Tsananin Zafi Ya Hallaka Sama Da Mutum 40 A Jihar Kano

IMG 20240229 WA0298

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa hukumomia jihar sun fitar da wasu jerin shawarwari ga al’umma kan yadda za su kare kansu daga yanayin da ake ciki na tsanani zafi.

Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton ƙaruwar zazzaɓi mai zafi da hukumomin lafiya a jihar suka danganta da ƙaruwar yanayin da kaɗawar busasshiyar iska.

Bayanai na cewa irin wannan yanayi da aka shiga ya haifar da mutuwar mutum fiye da 40 sannan da dama suna cikin mawuyacin hali.

Kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ya ce jami’an da suka tura don gudanar da bincike sun gano cewa tsananin zafin da ake fama da shi ne ya haddasa zazzaɓi mai zafi.

A cewarsa, babu mamaki zazzaɓin ne ya jawo mace-macen da aka gani a wasu garuruwa kamar Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a makon jiya.

Dr Labaran ya ce rahotannin da suka samu sun nuna cewa an fara ganin ƙaruwar zazzabin mai zafi da kuma mace-mace ne tun fa arkon watan jiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply