SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Amfani Da Karfin Iko Wajen Hana CBN Amfani Da Harajin Internet

IMG 20240228 WA0023

Kungiyar Rajin Kare Ha??in Jama’a ta SERAP, ta yi kira ga Shugaban ?asa, Bola Tinubu cewa , “ya yi amfani da ?arfin ikon sa ya gaggauta taka wa Babban Bankin Najeriya (CBN) burki, kada ya bari bankuna su fara cirar Harajin Da?ile Har?allar Ku?a?e ta Hanyar Intanet, wato ‘Cybersecurity’ da aka ?a?aba cikin wannan satin.

SERAP ta ce ?a?aba wa ‘yan Najeriya biyan harajin ta hanyar cire masu harajin daga ku?a?en taransifa a bankuna, da Gwamnan CBN Yemi Cardoso zai fara, ya karya Dokar Najeriya ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Talata, SERAP, wadda ?ungiya ce mai sa-ido kan batutuwan cin hanci da rashawa, ta yi kira da a sake duba dokar wadda CBN ke so ta yi amfani da ita wajen ?a?aba cire harajin.

“Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta umartar Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya gabatar da ?udirin gyaran Sashe na 44 da sauran batutuwan da ke ?ar?ashin Dokar ‘Cybercrime’ Act ta 2024.”

Sun kuma yi kira ga Shugaba Tinubu ya dakatar da Ofishin Mashawarcin Shugaban ?asa kan Harkokin Tsaro (NSA) daga fara aiki da Sashe na 44 na Dokar ‘Cybercrime’ ta 2024.

Cikin sanarwar wadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu, ya ce, “mun bai wa Shugaban ?asa wa’adin sa’o’i 48 ya hana CBN fara amfani da Dokar Cire Harajin Da?ile Har?allar Ku?a?e ta Intanet, wadda za a ?a?aba wa ‘yan Najeriya.”

Sun ce cirar ku?a?en haramun ne, kuma ya keta doka.

SERAP ta ce lauyan ta Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya fara shirye-shiryen garzayawa kotu domin shigar da ?ara, idan ba a soke cirar harajin ba.

A ranar Litinin ce dai CBN ya umarci bakuna cewa daga ranar 23 ga Mayu, 2024, su ri?a cirar kashi 0.5 na Harajin Da?ile Har?allar Ku?a?e a Intanet, wato ‘Cybersecurity Levy’, daga asusun masu tura ku?a?e a banki.

Related posts

Leave a Comment