Mun Yi Nasara Kan ‘Yan Bindiga Da Kashi Saba’in Cikin Dari – Gwamnan Katsina

Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage yawan ta’addancin ‘yan bindiga da kashi 70 cikin dari a cikin shekara daya da ta gabata.

Gwamnan ya ce an samu wannan nasara ne a sakamakon abin da ya kira kyakkyawan hadin kai tsakanin jami’an tsaro na sa-kai na jihar da kuma jami’an tsaro na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, da ya ruwaito labarai ya ce, gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Yola babban birnin jihar Adamawa, a yau Asabar a ziyarar aiki da ya kai.

Gwamnan ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a samu ‘yansandan jihohi da za a sanya su shiga yakin da ake yi da matsalar rashin tsaro a kasar.

Gwamna Radda, wanda ya ce sun bullo da dabarar yakar barayin, ya kara bayani da cewa abin da ake gani yanzu ‘yan bindigar na kai hari ne a kauyuka da yankunan da suke surkuki, inda suke kona gidaje da kashe jama’a

Related posts

Leave a Comment