Kaduna: Da Ni Ne Gwamna, Da El-Rufa’i Ya Gane Shayi Ruwa Ne – Shehu Sani

images (36)

Daga Ibrahim Ammani

Tsohon ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya soki lamirin gwamnatin Jihar kan gaza yin wani kataɓus akan tsohon gwamnan jihar El Rufai da muƙarrabanshi waɗanda suka talauta jihar da mugun bashi.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna Sanata Shehu Sani yace abin takaici ne yadda gwamnatin jihar ke shirin cika shekara guda akan mulki amma barayin da suka talauta jihar suna walwala cikin gidajensu ba tare da wata takura ba.

“Ina tabbatar muku da ni ne Gwamnan jihar Kaduna a yau wallahi da El Rufai ya gane shayi ruwa ne, amma ya ci Safa ba irin mu bane ke jagorantar Kaduna”.

Sanata Shehu Sani ya ƙara da cewar El Rufai ya kashe Jihar Kaduna gaba ɗaya da bashi, domin ya karbi bashin dala miliyan 350 duka ƙyale ƙyalen da ya yi na gyaran titi bai wuce na dala miliyan 40 ba ina sauran kudaden suke?!

Labarai Makamanta

Leave a Reply