Dakarun Sojin Najeriya sun ce sun yi wa ma?oyar ‘yan ta’adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ?ananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno.
Wata sanarwa da mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa ‘yan ta’ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu.
Samamen na ha?in gwiwa tsakanin rundunar Operation Ha?in Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin ‘yan ta’ddan abin da ya tilasta wa da dama tserewa.
Sai dai Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan sun yi yunkurin far wa sojojin sashe na 4 na MNJTF a garin Lada da ke kan iyakar jamhuriyar Nijar da Najeriya.
“Mun bi bayan ‘yan ta’addan da suka tsere a kan babura 8, inda muka gano su a wurare biyu da ke kauyen Zarri, mai tazarar kilomita 28 daga gabashin Damasak da Mala Alide a karamar hukumar Mobbar ta Jihar Borno,” in ji Gabkwet.
Ya ce an gano wani wuri da ‘yan ta’addan suke ?oye wa tare da baburansu a cikin Kauyen, karkashin bishiyoyi.
Ba ya ga wannan, dakarun Operation Ha?in Kai sun kuma kai hare-hare ta sama karkashin jagorancin jiragen le?en asiri na ?asar Nijar (ISR) a wuraren da ‘yan ta’addan suke.