Yadda Aka Rika Wasoson Dukiyar Kasa Da Sunan Biyan Kwangila A Makon Karshe Na Mulkin Buhari

Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria (cropped3)

Kwanaki biyar kafin cikar wa’adin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Hukumar Raya Ilmin Manyan Makarantu (TETFund), ta bayar da kwangilar Naira biliyan 3.8, (N3,812,500,000) ba tare da bin ƙa’ida ba.

An kamfaci kuɗaɗen an biya ba tare da an yi kwangilar ba tare da alamar aiwatar da ko kaɗan na kwangilar ba.

PREMIUM TIMES ta bankaɗo yadda TETFund ta biya Naira biliyan 2.9 (2,932,032,516.28) a ranar 30 ga Yuni da 17 ga Nuwamba, 2023.

TETFund ta kamfaci kuɗaɗen daga cikin asusun ayyukan kasafin 2023, waɗanda aka ware domin yin wasu ayyuka a manyan makarantu 251 a cikin faɗin ƙasar nan.

Kuɗaɗen na ayyukan rarar kasafin 2023 ɗin dai Naira biliyan 15.2 ne. Amma maimakon TETFund ta sakar wa makarantun kuɗaɗen, kamar yadda doka ta tanadar, sai hukumar ta cire kaso 50 bisa 100 na kuɗaɗen, daga kowace makaranta. Kuɗi sun tashi Naira biliyan 7.6 kenan.

An gano cewa TETFund ba ta buga tandar neman ‘yan kwangilar da za su yi gasar neman kwangilar ba, kamar yadda dokar bayar da kwangiloli ta ƙasa ta tanadar.

Sannan kuma babu amincewar Majalisar Zartaswa ko shi kan sa Shugaban Ƙasa.

TETFund ta bayar da kwangilar bogin ce ga wani kamfani mai suna Fides Et Ratio Academy.

Wannan kamfani dai na gidoga ne, domin ko shafin yanar gizo ba shi da shi a intanet. Amma dai TETFund ta ce “kamfanin Lasisin IP ne mallakar Farfesa Klaus Stierstorfer ne.”

Takardar bayar da kwangilar ta na ɗauke da sa hannun amincewar Daraktan Ayyukan Musamman, Kolopo Akulana.

An tuntuɓi Hukumar Tantance Haƙiƙanin Adadin Kuɗaɗen Kwangila (BPE), amma ta ce ba ta san da labarin bayar da kwangilar ba, kuma ba a tuntuɓi Ofishin BPE domin ya tantance kuɗaɗen kwangilar kamar yadda doka ta tanadar ba.

An danƙara wa kamfanin da aka ce an bai wa kwangilar Naira 550 a ranar 30 ga Yuni, 2023, a asusun bankin sa na Fedility Bank.

Kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya amince a tura kuɗaɗen kamar yadda lambar tura kuɗaɗen ta nuna, wato CBN/PROJ/224/JUN2023.

Ranar 12 ga Yuli kuma aka tura Naira miliyan 820, kuma ranar 26 ga Yuli aka tura Naira biliyan 1.5, sai kuma ranar 17 ga Nuwamba aka tura Naira miliyan 62, kuma duk CBN ke tura kuɗaɗen bisa umarni da amincewar TETFund.

Labarai Makamanta

Leave a Reply