kasheni Sakamakon Kwaikwayon Zakzaky – Peter Edochie

Jarumin finafinan Kudun ya ce tun kafin fim din ya fita kasuwa har ya fara samun sakonnin barazanar kisa ta hanyar kafofin sadarwa ta zamani. Wanda ya bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga rayuwarsa. Peter Edochie ya kara da cewar ‘ya’yan kungiyar Shi’a ne ke aiko da masa da barazanar kisa, sakamakon fitowa da ya yi a matsayin jagoransu Zakzaky, wanda kowa ya sani cewa wasan kwaikwayo ne ya yi. “Ina amfani da wannan dama in sanar da jami’an tsaro da iyalina da sauran jama’a baki ɗaya cewar rayuwata…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Farashin Kayan Abinci Ya Faɗi Warwas

A yayin da al’ummar Najeriya kokawa kan tashin farashin kayan abinci, farashin kayan abinci ya fadi da kamar kashi 30 a babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna. Shi dai wannan yanki na Saminaka, shi ne kan gaba a wajen noman masara a Najeriya.Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwar hatsin da ke ci a kowace ranar Laraba, ya gano farashin kayan abincin ya fadi kasa warwas. Wakilinmu ya gano cewa buhun sabuwar masara da ake sayarwa kan N15,000 mako biyu da suka gabata, yanzu ta komo…

Cigaba Da Karantawa

Waƙar Buhari: Na Sha Mamaki Na Miliyoyin Da Talakawa Suka Tara – Rarara

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ce ya yi matukar mamakin gano cewa ashe kaunar da talakawa ke yi wa Shugaba Buhari ta wuce yadda ya ke tsammani. Rarara ya yi wannan furucin ne sakamakon adadin kudin da ya ga ‘yan Najeriya sun tara masa bayan ya nemi mutane su bayar da N1,000 domin ya yi wa Buhari sabbin wakoki. Duk da cewa bai bayyana adadin kudin da aka tara ba kawo yanzu, Rarara ya ce cin mutunci ne a ce N70m kacal aka tara cikin kwanaki uku don…

Cigaba Da Karantawa

Kano Ce Kan Gaba Wajen Jin Daɗin Alhazzai A Najeriya – NAHCON

Hukumar Jin dadin Alhazai ta kasa ta bayyana Hukumar Jihar Kano a matsayin hukumar dake kan gaba bisa sauran jihohin kasar, sannan ta kara da cewa hukumar na kula da kuma tabbatar da hanya mafi sauki ga Alhazan jihar. Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Babban shuguban Hukumar jin dadin Alhzan ta Kasa Mallam Zikurullah kunle Hassan, bayan ziyar da ya kaiwa mai girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi umar Ganduje a masaukin sa bayan kammala taron Koli a fadar Mulki ta Aso a ranar Litinin din nan. Shugaban Hukumar…

Cigaba Da Karantawa

Zunubi Ne Babba Tura Wa Rarara Kudin Waƙa – Limamin Haɗeja

Sheikh Yusuf Abdulrahman Ya’u, wanda shi ne babban limamin garin Hadejiya, jihar Jigawa, ya yi magana game da kudin da ake tarawa Dauda Kahutu Rarara, inda ya ce a halin da ake ciki, bai kamata a bijirowa talaka da maganar bada gudumuwa domin ayi wa shugaban kasa Buhari wata waka ba. Shehin Malamin ya yi wannan bayani ne a wajen karatun littafin Adabul – Mufrad kamar yadda wani faifen bidiyo da ya shigo hannun mu ya bayyana. Limamin ya ke tsokaci ya na cewa: “Kuma ana wannan yanayin wani ya…

Cigaba Da Karantawa

Sukar Gwamnati: DSS Ta Gayyaci Mahadi Shehu

Hukumar tsaro ta farin kaya ta gayyaci sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu, domin amsa tambayoyi biyo bayan wasu kalamai da ɗan kasuwar ke yawan furtawa musanman akan batun tsaro na jihar Katsina. Da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Litinin ne Dr Mahadi ya bayyana ofishin hukumar da ke garin Kaduna, tare da rakiyar tarin wasu matasa wadanda suke rike da manyan kwalaye waɗanda aka yi wa rubuce rubucen neman adalci, da rera wakokin yabo da jinjina gareshi. Da yake zantawa da manema labarai jim…

Cigaba Da Karantawa

Rikicin Ƙungiyar Lauyoyi: Lauyoyi Sun Nemi A Cire Wa Malami Muƙamin Shi

Lauyoyi sama da 300 a Najeriya su ka neman a tsigewa ministan shari’an Najeriya, Malam Abubakar Malami, mukaminsa na babban Lauya watau SAN. Jaridar Punch ta ce wadannan lauyoyi sun bukaci a cirewa babban lauyan gwamnatin tarayya mukaminsa na SAN ne a dalilin yunkurin ragewa kungiyar su karfi. Wani mai suna Izu Aniagu, shi ne ya kirkiro wannan korafi a shafin yanar gizo, inda ya ke kira ga sauran mutane su taya shi kiran a cirewa ministan mukaminsa. Mista Izu Aniagu ya yi wa wannan korafi taken ‘Sa hannu a…

Cigaba Da Karantawa

Babu Komai A Mulkin Buhari Sai Tashin Hankali – Gurgun Da Ya Taimaki Buhari

A ‘yan kwanakin nan ana ta yawo da hoton mutumin a sabbin kafafen sadarwa inda al’umma da dama suka dunga bayyana ra’ayoyi game da mutumin har ana cewa ya sha jar miya, a saboda haka ne abokin aikin mu Shuaibu Abdullahi, ya yi tattaki don jin shin kwalliya ta biya kudin Sabulu? To sai dai Malam Abdullahi Aliyu, mazaunin Jihar Kaduna, ya ce babu wani abun da ya amfana da shi a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, banda tashin hankali, tsadar kayayyakin abinci, gashi ana ta kashe musu ‘yan uwa…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Faɗuwar Gini Ya Hallaka Amarya

Da yammacin ranar Juma’ah ne wani munnan lamari ya faru a Unguwar Gafai cikin Birnin Katsina wanda ya saka mutane cikin juyayi da kuka na rasuwar wata baiwar Allah mai suna Fateema Junaidu, ta bar gidan mijinta zuwa Unguwar domin taya wata daga cikin Aminan arziki murnar samun karuwa, ma’ana taje bikin suna. To dayake a Unguwarsu ake sunan wajen gidan mahaifanta, daga gurin sunan taje gidansu domin gaishe da mahaifiyarta, da sauran danginta dake cikin gidan dama yankin Unguwar baki Daya, saboda mafi yawan yan Unguwar ‘Yan’uwan juna ne.…

Cigaba Da Karantawa

Ciwon ‘Ya Mace: Sun Sayi Mota Domin Kai ‘Yan Uwansu Mata Asibiti

Matan wadanda suke zaune a wani kauye da ake kira Bordo a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa a Nijeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna biyu zuwa asibiti domin haihuwa. Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan bukatar hakan ta taso musammamma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin. Daga kauyen zuwa asibitin Jahun da ake kai matan haihuwa akwai tazarar kilomita 29, kuma kauyen ya kasance a lungu…

Cigaba Da Karantawa

Musulmi Na Cikin Mawuyacin Hali A Najeriya – Sheikh Gwauron-Dutse

Babban malamin addinin musulunci a Kano Sheik Nasidi Abubakar Goron-Dutse ya koka a kan rayuwar kunci da yan Nijeriya ke ciki musamman musulmi. Malamin, ya nuna damuwarsa a kan yadda wahalhalu, hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi ke karuwa a kasar. A cikin gajeren faifan bidiyon malamin da ya yi magana malamin ya ce wannan shine lokaci mafi muni da ya taba ganin musulmin Najeriya sun shiga. A dukkan rayuwa ta, ban taba ganin musulmin Nijeriya cikin kunci wanda ya fi wannan ba. Malamin ya cigaba da kira ga…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Rayuwa: Addu’o’in Da Manzon Allah Ke Yi – Sheikh Sani Khalifa

A wannan gaba da muke ciki na tsananin rayuwa saboda tsadar abinci da talauci, babu abinda zai fitar da mu sai addu’a, maimakon yawan zagi da zargi ya kamata mu koyi abinda manzon Allah saw yake yi idan ya rasa abinci a gidansa. Imamul Tabarani ya ruwaici hadisi cewa : wata rana manzon Allah saw zai yiwa bako liyafa sai ya aika wajen matayensa da a nemo abinci, da aka je sai ba’a samu abinci a wajen dukkan matansa ba, da aka dawo aka fada masa cewa babu abinci a…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Rayuwa: Addu’o’in Da Manzon Allah Ke Yi & Sheikh Sani Khalifa

A wannan gaba da muke ciki na tsananin rayuwa saboda tsadar abinci da talauci, babu abinda zai fitar da mu sai addu’a, maimakon yawan zagi da zargi ya kamata mu koyi abinda manzon Allah saw yake yi idan ya rasa abinci a gidansa. Imamul Tabarani ya ruwaici hadisi cewa : wata rana manzon Allah saw zai yiwa bako liyafa sai ya aika wajen matayensa da a nemo abinci, da aka je sai ba’a samu abinci a wajen dukkan matansa ba, da aka dawo aka fada masa cewa babu abinci a…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Rayuwa: Addu’o’in Da Manzon Allah Ke Yi – Sheikh Sani Khalifa

A wannan gaba da muke ciki na tsananin rayuwa saboda tsadar abinci da talauci, babu abinda zai fitar da mu sai addu’a, maimakon yawan zagi da zargi ya kamata mu koyi abinda manzon Allah saw yake yi idan ya rasa abinci a gidansa. Imamul Tabarani ya ruwaici hadisi cewa : wata rana manzon Allah saw zai yiwa bako liyafa sai ya aika wajen matayensa da a nemo abinci, da aka je sai ba’a samu abinci a wajen dukkan matansa ba, da aka dawo aka fada masa cewa babu abinci a…

Cigaba Da Karantawa

Sai An Biya Ni Kudi Kafin In Saki Sabuwar Waƙar Buhari – Rarara

Fittacen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yace zai je har fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin neman yafiyar sa akan ba ta masa suna da makiyan sa keyi ta shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai, kuma zai je wajen shugaban ne a madadin talakawan Nijeriya. Rarara ya ce, gwamnatin APC na kokari matukar gaske, wajen ganin ta samar da cigaba, saidai kuma cutar korona bairos ta kawo mata cikas, kuma zai yi waka mai suna ‘’Kainuwa” wacce zai bayyano ayyukan shugaban kasa guda 192, kuma talakawan…

Cigaba Da Karantawa

Sai An Bani Kuɗi Kafin In Fitar Da Sabuwar Waƙar Buhari – Rarara

Fittacen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yace zai je har fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin neman yafiyar sa akan ba ta masa suna da makiyan sa keyi ta shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai, kuma zai je wajen shugaban ne a madadin talakawan Nijeriya. Rarara ya ce, gwamnatin APC na kokari matukar gaske, wajen ganin ta samar da cigaba, saidai kuma cutar korona bairos ta kawo mata cikas, kuma zai yi waka mai suna ‘’Kainuwa” wacce zai bayyano ayyukan shugaban kasa guda 192, kuma talakawan…

Cigaba Da Karantawa

Legas: ‘Yan Sanda Sun Damke Masu Zanga-zangar Farashin Mai

‘Ya’yan jam’iyyar SPN tare da hadin gwiwar matasa a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin mai da na wutar lantarki. Sai dai jami’an ‘yan sanda sun tarwatsa gungun masu zanga-zangar tare da kama wasu daga cikin jagororin zanga-zangar. An kama masu zanga-zangar ne a yau, Alhamis, a yankin Ojuelegba da ke garin Legas. Bayan masu zanga-zangar da aka kama, an kwace kayan aikin wasu ‘yan jaridu. Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Hassan Soweto, ya ce an kama mutum 18 da suka hada da…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnati Za Ta Kafa Kwamitin Samar Da Hanyoyin Kai Agaji A Arewa Maso Gabas – Sadiya

Gwamnatin Tarayya za ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai samar da hanyoyi mafi sauƙi da za a rinƙa kai agaji ga waɗanda rikicin yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya ya shafa. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Kyautata Rayuwar Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a cikin wata takardar bayani ga manema labarai a Abuja ran Litinin. A cewar ta, rashin samun kaiwa ga jama’ar da rikicin ya shafa wani babban abin damuwa ne. A takardar, wadda hadimar musamman kan yaɗa labarai ta ministar, Nneka Anibeze,…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Ilimin Addini Ne Ke Haifar Da ‘Yan Ta’adda – Sheikh Lau

An bayyana cewar rashin samun ilimin addinin Musulunci yadda ya kamata shine ke haifar da samuwar ‘yan ta’adda musamman a yankin Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar Izala ta ƙasa baki daya Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana hakan lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna. Sheikh Lau ya ƙara da cewar a halin yanzu Ƙungiyar ta su za ta mayar da hankali sosai wajen yin da’awa da karantar da Fulanin Daji da ke rayuwa a rugage, kasancewar yadda ake yawaitar samun ‘yan ta’adda da masu garkuwa da…

Cigaba Da Karantawa

Ba Mu Fatan Sake Ganin Mulki Irin Na Buhari A Najeriya – Ustas Albani

Malamin ya ce sannanen abu ne idan aka ce matsalar tsaro ta ki ci balle cinyewa a arewacin Nijeriya. Ya kara da cewa da farko mayakan ta’addancin Boko Haram sun addabi yankin Arewa maso gabas, amma yanzu ‘yan bindiga sun gangaro yankin arewa ta yamma da ta tsakiya. Wannan matsalar ta kasance tana ciwa jama’a da dama tuwo a kwarya. Sheik Adam Albani wanda fitaccen Malami ne wanda lamarin ya matukar saka shi cikin damuwa a wani bidyonsa da ya bayyana, inda yake yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.…

Cigaba Da Karantawa