Kananan ‘Yan Kasuwa 100,000 Sun Karbi Tallafin N50,000 Daga Gwamnatin Tarayya – Minista

images 2024 03 14T070645.613

Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta bayyana cewa, ‘yan kasuwa Kimanin 100,000 a fadin tarayyar kasar nan ne suka Karbi Naira 50,000 ta hanyar tsarin bayar da tallafin sharadi na Shugaban kasa, Wanda kuma aka fi sani da Shirin Tallafin Kasuwanci. Ministar, wacce tayi magana ta bakin mai taimaka mata, Terfa Gyado, ta tabbatar da cewa an fara rabon kudaden ne makonnin da suka gabata, Kuma za a raba wa masu ƙananan sana’o’i kimanin 1,291 a kowace karamar hukuma. Gwamnatin Tarayya ta sanar da Shirin Ba da…

Cigaba Da Karantawa

Tsadar Rayuwa: Kayayyakin Masarufi Sun Yi Tashin Da Ba A Taba Gani Ba A Tarihi – Hukumar Kididdiga

IMG 20240226 WA0252

Wata sabuwar ƙididdigar da Ofishin Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa ta fitar, ya nuna cewa tsadar farashin kayan abinci da kayan masarufi ya cilla har zuwa ƙaruwa da kashi 37.92 a cikin watan Fabrairu. Amma malejin tsadar rayuwa a cikin watan Fabrairu ya ƙaru zuwa kashi 31.70, idan aka kwatanta da kashi 29.90 na tsadar rayuwa daga Janairu, kamar yadda NBS ta fitar a ranar Juma’a. Wannan ƙididdigar ta nuna cewa cikin watan Fabrairu 2024 tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 1.80, idan aka kwatanta da Janairu, 2024. NBS ta…

Cigaba Da Karantawa

Babban Banki Zai Fara Sayar Wa ‘Yan Kasuwa Canjin Dala

IMG 20240228 WA0023

A ranar Talata babban bankin ya sanar da hakan tare da cewa zai rika ba wa kowane dan canji mai rajista kudaden kasashen waje da kimarsu ta kai Dala N20,000 a kan kowace Dala, N1,301. “Ribar da za su dora ba zai haura kashi daya cikin 100 na farashin da suka samu kudaden kasashen wajen daga hannun CBN ba,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan Kasuwanci da Musayar Kudade na CBN, Hassan Mahmud. Hakan na zuwa ne kimanin shekaru biyu da CBN, a karkashin jagorancin tsohon shugabansa,…

Cigaba Da Karantawa

Daruruwan Matasa Za Su Samu Aiki A Matatar Mai Na – Dangote

Shugaban kamfanin Ɗangote Group, Aliko Ɗangote, ya ce sabuwar matatan man Fetur ɗin da ya gina zata samar da, “ɗumbin ayyukan yi,” ga matasan Najeriya. Ɗangote ya bayyana haka ne ranar Litinin a Legas, a wurin bikin kaddamar da matatar man mai suna, “Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals.” Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci buɗe matatar man fetur ɗin, wacce ake sa ran zata samar da isasshen mai ga Najeriya. Haka zalika ana tsammanin Matatar Ɗangote zata riƙa aikin samar da Man Fetur, Man Dizel, Man…

Cigaba Da Karantawa

Dukiyar Dangote Ta Sake Hawa Sama

Wani sabon rahoton Henley & Partners tare da hadin gwiwar New World Wealth ya ce, dukiyar attajirai a Afrika ta dara $2.4trn, tare da bayyana birane biyar na nahiyar da suka mallaki 50% na dukiyar Afrika. BusinessInsider ta ce, wadannan biranen sun hada da Johannesborg da Cape Town a Afrika ta Kudu da Alkahira ta Masar da Legas ta Najeriya da kuma Nairobi ta kasar Kenya. A cewar rahoton, a halin yanzu akwai masu hannu da shuni 138,000 da suke da jarin akalla dala miliyan 1 ko sama da haka,…

Cigaba Da Karantawa

An Kashe Malamai 10 Da Garkuwa Da 50 A Kaduna – Kungiyar Malamai

Kungiyar malaman sakandare a Najeriya reshen Jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe mambobinta malaman makaranta 10 sannan sun yi garkuwa da wasu malamai 50 a fadin kananan hukumomin jihar 23 daga watan Janairu zuwa yanzu. Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnan jihar Nasiru El-Rufai da yayi amfani da ikon da yake da shi domin ceto malaman da kuma sauran wadanda ‘yan bindiga ke ci gaba da tsare wa. Shugaban kungiyar na JIhar Kaduna, Ishaya Dauda ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labara da…

Cigaba Da Karantawa

Sana’ar Gyaran Takalmi Ta Yi Mini Komai – Bello Nasarawa

Muhammad Bello Adamu Nassarawa Dake Karamar Hukumar Chikun a Jihar KadunaMai Sana’ar gyaran Takalmi ne Wanda ya shafe Sama Shekaru 35 Yana wannan Sana’ar yace Sana’ar Gyaran Takalmi wato Shoe Shiner Sana’a ce Mai cike da Rufin Asiri, domin a cikinta yake ci Kuma yake Sha harma da Sauran bukatunsa na yau da Kullum. ya Kara da Cewa wannan sana’a tasa tayi Masa Riga da wando duk da Cewa wasu na Mata kallon sana’a ce ta Kaskanci amma agunsa ba haka abin yake ba. Inda yace da Wannan Sana’ar yayi…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Kasuwa Za Su Fara Cin Gajiyar Dubu 50-50 Duk Wata – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan ‘yan kasuwa a Nigeria. A wannan sabon shirin, a cewar shugaba Buhari, gwamnati za ta dinga tallafawa ‘yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata.Sai dai, gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo ‘yan kasuwan da za su ci moriyar wannan tallafi, kuma ‘yan kasuwar za su fito daga kowanne fanni na kasuwanci. Haka zalika, shugaban kasar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na farfado da tattalin…

Cigaba Da Karantawa

Kwangilar Gas: Najeriya Ta Yi Nasara Akan Kamfanin Birtaniya

Gwamnatin Najeriya ta samu nasarar karin wa’adin lokaci don daukaka kara gaban kotu a shari’ar da ta ke da katafaren kamfanin Birtaniya na P&ID kan kwangilar gas da kamfanin ke zargin kasar da saba ka’idoji. Nasarar da Najeriya ta samu a jiya juma’a gaban kotun Birtaniyar, na nuna cewa ta na da cikakkiyar damar kalubalantar hukuncin watan Agustan bara da ya yi umarnin kwace mata kadarorin da yakai darajar dala biliyan 9 da miliyan 600 da ke matsayin kashi 1 bisa 5 na yawan kudadenta da ke asusun ketare. Cikin…

Cigaba Da Karantawa