Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza DJs yin wasa a bukukuwan da mata a fadin jihar.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan a wani taro da wakilan DJs na jihar.
Ya ce matakin ya zama dole domin a hana caku?u wa tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwa.
Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga yanzu mata ne kawai za a bari su gudanar da taron su na mata.
Ya ce, “A matsayinmu na jihar shari’ar Musulunci, ba abin yarda ba ne a ce mu bari a rika cakuduwar maza da mata a wuri guda. Irin wannan na karfafa yada lalata.”
A nasa jawabin, wakilin DJs din, Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da DJ Farawa ya yabawa hukumar bisa gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta bullo da su domin gudanar da harkokinsu.
Ya ce, “Mun yi farin ciki da gayyatar hukumar Hisbah zuwa ga kungiyar mu ta DJ. Sun ba mu ?a’idoji a rubuce na yadda za mu kiyaye lokutan sallah da kuma wajibcin hana cakuduwar maza da mata a wajen taro.”
Ibrahim ya lura cewa duk DJs da ke gudanar da ayyukansu a jihar dole ne su bi sabbin ka’idojin da hukumar ta fitar don gujewa hukunci.