Bauchi: Gwamna Bala Ya Tube Rawanin Masu Sarauta Shidda

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewa Gwamnatin jihar ta tabbatar da korar hakimai da dagatai shida saboda a cewarta an same su da shiga harkokin siyasa da cin iyakar gandun dazuka ba bisa ƙa’ida ba.

Matakin korar wanda ya shafi masu riƙe da sarauta a masarautun Bauchi da Katagum, yana ƙunshe ne a sanarwar da Babban Sakataren riƙo a hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomi, Nasiru Ibrahim ya fitar.

Mutanen da lamarin ya shafa a cewar sanarwar, sun haɗar da Hakimin Udubo, Alhaji Aminu Muhammad Malami da Hakimin Azare Alhaji Bashir Kabir Umar da Dagacin Gadiya, Umar Omar da Dagacin Tarmasawa, Umar Bani dukkansu a masarautar Katagum.

Sai kuma Dagacin Beni Bello Suleman da Dagacin Badara, Alhaji Yusuf Aliyu Badara a masarautar Bauchi.

Sanarwar ta ambato hukumar na cewa ta amince da korar masu riƙe da sarautun ne saboda shiga harkokin siyasar jam’iyya da aikata ba daidai ba da cin iyakar dazuka ba bisa ƙa’ida ba da sare itatuwa da ɓarnatar da dukiyar jama’a da rashin biyayya, waɗanda suka saɓa da dokokin aikin gwamnati.

Labarai Makamanta

Leave a Reply