Shirin Kawancen Atiku Da Peter Obi Ba Barazana Bane – Fadar Shugaban Kasa

IMG 20240520 WA0040

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa fadar shugaban kasa ta yi watsi da shirin kulla kawance tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

A cewar fadar shugaban kasa, shugaban kasa Bola Tinubu bai damu da wannan kawancen da ake shirin yi ba, ganin cewa shugaban kasa ba ya barci.

A makon da ya gabatane dai ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya ziyarci wasu jiga jigan jam’iyyar adawa ta PDP domin daura ɗamarar fuskantar zaɓen 2027.

Daga bisani an ruwaito babban ɗan takarar jam’iyyar adawa Alhaji Atiku Abubakar na faɗin a shirye yake ya mara wa Peter Obi baya muddin jam’iyyar PDP ta sahale mishi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply