Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) sun bayyana matsalar tsaro da yankin arewa ke fama dashi a matsayin wata fitina da kowane mahaluki a yankin ya kamata ya bada gudummuwa wajen maganceta.
Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Alhaji Nastura Ashiru Sherif ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan ganawarsu da gwamnonin arewa a taron da gwamnonin suka gudanar a Kaduna.
Ashir Sherif yace sun gabatar da kuduri a gaban gwamnonin na matakan da ya kamata a dauka domin shawo kan matsalar tsaro da garkuwa da mutane dake addabar yankin.
“Ba wai amfani da ƙarfin soja kaɗai bane matakin yaƙi da matsalar tsaro, akwai bukatar yaƙi da talauci da samar da ayyukan yi ga matasa wanda hakan babban mataki ne na kawar da matsalar”
Gamayyar Kungiyoyin sun ce da akwai shiri da suke dashi inda za su sanya dukkanin jama’ar yankin ciki domin lalubo hanyoyin dakile matsalar tsaro tun daga kan gwamnoni da sarakuna da malamai zuwa ‘yan jarida da masu wasannin kwaikwayo.
Sherif ya ce sun gamsu da irin salon da gwamnoni ke ɗauka a yanzu ta hanyar tunkarar matsalar domin ko a ganawar da suka yi dasu sun ga yadda gwamnonin suka nuna damuwa kan halin da yankin arewa ke ciki wanda wannan alama ce babba dake nuna al’amura za su sauya.