Shugaba Bola Tinubu ya fara kamfen da taken sa na ‘Renewed Hope Agenda’, Ajandar Fatan Samun Sabon Canjin Rayuwa.
Ya fara kamfen wurjanjan a daidai lokacin da gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta tsunduma ‘yan Najeriya cikin ƙuncin rayuwar matsalar sauya launin takardun Naira.
Wannan ya janyo mutane da dama sun ƙagara mulkin Buhari ya ƙare, domin ana ganin idan har Tinubu ya hau mulki, to zai iya yin amfani da ƙudirorin sa na ‘Renewed Hope Agenda’, ya samar wa ‘yan Najeriya sassaucin rayuwa.
To sai dai kuma maimakon haka, ‘Renewed Hope Agenda’ ya fara da jefa Nejeriya cikin raɗaɗin tsadar rayuwa, yayin da Shugaba Tinubu ya fara mulki da cire tallafin fetur, tun a wurin da aka rantsar da shi. Dama kuma ya ce ko da ‘yan Najeriya za su yi kuka su gaji, to idan ya zama shugaban ƙasa sai ya cire tallafin fetur.
Tun daga ranar da aka cire tallafin fetur ake fama da tsadar rayuwa a ƙasar nan, kuma ba a san ranar fita daga wannan uƙuba ba.
Tsadar fetur ta haifar da tsadar komai a Najeriya, har ma da hauhawar farashin Dala, inda sai da ta haura Naira 1,5000, yayin da litar fetur ta koma Naira 630. Yanzu kuma ƙarancin fetur ya maida lita 1 zuwa Naira 1,050 a gidajen mai, kuma ya yi matuƙar wahala.
Tsadar abinci ta kai munin da sai da Gwamnatin Tarayya da Jihohi suka riƙa raba kayan tallafin abinci ga masara galihu.
Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce yadda gwamnati ke gaggawar bijiro da tsare-tsare ko dokokin da za su takura jama’a, amma kuma ta ke jan-ƙafa wajen bijiro da tsare-tsaren da za su sauƙaƙa wa talakawa tsadar rayuwa.
An cire tallafin fetur a rana ɗaya, amma kuma har yau dukkan tsare-tsaren da gwamnati ta ce za ta bijiro da su domin kawo sassauci, sai dabur-dabur da dawurwura ake yi a kan su. Ina banda rabon tallafin abinci da aka yi, wanda shi ma bai taka kara ya karya ba, sai dai ga mai jin yunwa ya kira abincin ‘ci-kada-ka-mutu.’
Kuɗin fetur ya ƙaru, kuɗin ruwa ya ƙaru, kuɗin wuta ya ƙaru. Kuɗin shiga motar haya ya ƙaru. Kuɗin gina gida ya ƙaru. Kuɗin kama hayar gida ya ƙaru. Kuɗin kowane kayan abinci ya ƙaru. Kuɗin kayan masarufi ya ƙaru. Kuɗin makarantar yara ya karu. Kuɗin sutura ya karu. Kuɗin komai ya ƙaru, amma kuma albashi na nan bai ƙaru ba.
Matsalar wutar lantarki sai ƙara muni ta ke yi. Masu amfani da janareto wajen gudanar da sana’o’i, a yanzu babu riba.
Jama’a sai rasa aikin su suke yi, ana sallamar su. Birkiloli da leburori babu aiki sosai.
A cikin wannan mawuyacin halin kuma ‘yan ta’adda, mahara da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sai ƙara ƙarfi su ke yi a Arewa.
Abin tambaya a nan shi ne, wane tasiri ko alfanu za a iya cewa ke tattare da Shirin ‘Renewed Hope Agenda’, shirin da a ƙarƙashin sa ruwan sanyi ma na yi wa talaka wahalar samu, a lokacin da yawancin gidaje ma abinci na gagarar magidanta da ‘ya’yan su?