Gawawwakin Da Muka Binne Sun Doshi 100 Rana Guda A Sokoto – Sarkin Musulmi

Rahotanni daga birnin Sokoto fadar Jihar Sokoto na bayyana cewar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Dr. Sa’ad Abubakar, ya ce ana ci gaba da kashe -kashen jama’a waɗanda ba a kai rohotonsu.

Sarkin ya fadi hakan ne a yayin taro na uku na 2021 na Majalisar Addini a Abuja ranar Alhamis.

Mai alfarman wanda ya ce yanayin tsaro a kasar ya koma baya, ya sha alwashin ci gaba da fadin gaskiya ga masu rake da mulki.

Ya ce, “A Sakkwato kadai, akwai ranar da muka binne mutane 76, masu laifi sun kashe su cikin ruwan sanyi, mutane ba sa jin labarin wannan, akwai ranar da muka binne mutane 48 a rana daya a Sakkwato, amma ba a jin labarin wancan.

“Duk mutanen da ke aikata wannan ta’asa dole ne a gano su, hukumomin tsaron mu dole ne su mai da hankali, gano su sannan su dauki mataki a kansu, ko ya kasance shugaban addini ko shugaban kabila.”

Da yake gargadi game da shiga tsakani daga kasashen waje, ya ce, “Dole ne mu kasance da gaske wajen dakatar da wannan kisan gilla amma idan muna son dakatar da shi, kun ba da damar kasashen waje su zo su yi aiki da ba mu san yadda zai kasance ba kuma zai iya kasancewa mara kyau gare mu. Ina yin wadannan sharhi da dukkan muhimmancin gaske domin abin ya dame mu sosai.

Labarai Makamanta

One Thought to “Gawawwakin Da Muka Binne Sun Doshi 100 Rana Guda A Sokoto – Sarkin Musulmi”

Leave a Reply