Gwamnatin Taraba Ta Ci Mutuncin ‘Ya’yan Kungiyar Mu _ Masu Hakar Ma’adinai

BASHIR ADAMU, JALINGO. Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Taraba na cewa Kungiyar Masu Hakan Ma’adinai ta Kasa, Shiyyar Arewa Maso-Gabas ta zargi Gwamnatin Jihar Taraba ta hannun Kwamitin Kula da Hana Tonan Ma’adinan Kasan Jahar, karkashin jagorancin, Janar Jeremiah Faransa (mai ritaya) da kama musu a kalla membobi 3,500 tare da tozatar dasu, da kwace Gwalagwalansu na Miliyoyin Naira a Karamar Hukumar Tongo na Jihar Adamawa. Sakataren Kungiyar na Shiyyar Arewa Maso Gabas, Kwamarade Salisu Shu’aibu Mai-zare yayi zargin a wurin wani taron Manema labarai da ya kira…

Cigaba Da Karantawa

Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bada Tallafin Karatu Ga Daliban Arewa

Gidauniyar tunawa da marigayi Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta ba da tallafin karatu ga dalibai 200 wadanda suka fito daga jihohi 19 na Arewa har da Abuja. Shugaban Gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar ya sanar da hakan a tattaunawar shi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala bikin bayar da tallafin wanda ya gudana a Kaduna. Injiniya Gambo ya ƙara da cewar tallafin karatun kebe shi ne kawai ga dalibai dake karantar ɓangaren kimiyya da fasaha a manyan makarantun Najeriya. “Mun zaɓo dalibai guda goma goma daga jihohi 19…

Cigaba Da Karantawa