Matsalar Jirgi Ta Hana Mataimakin Shugaban Kasa Zuwa Amurka

Kashim Shettima office portrait

Mataimakin Shugaban ?asa Kashim Shettima ya fasa zuwa taron tattalin arziki tsakanin Amurka da ?asashen Afirka da za a yi a birnin Dallas na Amurka kamar yadda aka tsara tun farko, a cewar fadar gwamnatin ?asar.

Yanzu Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar ne zai wakilci Shugaba Bola Tinubu, a cewar sanarwar da kakakin ofishin mataimakin shugaban ?asar ya fitar a yammacin yau.

Har yanzu Tinubu bai koma gida ba daga ziyarar da ya kai ?asashen Netherlands da Saudiyya, abin da ya jawo ‘yan adawa suka fara nuna damuwa game da wanda zai jagoranci ?asar idan Shettima ma ya yi tafiya.

Sai dai fadar shugaban ta ce matsalar jirgi ce ta hana mataimakin shugaban ?asar tafiya.

“Ya fasa tafiyar ne bayan tawagar kula da sufurin shugaban ?asa ta ba shi shawarar yin hakan,” in ji sanarwar da Stanley Nwokocha ya fitar. “Yanzu mataimakin shugaban ?asa zai ci gaba da hidimta wa ?asa.”

Related posts

Leave a Comment