Duniyar Fina-Finai: Za A Ɗaure Masu Fim Ɗin Maɗigo – Hukumar Tace Fina-Finai

Wasu masu shirya finafinai biyu na fuskantar yiwuwar ɗauri idan suka yi burus da tsattsauran gargaɗin da hukumomi suka yi masu, suka ci gaba da shirye-shiryen fitar da wani fim da ke nuna wasu mata biyu suna soyayya kamar yadda jaridar BBC ta rawaito. Haska fim Don samun damar haska fim ɗin, masu shiryawar na shirin fitar da shi a shafukan intanet don yi wa masu sa idon ba-zata. Sai dai NFVCB na matuƙar sa ido kan duka hanyoyin shafukan intanet don hana fim ɗin fita. A cewar shugaban tace…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: El Rufa’i Ya Ba ‘Yan Hausa Fim Katafaren Fili

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ba masana’antar Kannywood katafaren fili da ya kai girman murabba’i 8,000 domin gina sinima ta zamani a Kaduna. An ba su filin ne a yankin Doka na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda ake kira da cikin garin Kaduna. Furodusa Abdul Amart Mai Kwashewa ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Alhamdulillah! “A cikin alkawarurrika da gwamnatin APC ta yi mana don inganta masana’antarmu ta Kannywood, muna mutukar godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i bisa cika nasa alkawarin na…

Cigaba Da Karantawa

Na Tuba Da Yin Fim: Maryam Yola

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Maryam AB Yola, ta fitar da sanarwa a shafinta na Instagram inda ta ce daga ranar 1 ga watan Satumban 2020, ta fice daga masana’antar Kannywood. Daga karshe ta mika godiyarta ga masoyanta, kawaye da abokan arziki a kan irin kaunar da ake gwada mata. Kamar yadda ta wallafa a shafin nata, “Assalamu alaikum. Ni Maryam AB Yola ina mai sanar da ku cewa daga yau daya ga watan Satumban 2020, na daina yin fim kuma na bar Kannywood. Kuma ina matukar godiya da kaunar da…

Cigaba Da Karantawa

Yadda Jaruma Fadila Muhammad Ta Rasu – Mahaifinta

Rasuwa fitacciyar jaruma Fadila Muhammad a daren jiya ta girgiza masana’antar finafinai ta Kannywood matuƙar gaske. Mujallar Fim ta gano cewar ta rasu ne a jiya Juma’a, 28 ga Agusta, 2020, da misalin ƙarfe 11:00 na dare a cikin motar mahaifin ta a lokacin da ya ɗauke ta zai kai ta asibiti. Da ma ta na fama da ciwon zuciya. Tun a shekaranjiya Alhamis ciwon ya tashi, aka kai ta asibiti ta ɗan samu sauƙi aka dawo da ita gida a ranar. A daren jiya kuma ciwon ya yi dawowar…

Cigaba Da Karantawa