Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewa zaratan Sojojin Najeriya da aka tura yankin Allawa cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro ta cikin Jihar Neja, sun janye daga aikin da aka tura su na kakkaɓe ‘yan ta’adda.
Sun janye ne bayan an kashe masu sojoji biyu, ta hanyar ɗana masu nakiya a ranar Laraba.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Manjo Janar Mohammed Garba Mai Ritaya, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa sojojin sabbin tura wa ne a wurin domin su daƙile hare-haren ‘yan ta’adda.
Garba ya ci gaba da cewa baya ga sojoji biyun da mahara suka halaka, wasu guda 9 sun ji raunuka, har an kwantar da su wani asibiti da ba a ambaci sunan asibitin ba.
Shi ma wani mazaunin ƙauyen Allawa tabbatar na da adadin da aka kashe da waɗanda aka raunata ɗin kamar yadda kwamishinan ya bayyana shi ma.
Sai dai kuma Kwamishinan na Tsaro ya ce janye sojojin an yi hakan ne domin a ƙara yawan su.
Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu bai bada amsar tambayoyin da wakilin mu ya tura masa.
Zuwa yanzu dai a cikin sati ɗaya an kashe sojoji shida a yankin.
Ranar Juma’a ce da ta gabata mahara suka kashe soja biyar, a yankin, cikin su har da wani kaftin a Rogo, Kagara da Eumace a Mazaɓar Allawa a yankin Bassa.
Mazauna yankin sun ce sun yanke shawarar guduwa, ganin yadda sojin ke janyewa.
Ganau ya ce ya ga yadda maja’a ke tururuwar ficewa daga ƙauyen, mazan su da matan su, yara da manya.