An Rufe Rassan Bankin UBA Shidda A Jihar Kaduna

IMG 20240425 WA0037

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai samamen ne bayan da hukumar gudanar bankin ta gaza mutunta takardun da aka aike masu.

Tawagar hukumar, bisa jagorancin sakataren hukumar gudanarwa da mai bai wa hukumar shawara kan shari’a, Barista Aysha Muhammad, ta rufe rassan bankin tare da tallafin jami’an tsaro.

Barista Aysha ta ce “bisa sashe na 104 na dokar haraji, hukumar ta samu izinin kotu ta ƙwace tare da gano naira miliyan 14 da ɗoriya na kuɗin haraji da ba a biya ba tsakanin 2019 zuwa 2021 daga bankin da ke tafiyar da harkokinsa a Kaduna.”

Zuwa yanzu dai bankin bai ce komai ba game da rufe wasu sassan nasa sannan hukumar bankin a Kaduna ba ta ce komai ba da aka tuntuɓe ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply