Maciya Amanar Ƙasa Zasu Gwammace Kiɗa Da Karatu – Bawa

Sabon Shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce a karkashin jagorancinsa, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa za ta himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa, ba tare da nuna sani ko sabo ba. Da yake jawabi a ranar Juma’a lokacin da ya hau kujerar a hukumance, Bawa ya yi alkawarin jan ragamar hukumar zuwa ga bin diddigi da binciken sirri. Ya ce zai kirkiro da cikakken iko na hukumar leken asiri da za ta jagoranci tattara bayanan sirri, wadanda…

Cigaba Da Karantawa

An Samu Sa Hannun Magu A Badakalar Maina

A cigaba da zaman Shari’a da ake yi na tsohon Shugaban Hukumar Fansho Abdulrasheed Maina dangane da tarin zargi da ake yi masa na yin sama da fadi da dukiyar jama’a, wasu shaidu sun bayyana cewar an samu hannun tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu cikin badaƙalar. Wani jami’in hukumar ta EFCC Ngozika Ihuoma, wanda ya bada shaida a kotu a ranar Alhamis, ya jefa tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, a badakalar ta Abdulrasheed Maina. Ana shari’a a kotu inda ake zargin tsohon shugaban kwamitin binciken kudin fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina…

Cigaba Da Karantawa

Maina Ya Rasa Beli A Karo Na Biyu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar belin da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa ya mika gabanta domin neman fita waje ganin likita. Ana shari’ar Maina ne inda ake zarginsa da wawure kudi da suka kai naira biliyan biyu kuma ya daina halartar zaman kotu a watan Satumba, lamarin da ya jefa sanata Ali Ndume gidan gyaran hali. An kama shi a jamhuriyar Nijar inda ya je neman mafaka kuma aka dawo da shi Najeriya a ranar 3 ga watan Disamban shekarar…

Cigaba Da Karantawa

EFCC: Magu Ya Taya Sabon Shugaba Murna

Sabon Shugaban Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa yace tsohon Shugaban Hukumar Ibrahim Magu ya kira shi ta waya da aka ba shi wannan mukami inda ya taya shi murna tare da yi mishi fatan alheri. Abdulrasheed Bawa ya ƙara da cewa akwai dangantaka ta mutunci da girmamawa tsakaninsa da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu, wadda ba zata misaltu ba. Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne yayin amsa tambayoyi a gaban Majalisar Dattawa lokacin tantance shi a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC mai yaƙi da cin…

Cigaba Da Karantawa

Atiku Ya Jinjinawa Buhari Kan Batun Sayar Da Matatun Mai

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi farin ciki tare da yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakin da za ta dauka na sayar da kadarorin kasar da suka hada har da matatun mai. Waziri Adamawa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya jima yana kiran a mayar da ragamar tafiyar da tattalin arziki ga ‘yan kasuwa. A cewarsa, duk da a tsawon shekara ra’ayinsa ya sha bambanta da na gwamnatin APC, amma a yanzu ya gamsu da yadda gwamnatin ta dawo kan turbar…

Cigaba Da Karantawa

Zan Rasa Kafata Muddin Ban Samu Beli Ba – Maina

Tsohon Shugaban Hukumar kula da kuɗaɗen Fansho ta ƙasa PRTT Abdulrasheed Maina yace zai iya rasa kafarsa indai ba a bashi damar zuwa asibiti neman magani ba, domin halin da ƙafar tashi ke ciki. Maina yana hannun hukuma akan zargin wawurar naira biliyan biyu na kudin fansho kuma ya tsere ya bar sanata mai wakiiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, a hannun hukuma bayan ya tsaya masa a matsayin mai bashi kariya. An samu nasarar damkarsa a jamhuriyar Nijar inda ya lallaba ya shige, a ranar 3 ga watan Disamban…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Bai Yi Mini Adalci Ba – Magu

Lauyan tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta’annati, EFCC Ibrahim Magu, Barista Tosin Ojaomo a ranar Talata ya koka kan cewa ba a yi adalci ba a game da mataki da sakayar da aka yi wa Ibrahim Magu. Lauya Ojaomo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Politics Today’ na gidan Talabijin na Channels. An kaddamar da kwamitin Ayo-Salami ne domin yin bincike game da dakataccen shugaban rikon kwaryan na hukumar yaki da rashawar a shekarar data gabata. “kwatsam,…

Cigaba Da Karantawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari Ya Naɗa Matashi Shugaban EFCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC. Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a yau Talata. A cikin wasikar zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Shugaban ya ce yana yin aiki ne bisa ga sakin layi na 2 (3) na Part1, CAP E1…

Cigaba Da Karantawa

An Naɗa Ngozi Iweala Shugabar Hukumar Cinikayya Ta Duniya

An nada Mrs Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugaba Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO). Sanarwar nadin Okonjo-Iweala ya fito ne daga bakin hukumar da ke Geneva a ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu. Okonjo Iweala ce mace ta farko kuma bakar fata da ta fara shugabancin hukumar. Wa’adinta zai fara ne daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2021. Wakilai daga kasashe 164 da ke kungiyar ne suka jefa kuri’a kafin nadin na Okonjo-Iweala kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar. An nada Okonjo-Iweala ne bayan sabon shugaban kasar…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Amince Da Kafa Gagarumin Kamfani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da samar da wani kamfanin hadin guiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu mai suna Infra-Co, tare da fara wa da jarin Naira Tiriliyan daya. Ana sa ran karfin jarin kamfanin zai bunkasa zuwa Naira Tiriliyan 15.Kamfanin wanda shi ne irinsa na farko a Nahiyar Afirka, zai maida hankala ne wajen ci gaban ayyukan more rayuwa a kasar. Kamfanin wanda shugaban Buhari ya bukaci mataimakinsa ya jagoranci kafa shi, Babban Bankin Nijeriya tare da Majalisar Bunkasa Tattalin Arzikin kasar suka kirkiro shi. Kamfanin…

Cigaba Da Karantawa

Dattawan Arewa Sun Soki Gwamnan Babban Banki Da Nuna Wariya

Kungiyar tuntuba ta magabatan Arewa Arewa Consultative Forum (ACF) ta rubuta wasika zuwa ga gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, inda take zargin shi da nuna wariya ga yankin. Kungiyar Dattawan Arewan ta koka wa gwamnan CBN a kan yadda ake ware jihohin Arewa wajen yin rabon tsare-tsaren tattalin arziki a Najeriya, sannan ake fifita Jihohin Kudu duk da yawan jama’a da yankin Arewan ke dashi. Shugaban Kungiyar Dattawan na kasa, Mista Audu Ogbeh ne ya sa hannu a wannan doguwar wasika da kungiyar ta aika wa Gwamnan babban…

Cigaba Da Karantawa

Al-Mundahana: Za A Gurfanar Da Tsohuwar Ministar Jiragen Sama

Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama gaban kuliya bisa zargin wawurar kudaden al’umma gami da rub da ciki ba bisa ƙa’ida ba. An ɗage zaman da za a yi da ita a kotu ranar Talata saboda tsohuwar ministan bata nan, ko Lauyanta. Yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa, kuma ana zargin ta da wasu mutane 8 a wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CR/316/20. Hukumar tana zargin Oduah da kwasar kudin gwamnati lokacin tana minista. A…

Cigaba Da Karantawa

Za A Shiga Fitinar Tsadar Fetur A Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shirin jure wahalar karin farashin mai yayin da farashin danyen mai ya haura sama da $60 a kowace ganga. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Inganta Kudin Najeriyar a ranar Talata, Sylva ya ce ba tare da samar da tallafi a cikin kasafin kudin 2021 ba, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ba zai iya ci gaba da daukar nauyin da ke kasa-kasa ba. A halin yanzu, farashin man fetur ya kai…

Cigaba Da Karantawa

Za A Maye Gurbin Lambobin BVN Da NIN – Pantami

Ministan Sadarwa da sabon tsarin gina tattalin arziki Dakta Isa Ali Pantami, ya ce gwamnatin tarayya tana kan hanyar maye gurbin matsayin BVN da NIN. BVN lambobi ne na tantancewa da bankuna suke ba abokanan harkar su. Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sanusi Lamido, ne ya bullo da tsarin BVN domin tsaftace harkokin bankuna da kuma magance badakala da cin hanci. Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa, NIMC, ce ke bayar da lambobin tantancewa na NIN ga kowanne dan kasa da ya yi rijista da gwamnati. Da…

Cigaba Da Karantawa

Al-Mundahana: Babu Gaskiya A Zargin Da Ake Yi Mini – Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez Abubakar Yari, ya karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka yada cewar kotu ta umarci a kwace kudin hannun sa dala milliyan 621. Mai magana da yawun tsohon gwamnan Abdulrahaman Yahaya, ya bayyana haka a yayin da yake Alla-wadai akan labarin a cikin wata takarda daya rabawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja. ” Abdulrahaman, ya ce gaskiyar labarin shi ne kotu ta umarci a rufe asusun ajiya na tsohon gwamnan a bankunan Polaris da Zenith mai dauke da kudi naira milliyan 278.…

Cigaba Da Karantawa

An Fara Gwanjon Gwala-Gwalan Tsohuwar Ministar Mai

Kwamitin da aka kafa domin sayar da kayayyakin da gwamnatin tarayya ta kwace daga masu laifi ta fara sayar da wasu kadarori 25 a sassan kasar daban-daban. Mista Daya Apata, Shugaban kwamitin ya sanar da hakan a jiya yayin taron manema labarai a birnin Tarayya Abuja. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar bara ya kafa kwamitin bayan ganin akwai bukatar hakan sannan ya umurci ofishin Ministan Shari’a na kasa ya saka ido kan ayyukan kwamitin na karbo kadarorin gwamnati da sayar da su. Mista…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar A Faɗa Masifar Ƙarancin Mai – Gwamnatin Tarayya

Gwannatin Tarayyar Nijeriya ƙarkashin jagorancin mai girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta nuna damuwarta kan yiyuwar samun karancin man fetur a ƙasar. Karamin Ministan man Fetur Timipre Sylva ya bayyana haka a lokacin wani taro tsakanina Gwannatin da kungiyoyin kwadago a daren Litinin. Taron dai ci gaba ne a tattunawar da bangarorin ke yi a kokarin da ake na shawo kan kungiyoyin kwadagon kar su tafi yajin aiki biyo bayan karin farashin man da wutar lantarki. A lokacin zaman taron kwamitin aiki kan karin farashin man ya gabatar da rahotonsa…

Cigaba Da Karantawa

Ana Cuwa-Cuwa Wajen Tallafin Dubu 20-20 A Kaduna

Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ana tsananin yin cuwa-cuwa da sama da fadi akan kuɗin tallafin wanda aka ware domin talakawa, amma sai wasu manyan Mata a jihar ke cigaba da amfana. An ruwaito cewa mutanen da ba a san su ba suna karbar kudade daga wasu daga cikin wadanda suka amfana. Sun yi zargin…

Cigaba Da Karantawa

EFCC Ta Damƙe Matasa ‘Yan Damfara Ta Yanar Gizo

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce jami’anta sun yi nasarar cafke wasu matasa su 10 da ake zarginsu da damfara mai nasaba da kwamfuta da ake kira ‘Yahoo-Yahoo’. Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ta EFCC, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a makarantarsu ta ‘Academy’ da ke yankin Bwari na birnin Abuja inda aka ce su “su na koyon sana’ar yaudarar mutane ne”. Wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 30, su ne Sixtus Jude,…

Cigaba Da Karantawa

Za A Binciki Dalilin Rashin Ƙarkon Data

Hukumar kula da sadarwan Najeriya NCC ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan kararrakin da ake shigarwa kan saurin karewan Data da kwashewa mutane kudi a waya. Shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Danbatta, a ranar Alhamis ya bayyana haka a wani taron bashi lambar girma da mujallar MoneyReport ta bashi a matsayin jarumin 2020 a Abuja. Danbatta ya ce hukumar na iyakan kokarinta wajen ganin cewa kamfanonin sadarwa ba sa cutan jama’a. Ya ce ta wannan bincike da hukumar ke gudanarwa, “za’a gani takamammen dalilin da yasa Data ke…

Cigaba Da Karantawa