Kaduna: Za A Kaddamar Da Shirin Hadakar Makarantu Kan Batun Tsaro

IMG 20240310 WA0186

Gwamnatin Jihar Kaduna zata hade wasu makarantun Sakandare dana firamare wajen guda da yawan su ya kai 359 dake yankunan da matsalar tsaro ta fi Kazanta a fadin Jihar.

Manufar hakan shi ne tabbatar da cewar ko wane Yaro ya sami damar zuwa makaranta don samin ilimin daya da ce duk da kalubalen tsaro.

Gwamnatin Jihar ta dauki wannan matakin ne bayan data sami rahoton raguwar alkaluman adadin Yaran da suke zuwa makaranta, saboda barazanar tsaro.

Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani ne yake bayyana haka ta bakin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin sa Alhaji Liman Sani Kila, a wajen bude taron kaddamar da Shirin samar da jami’ai da zasu dunga bayar da cikakken tsaro a Makarantu wanda hukumar Yansanda ta shirya a Dakin taro na Dandalin Murtala Square dake Jihar Kaduna.

Gwamnatin ta ce tuni ta Samar da jami’ai har manta basu horo na musamman don tabbatar da igancin tsaron a Makarantu.

Kaddamar da hare-hare, barazana kisa da satar Dalubai da Malamai a makarantu ba wani abu bane sabo a fadin kasar nan musamman a yankin Arewa, lamari ne da aka fara tun daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply