Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, a zamain mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika da ‘yarsa Fatima kan naira miliyan 100 kowannen su.
A ran Alhamis ne aka gurfanar da Sirika da ƴarsa a gaban kotun.
Hukumar EFCC ce ta maka tsohon ministan a kotu domin a kwato wasu Naira biliyan 2.7 da take zargin an tafka harkalla a kansu lokacin yana minista.
Sirika ya yi shekara takwas ya na Ministan sufuri sannan an gurfanar da shi tare da ‘yarsa Fatima, sai Jalal Hamma da kuma kamfanin Al-Duraq Investment Limited, bisa tuhumomi shida a kan su.
Ana neman Naira biliyan 2.7 a hannun su.
Tun a ranar 23 ga Afrilu Hadi Sirika yake tsare a hannun EFCC a Abuja, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito.
An tsare shi a Ofishin Shiyya na EFCC da ke kan titin Formella Street, Wuse 2 Zonal Office.
Zaman kotu
“Masu bincike sun gayyaci tsohon ministan domin yi masa tambayoyi, dangane da wata kwangila da ake zargin an danƙara zambar maƙudan kuɗaɗe a cikin ta, wadda aka yi a Ma’aikatar Harkokin Sufurin Jiragen Sama a zamanin sa.
“Tun a lokacin ya amsa gayyata, kuma aka tsare shi.” Haka wata majiya daga EFCC ta shaida.
A zamanin Hadi Sirika ne ya na minista ya ƙaddamar da Jirgin Najeriya, wanda daga bisani aka gane abin ashe duk gidoga ce da rufa-rufa.
Mai shari’a Sylvanus Orji ya amince da bukatar belin wadanda ake tuhumar, bayan sun ki amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Bayan sauraron dukkan bangarorin, Mai shari’a Orji ya bayar da belin kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma a kan kudi miliyan 100 tare da tsayayyu biyu kowanne.
Mai shari’a Orji ya kara da cewa rashin cika sharuddan belin zai sa a tura wadanda ake tuhuma zaman gidan gyaran hali.
” Dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya ma wanda aka beli ya kasance yana da kadarar a cikin Babban Birnin Tarayya.
“ Sannan kuma wadanda ake tuhumar kada su yi balaguro zuwa wajen kasar.
Daga ƙarshe sai aka gargaɗi waɗanda ake tuhuma cewa duk wanda ya kasa cika sharuddan belin, za a tsare shi a gidan gyara halin.
Za a ci gaba da shari’ar a ranakun 10, 11 da 20 ga watan Yuni.