#EndSARS: Bamu Kashe Kowa A Lekki Ba – Rundunar Soji

A ci gaba da sauraren ainihin abinda ya auku a Lekki wanda ake zargin Sojoji sun kashe mutane, rundunar Sojin Najeriya ta ce gwamnatin Legas ta gayyace dakarunta su zo domin tabbatar da dokar ta baci da gwamnatin ta saka.

” Jami’an mu sun halarci wannan wuri domin amsa gayyatar gwamnatin Legas, amma kuma babu jami’in mu ko daya da ya harbi kowa a wurin. Dakarun mu na da kwarewar sanin abinda ya kamata, saboda haka babu wanda ya harbi wani a Lekki.

Sai dai kuma gwamnan jihar ya taba karyata cewa gwamnatin jihar ce ta gayyaci sojoji Lekki, sannan kuma ya shaida cewa an samu shaidar mutum biyu sun rasu a wannan wuri a ranar da aka yi harbin.

Mutane da dama zargi sojoji da bude wa masu zanga-zanga wuta a wannan wuri amma kuma babu wanda ya iya kawo gawar wanda aka kashe.

Har yanzu dai zargi ne ake ta yi ba a tabbatar da me ya auku ba a wannan rana.

Akwai wadanda ake cewa an kashe sai daga baya kuma su fito su ce suna nan da ran su.

Har yanzu dai kwamitin da jihar Legas ta kafa game da wannan harbi da kisa da ake zargin Sojoji da tafka na ci gaba da zama a legas.

Gwamman jiha Babajide Sanwo-Olu ya ce za a mika rikodin din da kamarorin da aka makala a wannan wuri ga kwamitin domin ya kalla.

Related posts

Leave a Comment