Lokaci Ya Yi Da Gwamnatin Jigawa Za Ta Dauki Nauyin Matsalar Ciwon Koda Rankatakaf

LOKACI YAYI DA GWAMNATIN JAHAR JIGAWA ZATA DAUKI NAUYIN MATSALAR CIWON KODA RANKATAKAF……………………….Ahmed Ilallah A wannan lokaci bisa duba da irn talauchi da wahalar rayuwar da mutane suke ciki, ya zama dole Gwamnatin Jahar Jigawa, karkashin jagorancin Malam Umar Namadi, ta dauki nauyin masu fama da ciwan Koda dari bisa dari. Kamar yadda a ka sani, jahar Jigawa musamman ma Jigawa ta Gabas sune kan gaba a wajen fama da matsalar ciwan Koda, ba ma a jahar nan ba, harma a kasa baki daya. Ciwan Koda ya sanaddiyar rayukan dubban…

Cigaba Da Karantawa

NEMAN AFUWA!!!

A madadin hukumar gudanarwa ta kamfanin ATAR Communications Nigerian Limited mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty. Muna neman afuwa dangane da sanya hoton wannan matashi da aka yi a wani labari da jaridar Muryar ‘Yanci mallakar Kamfanin ta yi amfani dashi a ranar 27 ga watan Yunin 2022 mai taken ” Kano: Kotu Ta Haramta Wa Matashi Hawa Doki Na Tsawon Shekaru Uku” Muna neman afuwar amfani da hoton wannan bawan Allah da muka yi ba shine Abdulsalam Bashir ba wanda Kotu ta hana hawa Doki ba. Sanarwa Daga…

Cigaba Da Karantawa

DAMULEWAR NIJERIYA: SHIN ‘YAN NIJERIYA ZASU IYA GYARA KASAR SU?
………………
Ahmed Ilallah

Abin takaici ne halin da nijeriya ta ke ciki na damulewa daga gazawar yaki da cin hanci da rashawa, lalacewar tsaro, rashin tsarin tattalin arziki da ciyar da Nijeriya gaba, uwa uba rushewar ilimin irin na jami’a, wanda shine ke bada tsarin da kowace kasa ta kan hau wajen cigaban ta. Ko ba komai, yau ta nuna wa kowa yadda ginin wannan kasa ke narkewa kadan-kadan, amma jagororin wannan kasar hankalin su yafi karkata wajen siyasar su, ta yadda kawai zasu dawwama a kan karagar mulki da tara dukiya ta…

Cigaba Da Karantawa

Addu’a Ce Mafita Ga Halin Da Najeriya Ke Ciki

Daga muhammad Sani Yusuf Nassarawa A daidai lokacin da ake kara shiga cikin dimuwa da rashin Tabbas na samun Tsaro a kasarnan Musamman a yankin Arewa wanda Matsalar Tsaron tafi shafarsu kama daga kona musu Muhalli tare da kayan abincin da suka tanada da kuma hana yankin Arewa Gudanar da sana arsu ta gado wato Noma da kiwo tunidai wannan ya zama Tarihi a yankin Shin Ko yaushe Talakan Kasarnan zai fahinci ana yin Dumukradiyya wacce ake cewa itace yancin Talakan? Maganar Gaskiya dai Itace Tuni talakawan Kasarna suka hakura…

Cigaba Da Karantawa

Nasiha Ga Matasa Game Da Shaye-Shaye

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa Don Allah Karka Saukemin caji, wannan Itace Kalmar da Wanda yasha kayan Maye ke fadi alokacin da yayi dif wato ya Dauke wuta. Wannan Kalmar da Makamantansu itace ke fitowa daga Bakunannsu yayin da Wani ke Musu Magana ko Kuma ya Nemi su Aikata wani abu na Daban Wanda Dole Sai Sun Tashi Daga Inda Suke Kafin su iya Aiwatar da Wannan abin, Misali kamar Fita Daga Daki Zuwa Waje, Ko Yi Musu Tambaya akan Wani Abu Daban Dadai Makamantansu, Wani Tuntube dadin gushi shine,…

Cigaba Da Karantawa

Shekaru Biyar Da Rasuwar Jarumin Soja Kanar Abu Ali

Daga Aliyu Ahmad WAIWAYE Wanene Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali? Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, shi ne kusan batun da ya fi kowanne jan hankalin ma’abota shafukan sada zumunta a Nijeriya a ranakun karshen mako. Laftanal Kanal Abu Ali yana cikin sojoji biyar da suka rasa rayukansu a daren Juma’a, yayin bata kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori a jihar Borno. Rundunar sojojin Nijeriyar ta sha…

Cigaba Da Karantawa

Tsananin Son Zuciya Ne Ya Jefa Zamfara Halin Da Take Ciki – Imam Murtadha Gusau

Assalamu Alaikum Ƴan uwana Zamfarawa kuyi hakuri don Allah, domin watakila, a cikin abun da zan fada a samu abun da zai bata ma wani rai, ko wanda bai yi maka dadi ba, ko wanda zai taba ubangidan siyasar ka ko jam’iyyarka, kai ko ma wanda zai iya taba ka kai tsaye! Amma dai daga karshe, ni zan yi magana ne tsakanina da Allah, akan abun da na gani, na shaida, kuma na sani. Har ga Allah, ba zan taba yin wata kalma ta son zuciya ta ba, ko da…

Cigaba Da Karantawa

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna

Daga: HASHIM BADIKKO Barka da warhaka Mai Girma Kwamishna, tare da fatan kana nan lafiya. Na saurari jawabi, tare da karanta takardar da ka rabawa ‘ƴan jarida kan matakan tsaro da kuka ɗauka a Jihar Kaduna, wanda zai fara aiki daga yau Alhamis 30/09/2021. Lallai duk wanda yake zaune a Jihar Kaduna ya san cewa babu wani abin a zo a gani da Hukuma take yi game da sha’anin tsaro. Kowa yana zaune ne cikin ɗar, da kuma zullumi. Babu wanda ya tsira. Ya Mai Girma Kwamishina! Mafi yawan matakan…

Cigaba Da Karantawa

2023: Adalci Shine Gwamna Ya Fito Daga Jigawa Ta Arewa Maso Gabas – Ahmed Ilallah

Duk da kasancewar wannan batun, batune mai nauyi da wahalar warwarewa, bisa yanayin zamantakewar mu da kuma babancin fahimtar mu akan al’amura irin wannan, kuma ban cika son yin magana irin wannan ba, amma bisa lura da adalcin siyasar Nijeriya, naga ya kamata a tunasar da masu ruwa da tsaki akan wannan batun. Dadi da kari kuma, har gashi an soma buga gangar siyasar 2023. Jahar Jigawa, wadda aka kirkira a watan Augusta, shekara 1991, a lokacin mulkin soja na General Ibrahim Badamasi Babangida, an kirkireta ne daga tsohuwar Jahar…

Cigaba Da Karantawa

Dakatar Da Kyari: ‘Yan Najeriya Na Cigaba Da Bayyana Ra’ayoyin Su

Tun bayan sanarwar da hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayar na dakatar da jami’in ‘yan sanda Abba Kyari, jama’a ke cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da yadda suke kallon lamarin. Abdullahi Muhammad Sani wani mai sharhi ne a Najeriya ga abin da ya rubuta dangane da yadda yake kallon al’amarin. “A ce duk lokacin da mutum zai bada rayuwar shi domin Nijeriya ta ci gaba sai ya samu kalubale daga makiya zaman lafiya?” “Kowa ya san irin kokarin da Abba Kyari yake yi domin zaman lafiyar kasar nan, amma…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Bai Da Ƙwarewar Mulki – BB Faruƙ

Dr Faruk BB Faruk mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa ”rashin fasahar iya gudanar da mulki na janar Buhari na daya daga cikin dalilan da yasa kasar ke cikin shakakin kalubalen tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Dr Faruk ya bayyana hakan ne a cikin shirin Babbar magana da ake gabatarwa a gidan talbijin da radio na liberty dake babban birnin tarayya abuja. Yace ko a maganar karin kudin mai da akayi ban yarda cewar kuskure akayi ba, kawai an bayyana matakin ne aga yadda ‘yan najeriya…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Bai Da Ƙwarewar Mulki – BBC Faruƙ

Dr Faruk BB Faruk mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa ”rashin fasahar iya gudanar da mulki na janar Buhari na daya daga cikin dalilan da yasa kasar ke cikin shakakin kalubalen tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Dr Faruk ya bayyana hakan ne a cikin shirin Babbar magana da ake gabatarwa a gidan talbijin da radio na liberty dake babban birnin tarayya abuja. Yace ko a maganar karin kudin mai da akayi ban yarda cewar kuskure akayi ba, kawai an bayyana matakin ne aga yadda ‘yan najeriya…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Buhari Kyanwar Lami Ce – Sardauna

An bayyana Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Buhari, a matsayin Gwamnatin mara karsashi wadda ta samu nakasu da kuma tawaya a wajen sauke nauyin dake rataye a kafaɗunta. Alhaji Hassan Sardauna ɗan siyasa kuma mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya kwatan ta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kyanwar lami wanda bata cizo balle yakushi, kuma hakan na daya daga cikin dalilan dake sa kowa ke abinda yaga dama a gwamnatin. Hassan Sardauna ya bayyana hakan ne a cikin shirin babbar magana da ake gabatarwa duk ranar lahadi…

Cigaba Da Karantawa

Ƙudurorin Shafe Hausawa Da Harshen Hausa – Daga Ɗankasawa

Da akwai daɗaɗden ƙudiri na kore samuwar Bahaushe a ƙasar Hausa, amman ba da makamai ba. Wannan ƙudirin ana aiwatar da shi ne ta hanyar wasa da hankali da rainin wayau ga Bahaushe. Ga fuskokin wannan ƙudirin Duk sanda Bahaushe ya ce asalin shi Bahaushe ne, sai a jefe shi da maguzanci. Duk wata ƙabila a ƙasar ga, in mutum ya ce asalin shi daga ita ya ke ba’a cewa komi. Amman da zarar mutum ya ce shi Bahaushe ne, sai ace ashe asalin shi Bamaguje ne. Dubarar ita ce…

Cigaba Da Karantawa

Ajandar Shafe Hausawa Da Harshen Hausa – Daga Ɗankasawa

Da akwai daɗaɗden ƙudiri na kore samuwar Bahaushe a ƙasar Hausa, amman ba da makamai ba. Wannan ƙudirin ana aiwatar da shi ne ta hanyar wasa da hankali da rainin wayau ga Bahaushe. Ga fuskokin wannan ƙudirin Duk sanda Bahaushe ya ce asalin shi Bahaushe ne, sai a jefe shi da maguzanci. Duk wata ƙabila a ƙasar ga, in mutum ya ce asalin shi daga ita ya ke ba’a cewa komi. Amman da zarar mutum ya ce shi Bahaushe ne, sai ace ashe asalin shi Bamaguje ne. Dubarar ita ce…

Cigaba Da Karantawa

Sai Mun Cire Hassada Da Girman Kai Kafin Samun Zaman Lafiya A Arewa – Dingyaɗi

Ba Shakka Muddin Muna Son Ganin Ci gaba Da Zaman Lafiya A Arewarmu Sai Mun Debe Hassada, Kwadayi Da Girman Kai A Tsakanin Juna. Cin Duga-dugan Juna Da Manyan Arewa Keyi Ba Abin Da Yake Haifarwa Illa Kiyayya Da Ganin Kyashi Da Tozarta Juna Tare Da Rarrabuwar Kawuna. Arewa Ta Shiga Gararin Da Bata Taba Shiga Ciki Ba A Sakamakon Rashin Hadin Kai, Mutunta Juna Da Son Kai Na Wasu Dake Ganin Ala Dole In Ba Abin Da Suke So Ba; Sai Dai Kowa Ya Rasa. Ba Ruwansu Da Neman…

Cigaba Da Karantawa

Hanyoyi 50 Da Ake Gane ‘Yan Maɗigo – Sister Bilkisu Ahmad

1- Macen da take bayyanawa ‘yar uwarta mace tsiraicinta. 2- Macen da ke yaba kyawun ‘yar uwarta mace ta fuskar sha’awa. 3- Macen da ke rungumar ‘yar uwarta mace ko sumbatarta da nufin wasa. 4- Macen da take nunawa kawarta bidiyon ‘yan madigo. 5- Macen da za ta kama hannun mace ‘yar uwarta ta dinga shafawa babu wani dalili. 6-Ko Macen da za ta dinga shafa gashin kan kawarta. 7- Mace mai lazimtar kwanciya kan cinyar mace ‘yar uwarta ba tare da dalili ba. 8- Macen da a kodayaushe take…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Gaza Wajen Biyan Soyayyar Da ‘Yan Najeriya Suka Gwada Mishi – Ramadan Gwale

Tsantsar soyayyar da ‘yan Nijeriya suka nunawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan zabensa da suka yi sau biyu, ita ce lokacin da ba shi da lafiya ya kwanta a asibiti a Landan sama da kwana dari. Ko Ina, Masallatai da Coci, ko Ina sai kaji ana cewa ayiwa Shugaban kasa adduah Allah ya bashi lafiya. Bil hakki muka dinga yiwa Shugaban kasa addu’a akan Allah ya bashi lafiya. Na san har a cikin Sujjada ina yi wa Shugaban kasa addu’ar samun sauki a lokacin, haka kuma, miliyoyin mutane haka nan…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar goma sha biyu ga watan Rabi-ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Nuwamba, na 2020. Gwamnatin Tarayya da kungiyar malaman Jami’a ASUU, sun ci gaba da tattaunawa, sun ma cimma matsaya har shugabannin malaman, sun koma su sanar da sauran ‘ya’yan kungiyar yadda suka yi da Gwamnatin Tarayya, wanda daga nan ne ake sa ran malaman su hakura su janye yajin aikin. An ci gaba da tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Asalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, goma sha daya ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halita, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Nuwamba, shekarar 2020. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 169 a jihohi da alkaluma kamar haka: Kaduna 74Abuja 42Legas 17Kano 8Ogun 6Oyo 6Ribas 6Ekiti 3Bauci 3Katsina 2Delta 1Ondo 1 Jimillar da suka harbu 66,974Jimillar da suka warke 62,585Jimillar da ke jinya 3,170Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,169 Gwamnatin Tarayya na nan tana ci gaba da…

Cigaba Da Karantawa