Kaduna: El Rufa’i Ya Rushe Makarantar Da Ake Lalata Da ‘Yan Mata

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya rushe makarantar Liberation Collage dake cikin garin Kaduna bayan an samu mai makarantar Mista Samuel Ejikeme da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara tara fyade. Wani dalilin da ya kara tunzura gwamnatin yin rushe makarantar kamar yadda wani hadiminsa a fannin yada labarai Abdallah Yunus Abdallah ya bayyana, shine rashin samun sahalewar gwamnati kafin gina makarantar. Kazalika aka samu Mista Samuel na amfani da makarantar wurin lalata yaran mutane.

Cigaba Da Karantawa

Ilimi: Makarantu Masu Zaman Kansu Zasu Koma Bakin Aiki

Ma’aikatar ilimi a Nijeriya ta baiwa masu makarantu har zuwa ranar 29 ga watan Yuli su cika ka’idojin da ta gindya musu na sake bude makarantu. Wata sanarwa da ta samu sa hannun darakatan yada labarai na ma’aiktar ilimin Ben Bem Goong ta ruwaito karamin minister a ma’aikatar na cewa wannan yunkuri na cewa wannan mataki na zuwa ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatar lafiya, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa da sauransu. A cewar sanarwar, ma’aikatar ilimin ta gana da hukumar shirya…

Cigaba Da Karantawa

Ilimi: Gwamnatin Tarayya Da WAEC Sun Cimma Matsaya

Gwamnatin tarayya da hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta yamma, sun cimma matsayar sauya ranar jarabawa. A maimakon fara jarabawar a ranar 4 ga watan Augusta da ta sanar da farko, za a fara a ranar 5 ga watan Satumban 2020. Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya sanar da hakan a Abuja, ya ce wannan ne sakamakon taron gwamnatin tarayya da shugabannin hukumar a Najeriya wanda aka yi a ranar Litinin. Sannan dukkan bangarorin sun amince da tuntubar kasashe hudu a kan sabuwar ranar fara jarabawar. Ministan…

Cigaba Da Karantawa

Ɗaliban Jihohin Mu Zasu Rubuta Jarrabawar WAEC – Gwamnonin Yarbawa

Gamayyar kungiyar Gwamnonin kudu maso yamma jihohin Yarabawa sun cimma matsaya akan bude makarantu a fadin jihohinsu. Gwamnonin sun cimma matsayar bude makarantun bayan sun gudanar da taro ta Zoom. Gwamnonin sun ce matakin bude makarantun ya zama dole saboda a baiwa dalibai ‘yan ajin karshe na sakandare damar rubuta jarabawar karshe ta WAEC. Gwamnonin da suka goyi bayan kudurin sun hada da Gwamnan Legas, Oyo, Osun, Ogun, Ondo da kuma Ekiti. Matakin da Gwamnonin suka dauka ya saba da na Gwamnatin tarayya inda ta jadada ba za ta bari…

Cigaba Da Karantawa

Soke Jarrabawar WAEC: Muna Nan Akan Matsayar Mu – Gwamnatin Tarayya

Yayin da ake tsakiyar sukar matsayar da gwamnatin tarayya ta dauka cewa dalibai masu fita sakandare a 2020 ba za su rubuta jarabawar WASSCE a 2020 saboda annobar Coronavirus ba, gwamnati kuma a na ta bangare na ci gaab da kare dalilai da hujjojin ta na kin barin dalibai a Najeriya su rubuta jarabawar ta fita sakandare. Cikin makon jiya PREMIUM TIMES ta buga labarin da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a bana dalibai ‘yan ajin karshe na sakandare ba za su zauna jarabawar ba, saboda barkewar cutar Coronavirus. Cikin…

Cigaba Da Karantawa

Aikin Allah: Gwamnan Zamfara Ya Ba Izala Gudummuwar Naira Miliyan 100

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bawa kungiyar ‘Jama’atu Izalatil Bidah Wa Ikamatul Sunna (JIBWIS)’ tallafin N100m domin gina jami’ar Musulunci a jihar Jigawa. Zailani Bappa, kakakin Gwamna Matawalle, ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da bayar da tallafin kudin ne yayin da ya karbi bakuncin shugabancin kungiyar JIBWIS a karkashin shugabanta na kasa, Sheikh Bala Lau, a fadar gwamnatin jihar dake Gusau. Matawalle ya bayyana cewa babu adadin wani kudi da za a ce ya yi yawa matukar an bayar da shine domin inganta harkar…

Cigaba Da Karantawa

CORONA: Muna Kira Ga Gwamnati Ta Buɗe Makarantu – Jingir

Shugaban majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga gwamantin tarayya da na jahohi da su bude makarantu don a cigaba da koyo da koyarwa a ciki. Sheikh Sani Jingir ya kara da cewa ko kasar Sin da Amurka da suke da anmobar sun bude makarantu ana ci gabada koyarwa. Amma a Nijeriya da ba annobar an rufe yara a gida an hana su zuwa makaranta. Sheikh Sani ya ci gaba da cewa akwai wasu masu mugun nufi ga ‘yan Nijeriya a…

Cigaba Da Karantawa

Kuskure Ne Babba Dakatar Da Jarrabawar WAEC A Najeriya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya nuna rashin jin daɗinsa bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da gudanar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a ƙasar. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai hanyoyin da gwamnatin za ta iya bi wurin gudanar da jarrabawar ba wai ta dakatar da ita baki ɗaya ba. Cikin hanyoyin da ya lissafo akwai batun amfani da manyan ɗakunan taro na ƙasar da makarantun firamare da filayen wasanni da sauran wurare domin amfani da…

Cigaba Da Karantawa

Zamu Zamanantar Da Makarantun Allo -Hukumar Kula Da Harshen Larabci

YUNKURIN ZAMANTAR DA MAKARANTUN ALLOukumar dake kula da harshen larabci ta kasa (NBAIS) tayi alkawarin bada takardan shahada wato (Certificate) ga al’majirai tsangaya. Hukumar za ta fara tantance dukkan daliban Tsangaya, Kolawa, Kotsawa, Gardawa da Alarammomi don basu takardan shaida wato (certificate) a fadin kasar nan don ganin ta inganta har kar ilimin Tsangaya. Jihar Gombe na cikin sahun farko da zasu amma fana da shirin, wanda hukumar zata ai watar da zaran samu saukin wanna annoba da ya addabi duni wato covid19. Yayin da suke baiyana dalilin su na…

Cigaba Da Karantawa

Hukumar WAEC Ta Fitar Da Jadawalin Zana Jarrabawa

Hukumar shirya jarrabawar kammala karantun sakandire ta Yammacin Afrika, WAEC, ta fidda jadawalin jarrabawar shekarar 2020. Babban jami’in hukumar WAEC a Najeriya, Mista Patrick Areghan, shi ne ya bayyana a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin kasar na tarayya wato Abuja. Ya tunatar da manema labarai yadda annobar korona ta wajabta dage jarrabawa wadda a baya aka kudiri gudanar da ita a tsakanin ranar 6 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Yuni. Ya ce a halin yanzu bayan bita kan halin da ake ciki, za…

Cigaba Da Karantawa

Buɗe Makarantu: Gwamnatin Tarayya Zata Gana Da Jihohi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gana da jihohi ranar Talata don tattaunawa kan hanyoyin sake bude makarantun firamare da sakandire. A yanzu haka dai Makarantu fadin kasar suna nan a kulle, tun cikin watan Maris sakamakon barkewar cutar corona virus a cikin kasar wanda ya haifar da ‘yan Najeriya sama da mutum 25,000, sun harbu da cutar. Shugaban kwamitin yaki da cutar corona virus, Boss Mustapha, a ranar Litinin ya ba da sanarwar sake bude makarantun, yana mai cewa hakan zai ba da damar baiwa daliban da ke…

Cigaba Da Karantawa