Kwarewar Tinubu A Fannin Tattalin Arziki Ya Ceto Miliyoyin ‘Yan Najeriya Daga Talauci – Shettima

IMG 20240504 WA0033

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu yayi a shekarar data gabata ya ceci rayuwar al’umma.

Ya bayyana sauye-sauyen a matsayin wadanda suka zama wajibi idan aka yi la’akari da halin da Najeriya ke ciki na talauci lokacin da ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya zabi hanyar da zai ceci rayuwar al’ummar kasar maimakon hanyar da zata iya janyo mutuwar tattalin arzikin kasar, in ji Shettima a lokacin da yake jawabi a matsayin babban bako a taron na biyu na Chronicle Roundtable a Abuja.

Ya kuma bayyana dalilin da ya sa gwamnatin ta yi aiki da tsarin cire tallafin man fetur da kuma shiga tsakani a kasuwar canji, inda ya ce shugaban kasar ya zabi hanya mafi tsauri amma mafi tabbatacciyar hanyar samun saukin halin da kasar ke ciki.

Shettimma ya kuma roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin yana mai tabbatar musu da cewa matakan da aka dauka za su samar da sakamakon da ake bukata ga al’ummar kasar nan ba da jimawa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply