Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shirin Harajin Internet Da Gwamnatin Tarayya Ta Bullo Dashi

IMG 20240307 WA0056

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin dakatar da Babban Bankin na CBN da gaggawar dakatar da aiwatar da harajin ta yanar gizo da babban bankin ya kaddamar, kamar yadda dokar ta tanada.

Majalisar ta nuna damuwarta kan yadda ‘yan Najeriya zasu iya fahimtar harajin da babban bankin ya fitar, domin bai yi daidai da ka’idojin da ke kunshe a cikin sashe na 44 (2a) na dokar aikata laifuka ta yanar gizo ba dangane da masu karbar harajin.

A martanin da shugaban marasa rinjaye Kingsley Chinda (PDP, Rivers) ya gabatar a madadin daukacin mambobin majalisar, Majalisar ta bukaci babban bankin kasar da ya gaggauta janye takardar da ta bayar a baya dangane da aiwatar da harajin, maimakon haka ta fitar da wata sabuwar takardar da ta yi daidai da tanadin dokar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply