Satar Danyen Mai: Najeriya Na Asarar Naira Tiriliyan 1.29 Duk Shekara – Kakakin Majalisar Wakilai

IMG 20240307 WA0056

Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce Najeriya na asarar Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara sakamakon satar mai, fasa bututun mai da sauran laifuka. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Najeriya tana asarar kusan gangar ɗanyen mai 300,000 kowace rana saboda sata.

Kakakin majalisar wakilan ya bayyana hakan ne ta hannun shugaban kwamitin tsaro na majalisa, Babajimi Benson, a wajen ƙaddamar da cibiyar horas da sojojin ruwa a Eleme, jihar Ribas a ranar Juma’a.

Ya ce lamarin ya haifar da ƙalubale ga rundunar sojojin ruwan Najeriya domin ta tashi tsaye wajen gudanar da aikinta na bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasa.

Ya buƙaci sojojin ruwan Najeriya da su kare tare da tsare martabar yankin ruwan Najeriya daga duk wata barazana, “Abin takaici, ana ƙiyasin cewa Najeriya tana asarar sama da ganga 300,000 na ɗanyen mai a kullum, ta hanyar satar mai, fasa bututun mai da sauran laifuka.”

“Hakan ya haifar da asarar kuɗaɗen shiga da aka ƙiyasta sun kai Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara.” Saboda haka, damuwa da na yi da asarar da satar mai ke jawowa Najeriya, na kafa kwamiti na musamman kan satar ɗanyen mai a ranar, 22 ga watan Nuwamba 2023, domin zaƙulo matakan da ya kamata a ɗauka.

“Na yabawa rundunar sojojin ruwa bisa matakan da ta ɗauka ya zuwa yanzu, sannan ina roƙonsu da su ci gaba da yin hakan.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply