Kungiyar Hamas ta ce an kashe shugaban ta Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran. Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar yau da safe ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da yake domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Ƙungiyar falasɗinawan mai riƙe da iko a Gaza ta ce Isra’ila ce ta kashe shugaban nata, Ismail Haniyeh, yayin da yake halartar rantsar da sabon shugaban Iran. Ƙungiyar Hamas ta bayyana kisan a matsayin babban laifi wanda martanin sa ba zai…
Cigaba Da KarantawaCategory: Ketare
Ketare
Hajjin Bana: An Shiga Damuwa Kan Tsananin Zafi A Saudiyya
Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ƙasar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji. Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a. Hukumomin ƙasar kan yi tanadin na’urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta. Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara
Cigaba Da KarantawaNajeriya Ta Goyi Bayan Tsagaita Wuta A Gaza
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan Harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa Domin dakile munanan hare-haren da ake kai wa a rikicin I$ra’ila da Falasdinu. Ambasada Tuggar ya kuma tabbatar da goyon bayan Najeriya ga shawarwarin tsagaita wuta na shugaba Joe Biden. “Ya kamata shugabannin duniya da daukacin al’ummar duniya su amince da kudurin tsagaita bude wuta na Biden don kara kaimi wajen warware rikicin cikin gaggawa da kuma dakatar da mummunan tashin hankali a…
Cigaba Da KarantawaAmurka: Malamar Makaranta Dake Lalata Da Dalibai Ta Shiga Hannu
Wata kotu a birnin Manchester ta samu wata malamar makaranta da laifin yin lalata da wasu ɗalibanta maza guda biyu. An samu Rebecca Joynes, mai shekara 30, da laifukan lalata da ƙananan yaran har sau bibbiyu kowannesu. An shaida wa alƙalin cewa hukumar makarantar ta kori malamar, saboda yin lalata da yaro na farko, sai kuma ta sake yi da yaro na biyu a lokacin da ake tsaka da tuhumarta. Malama Joynes ta samu juna-biyu sakamakon lalata da yaron na biyun duk da cewa yana da ƙananan shekaru. Malamar ta…
Cigaba Da KarantawaKetare: Mahamat Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Chadi
Sakamakon zaɓen shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaɓen wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru. Zaɓen na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin riƙon ƙwarya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga wanda ya baiwa ɗansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda. Sakamakon zaɓen…
Cigaba Da KarantawaCinikin Makamai: An Shiga Sa Toka Sa Katsi Tsakanin Najeriya Da Amurka
Sa-toka-sa-katsi da sa-in-sa sun ɓarke tsakanin Najeriya da Amurka, a ƙoƙarin da Najeriya ke yi na ganin ta karɓo kuɗin ta har Dala miliyan 8.6, waɗanda gwamnatin Amurka ta ƙwace tun cikin 2015. Tun bayan ƙwace kuɗaɗen dai Amurka ta ƙi sakin kuɗin bisa dalilan cewa an nemi a sayi makaman ba bisa ƙa’idar da doka ta gindaya ba. Tun da farko dai Najeriya ta biya kuɗin ta hannun wani kamfanin dillacin makamai na Amurka, mai suna Dolarian Capital Inc (DCL), cikin 2014, domin sayo makamai a Amurka, bayan ‘yan…
Cigaba Da KarantawaYakin Da Isra’ila Ke Yi A Gaza Ta’addanci Ne Fafaroma
Fafaroma Francis ya ce yana buga wa cocin Katolika da ke Gaza waya kullum domin sanin halin da mutanen yankin ke ciki. A cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CBS, Fafaroma ya ce daruruwan Falasdinawa da ke gudun hijira na fama da rashin abinci. Fafaroma ya ce a lokacin da aka kashe Uwa da ƴarta a harabar cocin, rikicin ya tashi daga yaƙi ya koma ta’addanci. Manyan mutane da ƙungiyoyi da dama dai na sukar yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Cigaba Da KarantawaAmurka Ta Gargadi Isra’ila Kan Shirin Kai Wa Iran Hari
Gwanatin Amurka ta yi wannan gargadi ne a yayin da Isra’ila ke tunanin kai hari a matsayin martani kan harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata a karshen mako. Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa Amurka ba za ta sa hannu a hare-haren soji da Isra’ila ke tunanin kaiwa Iran ba, saboda fargabar barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya. Wani babban jami’in kasar ya shaida wa ’yan jarida jim kadan bayan kawo karshen harin na Iran cewa “Mun yi imanin Isra’ila na da ’yancin ta kare kanta. Amma da…
Cigaba Da KarantawaDuniya Ba Ta Da Karfin Daukar Yaki A Yanzu – Majalisar Dinkin Duniya
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, inda ya buƙaci dukkan ɓangarorin da su kai zuciya nesa. “Ina kira ga dukkan ɓangarori da su kai zuciya domin guje wa duk wani abu da zai janyo yin fito na fito ta ɓangaren soji a Gabas Ta Tsakiya,” kamar yadda ya rubuta cikin wata sanarwa. “Na sha nanata cewa yankin ko ma duniya ba za su iya jurewa shiga wani yaƙi ba.”
Cigaba Da KarantawaIran Ta Kaddamar Da Harin Ramuwar Gayya Kan Isra’ila
Iran ta ƙaddamar da hare-hare a Isra’ila ranar Asabar da tsakar dare, inda ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200. Iran ta kai waɗannan hare-haren ramuwar gayya ne bayan Isra’ila ta kai hari a ofishin jakadancinta da ke Syria, inda ta kashe zaratan sojinta bakwai ciki har da masu muƙamin janar. Jirage marasa matuƙa da makamai masu linzamin da Iran ta harba shi ne karon farko da take kai hari Isra’ila kai-tsaye daga cikin ƙasarta. Waɗannan hare-hare sun jawo fargaba game da yiwuwar ramuwa daga…
Cigaba Da KarantawaKetare: Rasha Ta Aike Da Na’urorin Tsaro Da Sojoji 100 Nijar
Kasar Rasha ta aike da wani na’urorin tsaron sama da kuma masu horas da sojoji 100 zuwa Jamhuriyar Nijar da ke yammacin Afirka. Jami’an soji daga ma’aikatar tsaron kasar Rasha za su girka tsarin tare da horas da sojojin Nijar yadda za su yi amfani da na’urorin, kamar yadda kafar yada labarai ta Jamhuriyar Nijar RTN ta ruwaito a yammacin ranar Alhamis. Kafin hakan dai an yi wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban gwamnatin mulkin soja Abdourahamane Tchiani da shugaban Rasha Vladimir Putin a karshen watan Maris. Gidan talabijin…
Cigaba Da KarantawaKetare: An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Senegal
An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban kasar Senegal na biyar a tarihin kasar, a wani ƙatsaitatcen biki da aka yi a wani ɗakin taro da ke wajen birni Dakar. Bassirou Diyomaye Faye, wanda kusan makonni biyu da suka gabata yana matsayin ɗan takarar adawa garƙame a gidan yari, bayan maye gurbin abokin tafiyarsa jigon adawar kasar Ousmane Sonko – shugaban jam’iyyar (Pastef) – tun a zagayen farko ya lashe zaɓen shugaban kasar na ranar 24 ga watan Maris, don haka a wannan Talata 2 ga watan Afrilu…
Cigaba Da KarantawaIsra’ila Ta Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da sabon zagayen tattaunawa game da tsagaita bude wuta a Gaza su gudana a biranen Doha da Alqahira, a cewar sanarwar da ofishinsa ya fitar a yau Juma’a, kwanaki bayan da ake ganin kamar tattaunawar ta cije. Tun bayan da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza a Litinin din data gabata, Isra”ila da kungiyar Hamas ke zargin juna da gazawa wajen cimma yarjejeniyar. A Talatar data gabata, mai shiga tsakani kasar Qatar tace ana…
Cigaba Da KarantawaKetare: An Yi Zanga-Zangar Neman Tumbuke Firaministan Isra’ila
An fuskanci wata takaddama a tsakanin masu zanga-zanga da jami’na ‘yansanda a Tel Aviv babban birnin Isra’ila a dai dai lokacin da ake ci gaba da fafata yaki a Gaza. ‘Yan sandan Isra’ila sun tsare wani mutum a yayin wata zanga-zangar neman sabon zabe, tare da nuna takaicin gazawar gwamnatin kasar wajen kubutar da daukacin mutanen da ke garkame a zirin Gaza. Hakanan a wani bangare kuma ‘Yan sandan sun kakkama wasu masu zanga-zanga a birnin Tel Aviv, wadanda suka yi kira da firaminista Benjamin Netanyahu ya yi murabus da…
Cigaba Da KarantawaAmurka Ta Yi Allah Wadai Da Sace ‘Yan Makaranta A Kaduna
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya a shafinta na X ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci sakamako mai raɗaɗi. “Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan sace ‘yan makaranta da aka yi a Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a Borno. “Zuciyarmu tana kan iyalan wadanda abin ya shafa. Muna tsayawa tare da ku wajen neman wadanda suka aikata laifin su fuskanci shari’a kuma a gaggauta dawo da duk wadanda aka kama. “Muna goyon bayan kokarin Najeriya na…
Cigaba Da KarantawaDuk Wanda Ya Nemi Cin Hanci Wajenku Ku Fallasa Shi – Tinubu Ga ‘Yan Kasuwar Qatar
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya roƙi manyan masu zuba jari na ƙasar Qatar cewa shi gwamnatin sa ba irin gwamnatin baya ba ce, wadda wasu jami’an gwamnati ke karɓar cin hanci kafin su haɗa masu son zuba jari Najeriya da shugaban ƙasa. Tinubu ya roƙe su cewa ƙofa a buɗe ta ke so shigo Najeriya su zuba jari, domin akwai damammaki sosai na jiran su. Ya ce duk wani jami’in gwamnati da ya nemi su ba shi cin hanci kafin ya haɗa su da shugaban ƙasa, to su faɗa masa…
Cigaba Da KarantawaIsra’ila Ta Hallaka Falasdinawa 100 Dake Kan Layin Amsar Tallafin Abinci
Rahoton dake shigo mana daga yankin Gabas ta Tsakiya na bayyana cewa Amurka ta kai tallafin abinci na farko ga al’ummar Gaza ta jiragen sama. Fiye da kulli 30,000 na abinci jiragen saman Amurka uku suka jefa wa al’ummar Gaza. An gudanar da aikin rabon abincin tare da hadin gwiwar sojojin saman Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka suka bayyana. Jami’an Amurka sun ce abincin da aka rabar shi ne na farko daga cikin da yawa da shugaba Biden ya bayyana ranar Juma’a. Shugaba Biden ya alkawarta kai agajin abinci…
Cigaba Da KarantawaKetare: An Kashe Madugun ‘Yan Adawar Kasar Chadi
Rahotannin dake shigo mana daga ƙasar Chadi na bayyana cewa wani mai shigar da kara na gwamnati ya ce an kashe wani madugun ‘yan adawa a ƙasar Chadi yayin wani artabu da jami’an tsaro. Mutuwar Yaya Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta zargi jam’iyyarsa ta adawa da kai wani mummunan hari da aka kai kan hukumar tsaron ƙasar, lamarin da Dillo ya musanta. A ranar Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedkwatar jam’iyyarsa da ke babban birnin kasar. Mai gabatar da ƙara Oumar Mahamat…
Cigaba Da KarantawaECOWAS Ta Ba Sojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Wa’adin Mako Guda
Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun bai wa sojojin da suka kwace mulki a Nijar wa’adin mako guda da su janye, yayin da kuma suka kakaba wa kasar takunkuman karayar tattalin arziki da kudade. Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS mai mambobi 15 sun bukaci a gaggauta sakin shugaba Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan kujerarsa bayan sojojin sun hambarar da gwamnatinsa tare da tsare shi tun ranar Larabar da ta gabata. Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a…
Cigaba Da KarantawaKetare: Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar
Kakakin sojojin ƙasar Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya sanar da juyin mulkin. Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, sannan kuma sun kulle duka iyakokin ƙasar baki ɗaya. Babu dai labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki ya zuwa yanzu. Amma sojojin sun bayar da sanarwar sun tuɓe shi daga mu:ƙaminsa. Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi. Sun kuma sanar da dokar hana fita daga ƙarfe 10 dare zuwa 6 na safe. Shugaban ƙasar Benin Patrice…
Cigaba Da Karantawa