Babbar Sallah: Za A Tsaurara Matakan Tsaro A Filayen Idi – Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Shugaban ‘yan sanda na ƙasa Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinonin ‘yan sandan ƙasar nan da su ɗauki matakan tsaurara tsaro a wurraren ibada da manyan hanyoyi yayin gudanar da bikin babbar sallah a gobe Talata.

Shugaban ‘Yan Sandan ya faɗi hakane a cikin wani jawabi da ya yi mai taken, ‘Bikin sallah: ya bada tabbacin tsaro da aminci’ wanda kakakin hukumar, Frank Mba, ya fitar ranar Lahadi.

A cikin jawabin, Shugaban ‘yan sandan ya taya ɗaukacin al’ummar musulmai murnar zagayowar babbar sallah ta shekarar 2021, da fatan za’a yi bikin cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma jaddada ƙoƙarin ‘yan sanda na cigaba da samun nasarori wajen kare rayuwar al’umma da dukiyoyinsu, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasa.

Hakanan ya bayyana cewa jami’an yan sanda zasu cigaba da namijin ƙoƙarin da suke yi wajen daƙile duk wani harin ta’addanci na yan ta’adda a Najeriya a kowane lokaci, ya roƙi yan Najeriya da su yi murnar sallah cikin farin ciki kuma su cigaba da bin dokokin tsaro da na kare yaɗuwar cutar COVID19.

Wani sashin jawabin yace: ” Ina tabbatarwa ‘yan ƙasa cewa hukumar zata ƙara a kan ƙoƙarin da take da yaƙi da ta’addanci da yan ta’adda, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Labarai Makamanta

One Thought to “Babbar Sallah: Za A Tsaurara Matakan Tsaro A Filayen Idi – Shugaban ‘Yan Sanda”

  1. […] July 19, 2021Ibrahim Ammani […]

Leave a Reply