An bayyana ilimin ‘ya’ya Mata a matsayin wani tubali wanda ke gina al’umma gaba daya kasancewar duk wanda ya ba ‘ya mace ilimi to tamkar ya ba al’umma gaba daya ne. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar makarantar Nurul Huda Islamic Academy dake Kaduna Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin yayen daliban makarantar wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Ta ƙara da cewar a tsarin da suka ɗauka a makarantar Nurul Huda shine bada…
Cigaba Da KarantawaDay: August 1, 2023
Ilimin ‘Ya’ya Mata Shi Ne Tubalin Ginin Al’umma – Alawiyyah Aminu Dantata
An bayyana ilimin ‘ya’ya Mata a matsayin wani tubali wanda ke gina al’umma gaba daya kasancewar duk wanda ya ba ‘ya mace ilimi to tamkar ya ba al’umma gaba daya ne. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar makarantar Nurul Huda Islamic Academy dake Kaduna Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin yayen daliban makarantar wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Ta ƙara da cewar a tsarin da suka ɗauka a makarantar Nurul Huda shine bada…
Cigaba Da KarantawaEl Rufai Ya Cancanci Kowane Irin Mukami: Martani Ga Kungiyar Mahaddata- Sheikh Khamis
Abin mamaki ne yadda ‘yan siyasa masu iƙirarin addini da kare martabar almajirai suke shiga rigar almajirci suna fakewa da addini don cinma wata bukatar su ta siyasa da son zuciya. Mun wayi gari da ganin wasu rubuce rubuce dake korafi akan saka mai girma tsohon gwamnan mu na jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El rufai a jerin wadan za’a tantance a matsayin minista daga jihar Kaduna kuma ake danganta wannan labarin da gidan daya daga cikin manyan Malaman da ake girmamawa a kasar nan. Har ga Allah babu wanda…
Cigaba Da KarantawaECOWAS Ta Ba Sojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Wa’adin Mako Guda
Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun bai wa sojojin da suka kwace mulki a Nijar wa’adin mako guda da su janye, yayin da kuma suka kakaba wa kasar takunkuman karayar tattalin arziki da kudade. Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS mai mambobi 15 sun bukaci a gaggauta sakin shugaba Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan kujerarsa bayan sojojin sun hambarar da gwamnatinsa tare da tsare shi tun ranar Larabar da ta gabata. Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a…
Cigaba Da KarantawaJawabin Tinubu Ga ‘Yan Najeriya: Ku Kara Hakuri Sauki Na Nan Tafe
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa ma’aikatan ƙasar alƙawarin cewa nan gaba kaɗan gwamnatinsa za ta ƙara musu albashi, kamar yadda ya bayyana cikin jawabinsa a yammacin Litinin. Kazalika ya sake cin alwashin ɓullo da matakan sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa raɗaɗin da suke ji na cire tallafin man fetur, wanda ya ce “wasu mazambata ne ke amfana da shi”. “A cikin wata biyu, mun adana sama da naira tiriliyan ɗaya na tallafin mai da ake kashewa kan abin…
Cigaba Da Karantawa