Zan Sauya Fasalin Darikar Tijjaniya – Sanusi

A hira da gidan rediyon BBC Hausa Khalifa Muhammadu Sunusi II ya bayyana wa BBC Hausa cewa baban abinda zai fara maida hankali a matsayinsa na halifan tijjaniyya na Najeriya shine, na farko zamu fara zama da junan mu ‘yan tijjaniyya (masu hannu da shuni) mu kara fahimtar juna, sannan mu duba kalu balen da tijjaniyya ke fuskanta da addinin musulunci baki daya, musamman arewacin Najeriya.

Akwai matsaloli a harkar ilimi da iyali da yara da abinda ya shafi zawiyyoyi da tsangayu, zamu tafi da jagorancin Tijjaniyya daidai da ƙarni na 2, zamu fuskanci matsalolin da muke fuskanta domin mu kawo gyara, lallai ‘yan tijjaniyya miliyoyin mutane ne da ya kamata ace suna da tsari da zai taimake su wajen samar da sauyi da taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kansu gaba da kasar su baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply