Ketare: An Yi Yunkurin Hallaka Salman Rushdie A Amurka

Rahotanni daga birnin New York na ƙasar Amurka na bayyana cewa wani mutumi ya kai wa shahararren marubucin nan, Salman Rushdie, hari yayin da yake kan dandamali zai yi jawabi a ƙasar Amurka.

Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, ‘The Satanic Verses,’ da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a wani gari dake yammacin New York.

A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi shigar burtu zuwa kan dandamalin da Marubucin ke shirin gudanar da Lakca, inda ya rinka bugunsa yana daɓa masa wuka.

Shaidun da lamarin ya auku a gaban su, sun ce mutumin ya farmaki Mista Rushdie ne yayin da ake gabatar da shi a gaban taron Jama’a.

Bayanai sun nuna cewa mahalarta taron ne suka yi kokarin zuwa kan Dandamalin domin kai masa ɗauki, amma ana tsammanin an daɓa masa wuƙa a wuya.

A halin yanzu, ba’a san halin da Fitaccen marubucin ke ciki ba, amma ‘yan sanda sun tabbatar da cewa an daɓa wa wani mutumi wuƙa, ba su fayyace ko waye ba a bayanan su. Shaidu sun ce an ɗauke shi a Helikwafta domin zuwa a kula da lafiyarsa yayin da aka kama mutumin da ya kai masa farmakin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply