Baragurbin Ministoci Ne Suka Sa Ba A Ganin Kokarin Tinubu – Sanata Ibrahim

IMG 20240510 WA0026

Yawancin ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa ba sa kokari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a jam’iyyar APC.

Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu Yan Dagaji ne kuma ba sa tabuka komai.

Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.

A cewar dan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin kasar, amma babu wani tsari da mataimaka da za su sa ga kai gaci.

Ya shawarci shugaban kasar da ya rusa majalisar ministocin sa saboda rashin cancanta.

“Dole ne ka rusa majalisar ministocinka ka naɗa mutane masu ilimi. Majalisar ministoci ta yi sanyi da yawa kuma ba a gani kokarin gwamnatin ka,” inji Ibrahim.

“Ya kamata ka sallami wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa nan take. Idan ka kasa yin haka, to kai za a rika ganin laifi kuma hakan zai zama illa ga ƙasarmu. Ba na nagin yawancin ministocin a matakin farko na A ba. Yawancin su suna cikin makin B ko C.

Labarai Makamanta

Leave a Reply