Tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su sake jikinsu domin rungumar tsarin
Lauyan ya bayyana haka ne a ran Laraba 8 ga watan Mayu inda ya ce Tinubu ya na matukar jin tausayin ‘yan kasar
Abuja – Daniel Bwala, tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba ‘yan Najeriya shawara. Bwala ya bukaci ‘yan ƙasar su yi gaggawar sabawa da tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu musamman kan harajin tsaron yanar gizo.
Bwala ya musanta cewa Tinubu bai kula da halin da ake ciki inda ya ce wahala ba za ta tabbata ba. Tsohon hadimin Atiku na magana ne kan sabon tsarin harajin 0.5% da bankin CBN ya kawo domin tsaron yanar gizo. Bwala ya ce za a shiga wahala “Babu wanda ya ke tunani cewa shugaban kasa ya dauki wannan mataki wanda ya zama dole ba za a sha wahala na wani dan lokaci ba.” “Kamar lokaci ne na haihuwa dole za a sha wahala kadan kuma dole za a sadaukar.” “Idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan hali abin da ya kamata ya yi shi ne kokarin sabawa da hakan, wahala ba za ta ɗore ba, wannan shi ne tsarin rayuwa
Daniel Bwala Bwala ya ce Tinubu ya sha fada cewa ‘yan Najeriya suna cikin wani hali wanda ya fadi hakan ya fi a kirga. CBN ya ƙaƙaba sabon harajin 0.5% Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo sabon tsarin biyan haraji domin tsaron yanar gizo a kasar baki daya. Bankin daga bisani ya jero wasu hada-hadar kudi 16 da wannan sabon tsarin biyan haraji ba zai shafa ba a kasar. ‘Yan ƙasar da dama sun kushe sabon tsarin da babban bankin ya kawo inda suka koka kan halin da a yanzu ‘yan Najeriya ke ciki.