Wasanni: El Rufa’i Ya Shiga Gasar Gudun Fanfalaki

Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ya yi rajista domin shiga gasar tseren fanfalaki na kasa da kasa a jihar amma ba zai yi fiye da kilo mita biyar ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a ranar Asabar a Kaduna inda ya ce gasar da za ayi a ranar 21 ga watan Nuwamba zai ci kimanin Naira miliyan 300 kuma ana sa ran manyan ‘yan tseren duniya 10 za su shiga gasar. A cewarsa, an shirya gasar ne domin gano matasa masu…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Liverpool Ta Sayi Gogaggen Ɗan Wasan Tsakiya

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila ta sayi Gogaggen dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayern Munich a kan $26m. Thiago, dan asalin kasar ‘Andolus’ wacce aka fi sani da ‘Spain’ a yanzu, ya saka hannu a kan kwantiragi na zama na lokaci mai tsayi a kungiyar Liverpool. Dan wasan mai shekaru 29 a duniya ya shafe tsawon shekaru 7 tare da kungiyar Bayern Munich. Yayin zamansa a Bayern Munich, Thiago ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin gasar Bundesliga, kofin Jamus da kuma kofin gasar zakarun…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Ali Nuhu Ya Zama Jakadan La Liga

Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Hausa, furodusa kuma mai bada umarni, Ali Nuhu, ya bayyana a matsayin jakadan La Liga na arewacin Najeriya. An bayyana jarumin a wannan matsayin a yayin taron farko na masoya La Liga na arewa wanda gidan rediyon Arewa da La Liga suka dauka nauyi a Kano. Ali Nuhu ya tabbatar wa da masoyan La Liga na yankin arewacin Najeriya da cewa zai samar da alaka mai karfi kuma mai cike da zaman lafiya a yayin da ya zama jakadan La Liga a arewa. Hakazalika, shugaban fannin…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Messi Ya Amince Da Cigaba Da Wasa A Barcelona

Shahararren ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona Leonel Messi ya bayyana cewa ya hakura zai cigaba da murza tamola a ƙungiyar har sai kakar wasa mai zuwa. Messi ya bayyana haka ne a hira da yayi da jaridar Goal.com ranar Juma’a. Messi ya ce iyalan sa na daga cikin waɗanda suka sa ya canja shawara. ” Ko da na gaya wa matata da ƴaƴana cewa zan bar Barcelona sai suka barke da kuka kamar an yi mutuwa, matata tace na yi hakuri, sannan ƴaƴana suka ce sun saba da…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Messi Ya Ƙauracewa Atisaye Da Bercerlona

Lionel Messi ya kauracewa atasayen farko da Barcelona ta gudanar a jiya Litinin, domin sharar fagen shiga sabuwar kakar wasa. Wannan na nufin mai yiwuwa kaftin din ya tilasta rabuwa da kungiyar Barcelona, ta hanyar kin bugawa kungiyar tasa wasa a sabuwar kakar wasan dake tafe, da za a soma ranar 12 ga watan Satumba. Sai dai Messi da lauyoyinsa na ganin Shiga atasayen zai haifar da rudani kan ikirarinsu na cewar tuni Messi ya Raba Gari da kungiyar ta Barcelona. Lauyoyin Messi sun kara da cewar Dan wasan na…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Messi Ya Ƙauracewa Atisaye Da Bercerlona

Lionel Messi ya kauracewa atasayen farko da Barcelona ta gudanar a jiya Litinin, domin sharar fagen shiga sabuwar kakar wasa. Wannan na nufin mai yiwuwa kaftin din ya tilasta rabuwa da kungiyar Barcelona, ta hanyar kin bugawa kungiyar tasa wasa a sabuwar kakar wasan dake tafe, da za a soma ranar 12 ga watan Satumba. Sai dai Messi da lauyoyinsa na ganin Shiga atasayen zai haifar da rudani kan ikirarinsu na cewar tuni Messi ya Raba Gari da kungiyar ta Barcelona. Lauyoyin Messi sun kara da cewar Dan wasan na…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Arsenal Ta Doke Liverpool A Bugun Daga Kai Sai Mai Tsaron Gida

Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Liverpool kwallo 5 zuwa 4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan yin kunnen doki na tsawon mintuna 90 a wasan da aka buga a filin kwallo Wembely. Tsohon zakaran ‘yan kwallon nahiyar Afrika, Pierre-Emerick Aubameyang, ya fara zura kwallo ragar Liverpool a minti na 12. Sai da aka kusa tashi wasa Takumi Minamino na kungiyar Liverpool ya mayar da martani da kwallo a minti na 73. A haka aka cigaba da karawa babu wanda ya kara zura kwallo cikin kungiyoyin…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Ɗan Wasan Arsenal Ya Yi Tir Da Kisan Musulman Chana

Mesut Ozil ya wallafa a shafin sa na Istagram irin halin ƙunci da cin zarafi da ake yi wa musulmi a yankin Uighur na kasar Chana, da nuna takaici da damuwa dangane da watsi da sha’anin su da sauran ƙasashen musulmi suka yi. “Haƙiƙa an keta hakkin musulmi a Chana, ab kokkone musu Kur’anai da rusa musu Masallatai da kisan malaman su da yi wa matan su da ‘ya’yan su fyade, da tursasa matan su su auri ‘yan Chana da ba musulmi ba, amma babban abin damuwa ba wata ƙasa…

Cigaba Da Karantawa