Najeriya Ta Rasa Makama Tun Bayan Rantsar Da Tinubu – Babachir Lawal

IMG 20240519 WA0133

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir Lawal ya yi magani kan kamun ludayin gwamnatin Bola Tinubu. Babachir ya ce tun bayan hawan Tinubu karagar mulkin Najeriya ta ruguje ta rasa madafa.

Tsohon sakataren ya ce cire tallafin mai shi ne babban kuskuren da Tinubu ya yi tun kafin nadin mukamai a gwamnatin.

Na hannun daman tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Trust. Har ila yau, Babachir ya ce sanar da cire tallafin shi ne ya jefa jama’ar kasar cikin mummunan yanayi da har yanzu suke ciki.

Babachir ya koka kan farashin sufuri Lawal ya ce matakin ya shafi harkokin sufuri wanda shi ne ginshikin tattalin arziki da talaka da mai kudi ke tunkaho da shi.

“Zan sake maimaita abin da na dade da fada, kazo ka gwamnati a ranar da aka rantsar da kai ka dauki mummunan mataki.”
“A lokacin ba shi da Ministan tsare-tsare da zai tsara yadda za a samar da mafita idan aka cire tallafin mai.”

“Kuma ba kada Ministan kudi ko masu baka shawara kuma babu wadanda za su ce ya dace a yi ko kuma sabanin haka.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply