Akwai Kiristoci Masu Yawa A Ƙungiyar Boko Haram – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina ganin fitinar da ke faruwa a jihohin arewa maso gabashin jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin matsalar arewa; kalubale ne da ya shafi kowa da kowa. Zulum ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani na shekara ta 17 na Gani Fawehinmi wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, reshen Ikeja ta shirya ranar Juma’a. A cewarsa, mambobin kungiyar ta Boko Haram sun hada da fararen fata, ‘yan Asiya, ‘yan Afirka, Musulmai da Kirista.…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda 18

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun bayyana cewar gungun wasu ‘yan Bindiga ɗauke da makamai sun sace ayarin wasu ‘yan sanda har su 18 akan hanyar Birnin Gwari hanya mafi hatsari a fadin Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana cewa an nemi ‘yan sandan an rasa bayan harin da aka kai musu a hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari, an ruwaito cewa ‘yan sandan na hanyarsu ta zuwa Kano daga Minna, jihar Neja ranar Juma’a. Amma majiyoyi sun bayyana cewa Sojoji sun ceto kimanin ‘yan sanda 10 a Maganda ranar Asabar. Shugaban kungiyar…

Cigaba Da Karantawa

Jahilci Ne Silar Matsalolin Da Najeriya Ke Ciki – Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bayyana ce duk matsalolin da mu ke ci a halin yanzu a kasar nan, babban abinda ya haddasa shi rashin ilimi ne, watau bakin Jahilci da farin jahilci, wanda ya ke kawo matsalar ‘yan bindiga da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi da yin biris din hukumomi ga matasa shi ne musababbin matsalolin da kasar nan ta samu kanta. Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka a karamar hukumar Kaita, a lokacin da ya ke hannanta gidan marayun da makarantar islamiyya da Sanata Abubukar…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa

Wasu ‘yan bindiga sun sace tsohoon ‘dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdulmumuni Ningi. Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sace tsohon dan majalisar, wanda ya taba wakiltar mazabar Ningi a majalisar jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar ta Bauchi, Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka, inda yace an yi garkuwa da tsohon dan majalisar a cikin garin Bauchi. Sha’anin satar mutane da yin garkuwa da su wani abu ne wanda ya zama ruwan dare yanzu a Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar, inda ‘yan Bindiga da barayin…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Sanda Sun Cafke Matasan Aljannu Biyu A Katsina

Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar damke wadansu shahararrun ‘yan damfarar da ke make murya a matsayin fararen aljannu, inda suke kiran mutane da cewa su aljannu ne, inda suke tambayar sirrin katin fitar da kudi wato (ATM). Akwai Kabiru Bashir, dan shekara ashirin da bakwai da kuma Sadiq Ashiru, dan shekara talatin da haihuwa, dukkan su yan asalin karamar hukumar Danbatta a jihar Kano. Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya baje kolin su gaban manema labarai a yau Laraba, a helkwatar rundunar…

Cigaba Da Karantawa

Ƙungiyar Boko Haram Ta Kiristoci Ta Bayyana

An damke wasu fastoci biyu, Olumide Peter da Jasulayomi Adetola, kan laifin sauya tunanin mabiyansu domin watsi da iyayensu tare da kona takardun karatunsu saboda Boko Haramun ne. An gurfanar da su ne a kotun majistaren Ilori ranar Alhamis inda aka cajesu da laifin yaudara, tsorata mutane, boye mutane da kuma damfara. Alkalin kotun, Ibrahim Dasuki, ya bada umurin garkame Fastocin biyu a gidan kason Oke-Kura dake Ilori, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.Bayan haka, ya dage karar zuwa ranan 28 ga Junairu, 2020. Lauyan hukumar NSCDC, Ajide Kehinde, ya…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Kasuwar Kantin Kwari 27 A Hanyar Abia

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace wasu matasa ƴan Kasuwar Kantin Kwari ta Kano a kan hanyarsu ta zuwa birnin Aba na jihar Abia da ke kudancin Najeriya. Ƴan bindigar sun tare matasan waɗanda dukkansu ƴan jihar Kano ne, a kan hanyarsu ta zuwa Aba a cikin daren ranar Lahadi. A cewar ƙungiyar matasan arewacin Najeriya a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, matasan sun tafi garin na Aba a ranar Lahadin da ta gabata don yin sayayya, da niyyar koma wa Kano a makon da muke…

Cigaba Da Karantawa

Ana Cigaba Da Tsare Matashin Da Ya Yi Barazanar Harbe Buhari

Solomon Akuma mahaifin wani matashi da ke aiki da hukumar NAFDAC, Emmanuel Akuma, ya bada labarin yadda ɗan sa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan wani rubutu da ya yi a shafin sada zumunta na barazanar sa wa a kashe Buhari. Solomon Akuma wanda Fasto ne a Cocin Truevine Evangelical Mission da ke Delta, ya ce dakarun FCID sun cafke masa yaro, kuma har kawo ya zuwa wannan lokaci bai san halin da ɗan nashi yake ciki ba. Solomon Akuma ya shaidawa manema labarai cewa tun watan Afrilun 2020, ‘yan…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: An Yi Awon Gaba Da Almajiran Ɗahiru Bauchi Cikin Dare

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami’an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan. Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin. “Da misalin 12:00 na dare Sojoji da Ƴan sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren,” in ji shugaban makarantar. Ya bayyana…

Cigaba Da Karantawa

Muna Dab Da Kawo Ƙarshen ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina

A kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro da wasu kananan hukumomin jihar Katsina, ke fama da ita, Kwararren masanin tsaro Kuma mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya ce wannan sabuwar hanya da muka bullo da ita za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar ke ciki. Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da RARIYA a ci gaba da shirye-shirye wani taron karawa juna sani da ofishin sa zai shiryawa manema labarai a ranar…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Tura Sabbin Kuratan Sojin Da Aka Ɗauka Dajin Sambisa – Buratai

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa Hukumar Sojojin Najeriya za ta yi tankade da rairaye da zazzage a daukar kuratan sojoji, ta yadda sai wadanda su ka cancanta kadai za a dauka aiki. Ya ce babu wani gurbi ko guda daya da za a dauki wanda bai cancanta ba a jefa cikin aikin soja. Laftanar Janar Buratai dai ya yi wannan ban-tsoron a lokacin da ya ke jawabi wajen tantanace kuratan sojoji a Dajin Falgore, cikin Jihar Kano a ranar Litinin. Ya ce wannan aikin tantance sabbin…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare

A cigaba da kai hare haren ta’addanci da ‘yan Bindiga ke yi a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, a yammacin jiya wasu ‘yan Bindiga da ake kyautata zaton Fulani ɗauke da muggan makamai sun kaddamar da hari a yankin ƙaramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna. Harin ya yi sanadin rasa rayukan wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido dake yankin ƙaramar Hukumar, da jikkata wasu adadi masu yawa gami da salwanta na tarin dukiyoyin jama’a. Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari…

Cigaba Da Karantawa

Jama’atu Na Tunzura Musulmi Su Gama Da Ni – Kukah

Babban Faston cocin darkar Katolika dake jihar Sokoto, Mathew Kukah ya zargi wasu kungiyoyin addinin musulunci da ingiza mabiyansu su afkamasa sannan su ta da zaune tsaye. Kuka ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar ranar Litinin inda ya ke sukan sakataren kungiyar Jama’atu da Dakta Khalid da yin Kalaman Batanci a garsa da kuma yi masa kazafi a bayanan da yayi ranar kirsimeti. Dakta Khalid ya soki kalaman Kuka wanda yayi ranar Kirsimet inda ya ke sukar gwamnatin Buhari da nuna fifiko ga yankin Arewa sannan kuma…

Cigaba Da Karantawa

Rage Yawan Hakimai Da Dagatai A Jihar Kaduna Ya Ƙara Matsalar Tsaro – Abdul-Ra’uf

An bayyana cewar matakin da gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru Ahmad El Rufa’i ta dauka na rage adadin yawan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya a jihar ya taimaka wajen ƙara matsalar tsaro a jihar musamman a yankin ƙaramar Hukumar Birnin Gwari. Ɗan Masanin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Idris Abdul-Ra’uf ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shirin Tambihi a karshen mako. Basaraken ya ƙara da cewar a baya can lokacin da…

Cigaba Da Karantawa

Rage Yawan Hakimai Da Dagatai A Jihar Kaduna Ya Ƙara Matsalar Tsaro – Abdul-Ra’uf

An bayyana cewar matakin da gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru Ahmad El Rufa’i ta dauka na rage adadin yawan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya a jihar ya taimaka wajen ƙara matsalar tsaro a jihar musamman a yankin ƙaramar Hukumar Birnin Gwari. Ɗan Masanin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Idris Abdul-Ra’uf ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shirin Tambihi a karshen mako. Basaraken ya ƙara da cewar a baya can lokacin da…

Cigaba Da Karantawa

Rage Yawan Hakimai Da Dagatai A Jihar Kaduna Ya Ƙara Matsalar Tsaro – Abdul-Ra’uf

An bayyana cewar matakin da gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru Ahmad El Rufa’i ta dauka na rage adadin yawan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya a jihar ya taimaka wajen ƙara matsalar tsaro a jihar musamman a yankin ƙaramar Hukumar Birnin Gwari. Ɗan Masanin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Idris Abdul-Ra’uf ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shirin Tambihi a karshen mako. Basaraken ya ƙara da cewar a baya can lokacin da…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Allah Fallasa Masu Hannu A Ta’addanci – Sakataren Gwamnati

Shugaban kwamitin tsaro na jihar Katsina, kuma sakataren gwamnati jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya roki al’umma da su dukufa yin addu’o’in samun dawammamen zaman lafiya, da kuma addu’ar Allah ya toni asirin duk wanda ke da hannu a cikin sace-sacen mutane da kashe-kashen yan bindigar ke yi a jihar Katsina dama Nijeriya baki daya. Malam Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabin bankwana ga wasu mutane talatin da bakwai da gwamnatin jihar Katsina ta kubutar a hannun yan bindiga, a sasanin ‘yan yi…

Cigaba Da Karantawa

Kano: An Damƙe Matashin Da Ya Yi Yunƙurin Kisa Da Ƙaho

Rundunar’ yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai suna Dini Abdullahi da yunkurin kisa inda ya cakawa Ahmad D. Ahmad kaho a idonsa da kuma kirjinsa a unguwar Diso cikin birinin Kano, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a ranar Talata, inda ya ce wanda ake zargin ya soke shi ne bayan da rigima ta kaure a tsakaninsu kan bashin 850, Dini ya ce yana bin Ahmad bashin kudi N850 ne, inda shi kuma ya…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Kullum Sai ‘Yan Bindiga Sun Mini Wanka Da Ruwan Sanyi – Mai Unguwar Malamai

A cigaba da tattaunawar da wakilinmu ke yi da wasu daga cikin mutanen da ‘yan bindigar suka sace kuma gwamnatin jihar Katsina ta kubutar da su. Malam Abubakarub, shi ne Maigarin Unguwar Malamai, da ke gundumar Yantumaki, a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo ne garin ne da bindigogi, inda suka dauke ni da mata da kananan yara goma sha shidda har da na goye. Maigarin Unguwar Malamai ya bayyana haka ne, jim kadan bayan ziyarar bankwana da sakataren gwamnati jihar Katsina, ya…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Ceto Amarya Da Angon Da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da ceto karin mutane 37 da aka yi garkuwa da su, ciki kuwa ha da amarya da angon da aka yi garkuwa da su makwonni biyu da suka gabata. Mutanen da mafi yawansu mata ne da kananan yara, sun ce sun kwashe kwanaki 15 a hannun ‘yan bindiga. Ango da amaryar wadanda ‘yan asalin kauyen Bakon Zabo ne na karamar hukumar Batsari jihar Katsina, sun ce sun sha bakar azaba a hannun wadannan ‘yan ta’adda. Da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce a wurin…

Cigaba Da Karantawa