#EndSARS: Sai Mun Cire Bambance-Bambance Kafin Ƙasa Ta Zauna Lafiya – Bafarawa

Jigo a jam’iyyar PDP Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce idan har ‘yan Nijeriya ba zasu cire bambance-bambancen Addini ko jam’iyya ba, kasar ba zata taba zama lafiya ba. Bafarawa ya kara da cewa idan kasar bata zauna lafiya ba, babu yadda za’ayi a gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali, ko shugabancin kasar. Duk wani musifan da zata fado kasar babu ruwanta da bambance-bambancen Jam’iyya ko wani abu akasin haka, kan kowa musifan zata fada. Daga karshe ya yi kira ga al’ummar kasar da su kasance tsintsiya madaurin daya don ganin…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Kaduna Ta Fara Bi Gida-Gida Domin Dawo Da Kayan Tallafin Da Aka Sace

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara bi gida gida domin gano kayayyakin tallafin COVID-19 da aka sace a dakin ajiyar kayan da ke wasu garuruwa na jihar. Rundunar ‘yan sanda tare da sauran jami’an tsaro ne za su fara wannan atisayen binciken gida gida don gano kayan tare da cafke wadanda aka kama da laifin satar su. Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya tabbatar da wannan atisayen a shafinsa na Twitter a ranar Talata. Ya zuwa yanzu, rahotanni suna ta bayyana yadda bata gari ke ci gaba da fasa shaguna…

Cigaba Da Karantawa

Bincike: Ba Gaskiya Ba Ne Yunkurin Fasa Rumbun Abinci A Bauchi

A rahotannin da aka wallafa ranar Lahadin nan a wasu kafafen watsa labarai na jaridun Najeriya suna cewa matasa sunyi yunkurin fasa rumbun abinci na gwamnatin jihar Bauchi domin dibar ganima amma masu yun’kurin suna isa sai aka bama Shugaban ma’aikata na gidan gwamnati izinin, Dr. Ladan Salihu da ya bude masu rumbun abincin, sai suka tarar babu komai a ciki sai suka juya ba tare da sun dauki komai ba. Mazauna wurin sunce babu wadanda sukayi yunkurin fasa rumbun abinci na gwamnati, suka kara da cewa labarin ba gaskiya…

Cigaba Da Karantawa

An Cire Bambancin HND Da Digiri A Hukumomin Tsaron Najeriya

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta cire banbancin matsayi da karin girma da ke tsakanin masu takardar karatu ta babbar Diploma HND da kuma Digiri, a hukumar tsare ta Civil Defence, Hukumar Shige da Fice, Hukumar kula da gidajen yari da kuma hukumar Kashe Gobara da ke karkashin ma’aikatar. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar cikin gida mai dauke da kwanan watan ranar 16 ga watan Oktoba, wadda sakataren hukumomin Alhassan Yakmut ya sanya wa hannu kuma aka gabatar a karshen taron hukumar gudanarwar ma’aikatar. Sanarwar, ta ce daga…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Oktoba, shekarar 2020. Gwamnatin tarayya ta ce ba ta ce sai wani gwamna ya jira, ta ba shi izini kafin ya raba kayan tallafi na kwaronabairos ba. Ita kuma Zahra Buhari ta ce ta gode wa Allah da aka yi wallakiya aka gane ba mahaifinta ne matsalar kasar nan ba. Rijiya na bayarwa guga ke hanawa. Kodayake gwamnatin tarayya ta…

Cigaba Da Karantawa

A Yi Gaggawar Bincikar Waɗanda Suka Ɓoye Tallafin CORONA – NLC

Tun bayan samun rahotannin balle manyan shagunan da aka ajiye kayan tallafin korona tare da kwashesu a sassan Najeriya, Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi kira da babbar murya ga gwamnati akan ta zaƙulo jami’an da suka ɓoye wadannan kayayyakin domin fuskantar hukunci, sannan ta bukaci a gaggauta rabar da duk wani sauran kayan tallafin korona da suke jibge a manyan shagunan ajiya da ke fadin kasar nan. Kazalika, NLC ta yi Alla-wadai da barnatar da kayan tallafin korona da wasu batagari ke yi har yanzu a fadin Najeriya.…

Cigaba Da Karantawa

Ɓatanci Ga Annabi: Shehu Sani Ya Yi Tir Da Faransa

Tsohon ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya majalisar Dattawa Kwamared Shehu Sani, ya ce dole ayi tir da masu ta’addanci da rigar musulunci a kasar Faransa, sai dai wannan bai hana shi yin tir da aikin Shugaba Macron ba. Ɗan siyasar ya ce babu abin da zai hana a fito a yi tir da abin da shugaban kasar Faransar ya yi na ba masu yi wa addinin musulunci isgilanci goyon-baya. “Ya kai @EmmanuelMacron, dole ayi tir da duk wani harin ta’addanci ko zagon-kasa da aka yi a…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Imani Ne Ɓoye Kayayyakin Tallafin CORONA Da Gwamanoni Suka Yi – Galadima

Tsohon na hannun daman Shugaban ƙasa Buhari Malam Buba Galadima, ya ce, abin baƙin ciki ne da takaici kuma rashin imani ne ƙarara ɓoye kayayyakin tallafin CORONA da gwamnoni suka yi, kuma tabbas jami’an gwamnatin wata jiha da bai bayyana sunanta ba, sun taba tunkarar ofishinsa domin sayar da kayayyakin tallafin korona da suka karbo daga gwamnatin tarayya. Dattijon dan siyasar ya caccaki gwamnatocin jihohi a kan boye kayan abincin da ‘yan kasuwa da kungiyoyi (CACOVID) suka bayar a matsayin gudunmawarsu domin tallafawa talakawa lokacin annobar korona. Galadima ya bayyana…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: ‘Yan Ta’adda Na Barazanar Hanamu Fita Waje – Buratai

Shugaban Dakarun Rundunar Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce wasu ‘yan ta’adda na ta tsoratar da su da yunkurin hanasu fita kasashen ketare. Tun bayan bude wutar da sojoji suka yi a Lekki Toll gate a Birnin Ikko a yayin Zanga-Zangar Endsars Jami’an rundunar suka shiga tsaka mai wuya. A wani taro da shugaban rundunar sojin kasa, Tukur Buratai yayi a Abuja, ya zargi wasu kungiyoyi na kasashen ketare da tsoratar da Sojojin da fita kasashen waje saboda zargin shiga hakkin bil’adama. “Ya ce wasu miyagu na tsoratar…

Cigaba Da Karantawa

Bamu Ɓoye Kayayyakin Tallafin CORONA Ba – Gwamnoni

Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata labarin boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19. Kungiyar manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyoyin nairori don taimakon ‘yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992. A cikin kudaden da suka hada an yi amfani da wasu don gina cibiyoyin kula da lafiya da magunguna cikin jihohi 36 da…

Cigaba Da Karantawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sassauta Dokar Hana Fita

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana walwala a ƙananan hukumomi 21 dake Jihar, a yayin da sauran ƙananan hukumomi biyu Kaduna ta Kudu da Chikum zasu cigaba da zama cikin dokar kulle na awa 24 har abin da hali ya yi. Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Kwamishinan tsaro na Jihar Samuel Aruwan ya fitar aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna. Aruwan ya bayyana cewar sauran ƙananan hukumomin Jihar zasu cigaba da zirga-zirga daga misalin karfe huɗu na asubah zuwa…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, tara ga wtatan Rabi’ul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Oktoba na shekarar 2020. Gwamnatin Tarayya ta ce akwai wata naira biliyan ashirin da biyar da za ta bayar, ta matasa ce, don magance tashin hankali na matasan. Jama’a na ci gaba da wasoson kayan abinci duk inda suka samu labari an adana kayan abinci, kuma na baya-bayan nan ita ce Yola. Suka fasa sito uku da har ta kai…

Cigaba Da Karantawa

Ba A Taɓa Yin Adalin Shugaba A Najeriya Kamar Buhari Ba – Jiƙamshi

Shugaban hukumar Kula Da Zuba Hannun Jari ta Jihar Katsina Kuma Shugaban kwamitin wayar da Jama’a Kan Al’umma Jihar Katsina bisa ga shirye-shiryen tallafin da Gwamnatin Tarayya, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana cewa tunda aka dawo mulkin damakaradiyyaamakaradiyya a kasar nan ba’a taba samun gwamnatin da ta bullo da shirye- shiryen tallafi da ta zizarawa yan Nijeriya kudade daban daban kamar ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ba. Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana haka ne a dakin taro na hukumar EEC, da ke kan hanyar Kano a cikin garin Katsina,…

Cigaba Da Karantawa

Zamu Rage Farashin Data A Najeriya – Pantami

Mataimakin Shugaban zartarwa, na Hukumar Sadarwa ta Najeriya, Umar Danbatta, ya bayyana cewa Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki da karkashin jagorancin Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, na shirin rage farashin data daga N1,000 zuwa N390 a kowace gigabyte. Da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar, Mista Danbatta ya bayyana cewa wani bangare na shirin shi ne sabon tsarin watsa shirye-shiryen harkokin sadarwa na kasa baki daya na shekara ta 2020-2025, wanda ya ce dole ne Najeriya ta samar da hanyoyin kafafen sadarwa ta hanyar sadarwa, don…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: Lallai Gwamnati Ta Ɗau Mataki Akan Cutar Da Musulmi Da Aka Yi A Kudu – Gadon Ƙaya

Babban Malamin musulunci a Jihar Kano ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa game da zaluncin da masu zanga-zangar SARS suka yi wa musulmi ‘yan Arewa mazauna kudancin Nijeriya. “Muna kira da akai tallafin gaggawa ga musulmin Fatakwal don suna cikin tsanani, musulminmu na Imo da wanda suke Fulato, da na Aba, da sauran garuruwa, su ma suna bukatar taimako domin suna cikin bala’i, masu wannan zanga-zanga suna son juyar da ita zuwa fada da musulunci, to jami’an tsaro su sani mu ma Wallahi da karfinmu, ba za…

Cigaba Da Karantawa

#EndSARS: Lallai Gwamnati Ta Ɗau Mataki Akan Cutar Da Musulmi Da Aka Yi A Kudu – Gadon Ƙaya

Babban Malamin musulunci a Jihar Kano ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa game da zaluncin da masu zanga-zangar SARS suka yi wa musulmi ‘yan Arewa mazauna kudancin Nijeriya. “Muna kira da akai tallafin gaggawa ga musulmin Fatakwal don suna cikin tsanani, musulminmu na Imo da wanda suke Fulato, da na Aba, da sauran garuruwa, su ma suna bukatar taimako domin suna cikin bala’i, masu wannan zanga-zanga suna son juyar da ita zuwa fada da musulunci, to jami’an tsaro su sani mu ma Wallahi da karfinmu, ba za…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Matasa Sun Yashe Gidan Dogara

A ranar Lahadi, wasu bata-gari sun shiga tare da yashe gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar jihar Filato. Jaridar Punch ta gano cewa, ‘yan daban sun take dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka musu inda suke ta kusatwa gine-gine domin neman kayan tallafin korona. An kai harin gidan Dogara da karfe 9 na safe, wata majiya da ta kasance ganau ba jiyau ba ta sanar da Jaridar Punch. ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke tabbatar da an bi…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Matasa Sun Yashe Gidan Dogara

A ranar Lahadi, wasu bata-gari sun shiga tare da yashe gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar jihar Filato. Jaridar Punch ta gano cewa, ‘yan daban sun take dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka musu inda suke ta kusatwa gine-gine domin neman kayan tallafin korona. An kai harin gidan Dogara da karfe 9 na safe, wata majiya da ta kasance ganau ba jiyau ba ta sanar da Jaridar Punch. ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke tabbatar da an bi…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban Kasa Ya Umarci Ministoci Su Koma Jihohinsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministocinsa da su koma jihohinsu na haihuwa domin kwantar da tarzomar masu zanga zangar #EndSARS da kuma wanzar da zaman lafiya. Ana sa ran ministocin za su gana da masu ruwa da tsaki na jihohinsu domin zayyana masu kokarin gwamnatin tarayya na cika buri da bukatun matasan. Ministan albarkatun ruwa Sulaiman Adamu, ya tabbatar da hakan a ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, a Dutse, babban birnin jihar. Ya ce an umurci ministocin da su koma jihohinsu, domin taimakawa shuwagabannin…

Cigaba Da Karantawa

Da Guba Ciki: Wanda Ya Ci Abincin CORONA A Kaduna Ya Shirya Mutuwa – NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, ta Kasa reshen jihar Kaduna ta gargadi barayin da suka fasa dakin adana abincin agaji na Kaduna da kada su kuskura su ci wannan abinci domin akwai guba magunguna da aka saka a ciki sannan wasu ma sun gurbata. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin Gida, na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya saka wa hannu. Aruwan yace hukumar ta sanar wa gwamnatin jihar cewa an saka magunguna a ciki sannan wasu daga ciki sun lalace…

Cigaba Da Karantawa