Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na Saudiyya don halartar taron Tattalin Arziki na Musamman na Duniya da za agudanar a ƙasar.
Taron zai mayar da hankali wajen haɗin kai don bunƙasa samar da makamashi a duniya.
Shugabannin gwamnatoci da na cibiyoyin kasuwanci da masana fiye da 1,000 ne daga ƙasashe 90 ake sa ran za su halarci taron da za a gudanar a birnin Riyadh.
Manufar taron ita ce ɗora wa kan nasarorin da ka cimma a taron shekarar da ta gabata da aka gudanar birnin Geneva na ƙasar Switzerland.
Mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce ya ce shugaba Tinubu zai yi amfani da taron wajen ƙarfafa manufofin gwamnatinsa da ake yi wa laƙabi da “Renewed Hope Agenda”.
Tun da farko shugaba Tinubu na ziyarar aiki a birnin Hague na ƙasar Netherlands, bisa gayyatar da firaminstan ƙasar ya yi masa don wata tattauna hanyoyin zuba jari tsakanin ƙasashen biyu.