Amurka: Malamar Makaranta Dake Lalata Da Dalibai Ta Shiga Hannu

IMG 20240518 073810

Wata kotu a birnin Manchester ta samu wata malamar makaranta da laifin yin lalata da wasu ?alibanta maza guda biyu.

An samu Rebecca Joynes, mai shekara 30, da laifukan lalata da ?ananan yaran har sau bibbiyu kowannesu.

An shaida wa al?alin cewa hukumar makarantar ta kori malamar, saboda yin lalata da yaro na farko, sai kuma ta sake yi da yaro na biyu a lokacin da ake tsaka da tuhumarta.

Malama Joynes ta samu juna-biyu sakamakon lalata da yaron na biyun duk da cewa yana da ?ananan shekaru.

Malamar ta fa?a wa yaron cewa ba ta tsammanin za ta ?auki ciki sakamakon lalatar.

An shaida wa kotun cewa malamar ta ja hankalin yaron ne mai shekara 15, ta hanyar saya masa wata belet (belt) mai ?an karen tsada da ta kai fam 345, kafin ta yi lalata da shi a gidanta.

?wararrun masu binciken kimiyya sun gano ?wararan hujjojin aikata lalata a kan gadon malamar.

A lokacin da lamarin ya faru hukumar makarantar da takadar da malamar, yayin da ‘yan sandasuka ?addamar da bincike.

Da farko an bayar da belinta sakamakon gaza samun hujjar ala?arta da yaron da bai kai shekara 18 ba.

To amma daga bisani sai ‘yan sanda suka gano cewa ta jima tana ala?a da wani ?alibin da suka ayyana a matsayin yaro.

A karon farko yaron ya ta?a zuwa gidanta a lokacin yana mai shekara 15, haka kuma bayan ya cika 16, ya sake komawa gidan suka sake aikata lalata da malamar, lamarin da ya sa ta samu juna-biyu.

Related posts

Leave a Comment