Masarautar Zazzau Ta Yi Nadin Turakin Bai Zazzau

IMG 20240504 WA0222

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Zazzau na jihar Kaduna na bayyana Masarautar Sarkin Zazzau ta naɗa Alhaji Ibrahim Bello Rigachikum a matsayin Turakin Bai Zazzau Hakimin Gundumar Ragachikum.

An yi nadin ne a fadar mai martaba sarkin Zazzau Dr Ahmad Nuhu Bamalli dake birnin na Zazzau a ranar juma’a, dimbin jama’a daga sassa daban-daban na ciki da wajen Jihar Kaduna suka halarci nadin.

Da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Rigachikum jim kaɗan bayan kammala bikin nadin, sabon Hakimin na Rigachikum Turakin Bai Zazzau Alhaji Ibrahim Bello Rigachikum ya gode wa masarautar Zazzau da mai martaba Sarki bisa ga wannan nadin da suka yi mishi inda ya yi alkawarin bayar da dukkanin gudummawar da ta kamata wajen ciyar da masarautar dama jihar Kaduna gaba.

Barista Ibrahim Bello Rigachikum wanda mataimaki ne na musamman ga mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani a bangaren Masarautu, yace wannan nadin da aka yi mishi wata dama ce ya samu wajen sauke nauyin da aka ɗora mishi.

Hakimin ya yi kira ga jama’ar Masarautar Zazzau da Jihar Kaduna gaba daya da cewa su rungumi akidar zaman lafiya domin babu wani cigaba da za a samu matukar babu zaman lafiya.

Turakin Bai Zazzau ya kuma shawarci matasa dake Jihar Kaduna da cewa su tashi tsaye wajen dogaro da kansu ta hanyar koyon sana’a ba wai jiran aikin gwamnati kadai ba domin samun al’umma ta gari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply