Majalisar Wakilai Ta Ki Amincewa Da Kudurin Dakatar Da Sabon Tsarin Harajin Internet

IMG 20240307 WA0056

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da kudirin dakatar da sabon harajin internet da Babban bankin Najeriya ya buƙaci Bankuna Su fara

A zaman majalisar na ranar Laraba, Hon. Mansur Manu Soro ya nuna damuwarsa, inda ya nuna cewa shirin karbar harajin bai dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta a halin yanzu.

‘Yan majalisar sun bayyana imanin cewa bai kamata alhakin sarrafa kudaden da aka tara ya kasance ƙarƙashin kulawar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya bukaci dan majalisar ya janye kudirin, tare da baiwa shugabannin majalisar damar tattaunawa kan lamarin tare da tantance matakin da ya dace.

Tun bayan da babban bankin Najeriya CBN ya bayyana kudirin cire 0.5 na harajin internet ga musayar kudade a bankunan ‘yan Najeriya, jama’a ke ta faman tattaunawa akan batun.

Labarai Makamanta

Leave a Reply